Wasu daga cikin ƙayatattun hotunan 2024

Lokacin karatu: Minti 7

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna mafi ƙayatarwa da masu ɗaukan hoto a faɗin duniya suka ɗauka a shekarar 2024.

Ruwan narkakken dutse na kwarara kan titi a yankin Reykjanes na ƙasar Iceland, ranar 21 ga watan Nuwamba, 2024.

Asalin hoton, ANTON BRINK/EPA

Bayanan hoto, Ruwan narkakken dutse na kwarara kan titi a yankin Reykjanes na ƙasar Iceland sa'ilin da dutsen ya yi amon wuta.
Ƴan gudun hijira da ke kutsawa cikin Amurka ta wata kafa a katangar da ta raba ƙasar da Mexico, a ranar uku ga watan Janairun, 2024, a yankin Jacumba Hot Spring na San Diego a jihar California

Asalin hoton, Qian Weizhong/VCG via Getty Images

Bayanan hoto, Ƴan gudun hijira da ke kutsawa cikin Amurka ta wata kafa a katangar da ta raba ƙasar da Mexico, a ranar uku ga watan Janairun, 2024, a yankin Jacumba Hot Spring na San Diego a jihar California

Yawan ƴan ci-ranin da ke isa kan iyakar Amurka da Mexico ya kai yawan da ba a taɓa gani ba a lokacin mulkin shugaban Amurka Joe Biden, lamarin da ya zame masa babban ƙalubale gabanin zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a watan Nuwamba.

Yawan ƴan ci-ranin da ke kwarar zuwa Amurka ya fara tashi ne a 2018, waɗanda ke fitowa daga ƙasashen da ke tsakankanin nahiyoyin Amurka biyu, sanadiyyar faɗace-faɗacen ƴan daba, da zaluncin shugabanni da kuma bala'i'o.

Alicia Keys lokacin da ta yi waƙa a gagarumin bikin wasanni na Super Bowl a birnin Las Vegas ranar 11 ga watan Fabarairun 2024.

Asalin hoton, AP Photo/David J. Phillip

Mawaƙiyar Amurka, Alicia Keys ta nuna basirarta a gagarumin bikin wasa na Super Bowl na shekarar 2024.

Alicia Keys ta zauna a kusa da kayan kiɗan piano mai launin ja, inda ta sanya kaya mai launin ja, sannan ta rera waƙarta mai taken "If I Ain't Got You".

Daga nan sai ita da mawaƙi Usher suka yi waƙar "My Boo".

Ƴan gudun hijiran Rohingya maƙale a kwale-kwalensu da ya yi hatsari a ranar 21 ga watan Maris, 2024.

Asalin hoton, Reza Saifullah/AP

Bayanan hoto, Ƴan gudun hijiran Rohingya maƙale a kwale-kwalensu da ya yi hatsari a ranar 21 ga watan Maris, 2024.

Masu aikin ceto na ƙasar Indonesia sun gano wasu ƴan gudun hijira na ƙabilar Rohingya waɗanda rana da rashin abinci ta galabaitar a kan kwale-kwalen da ya yi hatsari a gaɓar Aceh.

Hukumar aikin ceto ta ƙasar ta ce an ceto yara 9 da mata 18 da kuma maza 42 ne aka ceto.

An yi amannar cewa kimanin ƴan gudun hijira 80 ne ruwa ya yi awon-gaba da su - wadanda ake kyautata zaton sun mutu.

Hasken da ake kira 'Aurora Borealis', wanda ake kira 'Northern Lights', lokacin da suke haskawa a samaniyar birnin Kiruna da ke ƙasar Sweden a daren ranar 7 ga watan Maris, 2024.

Asalin hoton, Leon Neal/Getty Images

Bayanan hoto, Hasken da ake kira 'Aurora Borealis', wanda ake kira 'Northern Lights', lokacin da suke haskawa a samaniyar birnin Kiruna da ke ƙasar Sweden a daren ranar 7 ga watan Maris, 2024.

Hasken 'northern lights', mai ban sha'awa - wanda ke fitowa da daddare a yankunan maƙurar arewacin duniya - ya bayyana sosai a arewacin nahiyar Turai a watan Maris.

Akwai sa ran za a ci gaba da tsinkayar irin wannan haske a shekaru masu zuwa.

