Ecowas ta umarci dakarunta su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar

Shugabannin ƙasashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar, su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar, bayan juyin mulkin sojoji na ranar 26 ga watan Yuli.

Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar ranar Alhamis, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin shirya dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta wa Nijar aiki da ƙudurorin ƙungiyar.

Sun cimma wannan matsaya ce yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a Abuja.

Cikin sauƙi, ba za a iya fayyacewa ƙarara ba, ko umarnin yana nufin dakarun sojin Ecowas za su auka wa Nijar ne da yaƙi, ko kuma za su ɗaura ɗamara su zauna cikin shiri kawai.

Tun da farko, Ecowas ta bai sojojin da suka yi juyin mulki wa'adin kwana bakwai, su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da suka hamɓarar kan karagar mulki, ko su fuskanci amfani da ƙarfin soja.

Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika, kuma sun yi muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron Ecowas suka bayar, da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.

Sun kuma nanata yin Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.

Ƙungiyar ta ce za ta tabbatar da ganin ana aiki da duk ƙudurorinta kuma har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke. Shugabannin sun kuma ɗora wa jagororin Ecowas alhakin ci gaba da bin diddigin takunkuman da aka ƙaƙaba wa shugabannin juyin mulki a Nijar.

Haka zalika, sun gargaɗi waɗanda suka ce suna kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Nijar, su guji yin haka.

Ƙudurorin taron Ecowas

Sanarwar ta nunar cewa duk ƙoƙarin diflomasiyya da Ecowas ta yi don warware rikicin, shugabannin soji na Jamhuriyar Nijar sun ƙeƙasa ƙasa, kuma sun sa ƙafa sun shure.

Ta ce bayan la'akari da ƙarewar wa'adin mako ɗaya da aka bayar don mayar da Nijar kan tsarin mulki, ƙungiyar ta yanke shawarwari kamar haka:

  • Jaddada Allah-wadai cikin kakkausar murya ga yunƙurin juyin mulki da kuma ci gaba da haramtacciyar tsarewar da ake yi wa Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa da kuma jami'an gwamnatinsa.
  • Ƙara yin Allah-wadai da yanayin da ake tsare da Shugaba Bazoum, kuma za su yi wa Majalisar Tabbatar da Tsaron Ƙasa (CNSP) cikakken kamu, sannan ita kaɗai suka sani da alhakin tsaron lafiya da tsaron rayuwa da tsare mutuncin Shugaba Bazoum da iyalinsa da kuma gwamnati.
  • Ƙara jaddada dukkan matakai da ƙa'idojin da taron gaggawa a kan Nijar na ranar 30 ga watan Yulin 2023 ya amince da su.
  • Jaddada muhimmancin ƙudurin ikon Ecowas na ci gaba da buɗe dukkan ƙofofi don cimma masalahar zaman lafiya a rikicin.
  • Tilasta dukkan matakan da aka ɗauka musamman na rufe iyakoki da tsaurara haramcin tafiye-tafiye da datse kadarorin illahirin mutane ko rukunin mutanen da ayyukansu ke kawo cikas ga duk wani ƙoƙarin zaman lafiya da nufin mayar da Nijar gaba ɗaya kan tsarin mulki ba tare da tangarɗa ba.
  • Gargaɗi ga ƙasashe mambobin (ƙungiyar) waɗanda ta hanyar matakinsu kai tsaye ko a kaikaice, ke kawo cikas ga ƙoƙarin cimma masalahar zaman lafiya a rikicin Nijar, game da sakamakon abin da suka aikata.
  • Kira ga Tarayyar Afirka ta amince da duk shawarwarin da Ecowas ta ɗauka a kan lamarin da ke faruwa a Nijar.
  • Ƙara kira ga dukkan ƙasashe abokan ƙawance da hukumomi ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya a kan su tallafa wa Ecowas, a ƙoƙarinta na tabbatar da aiki da tsarin mulki don bin ƙa'idar tanade-tanaden kafuwarta.
  • Umarni ga Shugaban Hukumar (Ecowas) ya bi diddigin aiwatar da takunkuman da aka sanya.
  • Umarni ga kwamitin manyan hafsoshin tsaro su shirya dakarun ko-ta-kwana na Ecowas cikin ɗamara da duk al'amuransu nan take.
  • An umarci tura dakarun ko-ta-kwana na Ecowas su dawo da aiki da tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.
  • Jaddada muhimmancin ci gaba da ƙudurin dawo da aiki da tsarin mulki ta hanyoyin zaman lafiya.

