Inter Milan na shirin ɗaukar Lookman, Real Madrid ta yi barazanar sayar da Vinicius

Lokacin karatu: Minti 1

Inter Milan na shirin miƙa tayi kan ɗan wasan Atalanta da Najeriya Ademola Lookman mai shekara 27. (Gazzetta dello Sport)

Real Madrid ta yi barazanar sayar da ɗan wasan gaban Brazil Vinicius Jr idan har ɗan wasan mai shekara 25 bai rage yawan albashin da ya ke buƙata ba. (Sport)

Manchester United ta samu cikas a yanƙurinta na sayen ɗan wasan gaban Brentford Bryan Mbeumo, mai shekara 25, yayin da kulob ɗin na birnin Landan ya ƙara farashin ɗan wasan zuwa kusan fam miliyan 70, yayin da United ba ta son biyan sama da fam miliya 65. (Guardian)

Liverpool ta fara tattaunawa da Eintracht Frankfurt kan cinikin ɗan wasan gaban Faransa Hugo Ekitike mai shekara 23. (Sky Sports)

Sai dai Newcastle United na ci gaba da nata yunƙurin na ɗaukar Ekitike inda ta ke fatan hada shi da ɗan wasan Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, a kakar wasa mai zuwa. (Telegraph)

Aston Villa na daga cikin ƙungiyoyin Premier da ke zawarcin ɗan wasan gaban Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 21. (Mail)

Manchester United na zawarcin ɗan wasan Chelsea Nicolas Jackson, mai shekara 24, yayin da Aston Villa da AC Milan suma suka sanya ido kan lamarin ɗan wasan na Senegal. (Times)

Manchester United na duba yiwuwar ƙulla yarjejeniyar musayar ƴan wasa a batun Jackson inda za ta iya miƙawa Chelsea Garnacho. (i paper)

Sunderland na zawarcin ɗan wasan Bayer Leverkusen ɗan ƙasar Switzerland Granit Xhaka mai shekara 32 . (Sky Sports)

West Ham na bibiyar ɗan wasan tsakiya na Bournemouth Marcus Tavernier, mai shekara 26. (Insider Football)

Manchester United ta tattauna da Brighton kan yiwuwar cinikin ɗan wasan bayan Ecuador Pervis Estupinan mai shekara 27. (Mirror)

Leeds United ta cimma yarjejeniyar fatar baki da ɗan wasan Hoffenheim da Jamus Anton Stach, mai shekara 26. (Sky Sports Germany)

Stuttgart ta yi watsi da tayin fam miliyan 43 daga Bayern Munich kan ɗan wasan Jamus Nick Woltemade, mai shekara 23. (Sky Sports Germany)