Mutane a Gaza na gudu zuwa wurin da kayan agaji ke sauka a Zirin Gaza ranar 23 ga watan Afrilun 2024.

Asalin hoton, AFP

Yadda mutane suka riƙa garzayawa domin tsintar kayan agaji da ake jefowa ta jiragen sama a Zirin Gaza.

Tsarin da aka fara amfani da shi a lokacin yaƙin duniya na biyu domin isar da kayan buƙata ga sojojin da ke a yankin ba a iya zuwa wajensu ta ƙasa, yanzu ana amfani da tsarin wajen isar da kayan agaji, wanda ake amfani da shi a duk lokacin da babu wata hanya da za a iya taimakawa.

Wani gini da girgizar ƙasa ta lalata a birnin Hualien, a ranar 4 ga watan Afrilun 2024.

Asalin hoton, Carlos Garcia Rawlins/Reuters

Taiwan ta yi fama girgizar ƙasa mafi muni a cikin shekara 25, wadda ta kai ƙarfin maki 7.4 a ma'aunin girgizar ƙasa, lamarin da ya lalata gine-gine, musamman a gaɓar tsibirin ta gabas.

Kisfewar rana a Washington, 8 April 2024

Asalin hoton, Chip Somodevilla/Getty Images

Wannan hoto ne na kisfewar rana a kusa da ginin Washington Monument da ke birnin Washington DC, kamar yadda miliyoyin al'umma suka kalli kalli abin al'ajabin wanda ya bayyana a ƙasashen nahiyar Amurka ta Arewa a watan Afrilun.

Sabbin ƴan gudun hijirar Sudan da suka isa sansanin da aka samar a kusa da Adre na ƙasar Chadi, inda suke dafa abinci a yammacin ranar 24 ga watan Afrilun 2024.

Asalin hoton, Dan Kitwood/Getty Images

Sama da mutum miliyan 10 ne yaƙi ya tursasa wa tserewa daga gidajensu a Sudan, inda mata da yara suka zamo cikin mafiya yawa a cikin waɗanda ke tuɗaɗa zuwa sansanonin ƴan gudun hijira a ƙasar Chadi.

Sudan ta faɗa cikin mummunan yanayi ne tun bayan da dakarun ƙasar da kuma wani ɓangare na sojojin ƙasar suka fara yaƙar juna a cikin watan Afrilun 2023.

An gaggauta fitar da Donald Trump daga wurin da yake yaƙin neman zaɓe a garin Buttler na jihar Pennsylvania, bayan wani ɗan bindiga ya buɗe masa wuta daga kan rufin gini.

Asalin hoton, AP/Evan Vucci

An gaggauta fitar da Donald Trump daga wurin da yake yaƙin neman zaɓe a garin Buttler na jihar Pennsylvania, bayan wani ɗan bindiga ya buɗe masa wuta daga kan rufin gini.

Ɗan takarar shugaban ƙasar ta Amurka a jam'iyyar Republican ya duƙa ƙasa, inda jini ya riƙa zuba a gefen fuskarsa.

A lokacin da jami'an tsaro suke ƙoƙarin saukar da shi daga kan dandamali, Trump ya ɗaga hannunsa sama.

Buɗe gasar Olympics ta 2024 a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Asalin hoton, FRANCOIS-XAVIER MARIT/REUTERS

An yi ƙasaitaccen biki wajen buɗe gasar wasanni ta Olypics 2024 a birnin Paris na ƙasar Fransa, lokacin da dubban ƴan wasa suka wuce a kwale-kwale ta kogin Seine, yayin da mutane ke kallo.

Masu zanga-zangar kisan jagoran Hamas, Ismail Haniyeh a Sidon da ke Lebanon, ranar 11 ga watan Yuli 2024.

Asalin hoton, REUTERS/Alkis Konstantinidis

Masu zanga-zanga a Sidon, da ke Lebanon lokacin da suke zanga-zangar adawa da kisan jagoran Hamas, Ismail Haniyeh.

Hamas ta ce an kashe Haniyeh ne lokacin wani samame da Isra'ila ta kai a gidansa a Tehran, na Iran, lokacin da Haniyeh ya je Iran din domin bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian.

Masu aikin ceto a sibitin yara na Okhmatdyt da ke birnin Kyiv na Ukraine lokacin da makamin Rasha ya faɗa kansa a ranar Litinin, 8 ga watan Yulin 2024.