Su wane ne suka halarci taron?

Da safiyar Alhamis ne shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma suka buɗe taron gaggawa na Abuja a ƙoƙarinsu na yanke shawarar ko su yi amfani da ƙarfin soja ko kuma hanyar diflomasiyya da nufin mayar da Nijar kan tsarin dimokraɗiyya, bayan juyin mulkin watan Yuli.

Mako biyu kenan da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka hamɓarar da Bazoum Mohamed daga kan mulki tare da tsare shi - a wani al'amarin juyin mulkin soji na baya-bayan nan da ke naso a faɗin nahiyar Afirka.

Shugabannin da suka halarci Abuja don wannan taro sun haɗar da:

  • Shugaban Saliyo - Julius Maada Bio
  • Shugaban Guinea Bissau - Umaro Sissoco Embalo
  • Shugaban Burundi - Everiste Ndayishimiye
  • Shugaban Kwatdebuwa - Alassane Ouattara
  • Shugaban Ghana - Nana Akufo-Addo
  • Shugaban Senegal - Macky Sall
  • Shugaban Benin - Patrice Talon
  • Shugaban Togo - Faoure Gnassimbe
  • Shugaban Najeriya kuma shugaban Ecowas - Bola Tinubu
  • Mamadou Tangara - Ministan harkokin wajen Gambia
  • Ambasada Dee‑Maxwell Saah Kemayah - Ministan wajen Laberiya
  • Belarmino Silva - Ambasadan Cape Verde

Shugaban Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani da takwaransa na Burundi Everiste Ndayishimiye, su ma sun shaida taron.

Shi ne na biyu da Ecowas ta yi a kan juyin mulkin Nijar.

Haka zalika, taron na ranar Alhamis ya samu wakilcin ƙasar Aljeriya, yayin da ministan harkokin wajen hamɓararriyar gwamnatin Bazoum, Hassoumi Massaoudou ya wakilci Nijar.

Sai kuma Mista Bankole Adeyoye daga Tarayyar Afirka da Mohammed Ibn Chambers, babban jami'in shirin Tarayyar Afirka mai taken "Kawo Ƙarshen Tashe-tashen Hankula". Da kuma Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas.

Haka ma, akwai wakili na musamman daga Majalisar Ɗinkin Duniya a kan Yankin Afirka ta Yamma da Sahel, Mista Leornado Santos Simao.

Babu dai wani zaɓi mai sauƙi ga shugabannin na Ecowas, wadda Tinubu ke jagoranta.

Akwai matsin lamba a kansu na ganin sun mayar da tsarin dimokraɗiyya a Nijar - wata makekiyar ƙasa da ke fama da ɗumbin matsaloli kamar rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi da kuma talauci.

Sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar ya zuwa yanzu sun ƙesasa ƙasa kan duk wani matsin lambar tattalin arziƙi da na diflomasiyya.

A shekarun baya, barazanar amfani da ƙarfin soja ga ƙungiyar Ecowas, na iya zama wani zaɓi da babu wata taƙaddama kansa.

Amma yanzu sauran ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijar musamman Mali, da a baya-bayan nan suka faɗa ƙarƙashin mulkin sojoji kuma suke samun tallafi daga sojojin hayar Rasha, suna goyon bayan janar-janar ɗin da suka yi juyin mulki a Nijar.

A jawabin buɗe taro da ya gabatar, shugaban ƙungiyar Ecowas, ya faɗa wa shugabannin da ke halarta cewa kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba ga wa'adin kwana bakwai da suka bai wa shugabannin juyin mulkin Nijar.

Ya kuma shaida musu cewa ƙungiyar Ecowas ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya don cimma masalaha.

Ya ce ya yi farin cikin cewa ƙwararren jami'in diflomasiyyar Najeriya, Babagana Kingibe da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III da Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), tsohon shugaban Najeriya sun halarci taron don bai wa shugabannin ƙasashen ƙungiyar ƙarin haske a kan ƙoƙarin shiga tsakani.

A cewarsa, jami'an sun halarci Libya da Aljeriya, inda suka samu tarba daga shugabannin ƙasashen masu maƙwabtaka da Nijar.

Tinubu ya kuma bayyana cewa bisa matsayar da suka cimma a taronsu na farko, manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas sun yi taro daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Agusta, kuma za a gabatar musu da shawarwarin da suka bayar da ma wata muƙala da shugaban Hukumar Ecowas ya gabatar kan halin da ake ciki a Nijar.

Bayan jawabin ne kuma sai taron ya shiga zaman sirri.