Asalin hoton, Evgeniy Maloletka/AP

A watan Yuli, wasu hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai a birnin Kyiv na ƙasar Ukraine ya faɗa a kan wani asibitin yara.

Mutum biyu ne suka mutu a lokacin da makaman suka faɗa kan asibitin yaran na Ohmatdyt.

Gisele Pelicot tare da lauyanta Stephane Babonneau lokacin da suke barin kotu a shari'ar maza 50 da ake zargi da yi mata fyaɗe, ciki har da mijinta.

Asalin hoton, GUILLAUME HORCAJUELO/EPA

Gisèle Pelicot ta shafe watanni a wata cibiya yayin da ake shari'ar mutane 51 da ake zargin sun kwashe shekaru suna yi mata fyaɗe - cikin su har da mutumin da ta aura tsawon shekara 50.

Ta buƙaci a bayyana fuskarta, inda ta zamo wata alama ta juriya da ƙwarin gwiwa yayin da labarin batun ke ƙara yaɗuwa.

Falasɗinawan da ke ƙoƙarin tserewa daga gabashin Khan Younis a Gaza, ranar 7 ga watan Oktoban 2024.

Asalin hoton, REUTERS/Hatem Khaled

Yayin da ake gumurzu tsakanin Isra'ila da Hamas a yankin Gaza, Falsɗinawa waɗanda yaƙin ya tarwatsa sun cunkusu a cikin wata ƙaramar mota yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga birnin Khan Younis bayan umarnin da Isra'ila ta ba su.

Shekara ɗaya bayan ɓarkewar yaƙin ne Isra'ila ta bai wa mutane umarnin su fice daga arewacin Gaza a watan Oktoba, abin da ya tursasa wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa zuwa kudancin yankin.

To amma kudancin Gaza ya ci gaba da fuskantar ruwan bama-bamai, abin da ya sanya Majalisar ɗinkin duniya ta yi garghaɗin cewa babu wata mafaka a faɗin Gaza.

Ƴar takarar shugaban ƙasa ta jam'iyyar Democrat a zaɓen shugaban Amurka, lokacin da take ƙaratowa kusa da ƴan jarida gabanin shiga jirgi a tashar jirgi ta Harry Reid da ke Las Vegas a jihar Nevada, ranar 10 ga watan Oktoban 2024, a kan hanyarta ta zuwa jihar Arizona.

Asalin hoton, Jacquelyn Martin/AP

Ƴar takarar shugaban ƙasa ta jam'iyyar Democrat a zaɓen shugaban Amurka, Kamala Harris lokacin da ta tsaya domin ganawa da manema labaru gabanin shiga jirgi a filin jirgin sama na Harry Reid International Airport da ke birnin Las Vegas.

Ta ziyarci jihar Nevada, kasancewar jihar na da matuƙar muhimmanci a zaɓen.

Jihar ta taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a cikin watan Nuwamban 2024.

Wata mata na kallon yadda ambaliyar ruwa ta jibge motoci a kan hanya a birnin Valencia, ranar 30 ga watan Okotoban 2024.

Asalin hoton, Alberto Saiz/AP

Fiye da mutum 200 ne suka mutu sanadiyyar mamakon ruwan sama wanda ya haifar da mummunar ambaliyar da ta tagayyara al'umma a gabashin Sifaniya.

Ambaliyar ta lalata gine-gine da fasa gadoji da kuma jibge tarin bola a kan tituna, a lokacin da aka yi ruwan wanda ya kai adadin na shekara ɗaya a cikin ƴan sa'o'i.

Dalibai sun tuntsurar da butum-butumin tsohon shugaban Syria, Hafeez al-Assad a kusa da Jami'ar Damascus da ke babban birnin Syria a ranar 15 ga watan Disamba.

Asalin hoton, Omar HAJ KADOUR / AFP

Mulkin iyalin gidan Assad ya zo ƙarshe a Syria bayan kwashe shekara 50, inda ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) da wasu ƙungiyoyi suka yi haɗaka suka ƙaddamar da farmaki daga yankin arewa maso yammaci.

Ba da daɗewa ba ƴan tawayen suka kame gari na biyu mafi girma a ƙasar, Aleppo, sannan suka dumfari Damascus, inda Bashar al-Assad ya tsere daga ƙasar a lokacin da ya ga an ci galabar sojin ƙasar.