Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Masana'antar mutuwa' a Indiya
"Wannan masana’antar mutuwa ce."
Hannun Isma’il Khan na karkarwa lokacin da ya fadi hakan yana nuni da hawa na biyu na ginin da ke birnin Delhi a Indiya.
A wannan ginin ne ya yi wa kanwarsa kallon karshe, inda ta makale, ga rashin iska, ta rasa inda za ta samu hanyar fitowa saboda hayakin da ya turnuke lokacin da gobara ta tashi.
Muskan, mai shekara 21, na daga cikin mutane 27 da gobara ta hallaka a watan Mayu, a sashen lantarkin masana’antar mai hawa hudu.
Kwanaki kadan da tashin gobarar, wani babban jami’in ‘yan sanda ya shaida wa manema labarai ma su masana’antar da suke ‘yan uwan juna, ba su nemi cikakken izinin daga ma’aikatar lantarkin Indiya, kafin kara bene hawa uku a ginin ba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin Delhi, ya shaida wa BBC cewa ba su da lasisin aiki.
BBC ta kira lambar tarhon masu masana’antar domin jin ta bakinsu, amma ba su amsa kiran ba. Har wayau, BBC ta tuntubi lauyansu, shi ma ya ki cewa uffan ko karin bayani a kai.
Indiya na da kudurin zama kasar da ta fi kowacce karfin masana’antu, yayin da gwamnati ke gabatar da shirin bunkasa dinki domin karfafa wa masu zuba jari da masu kirkira.
Sai dai bala’o’i kamar na gobarar Delhi ba bakin abu ba ne a Indiya, inda ma’aikatan da ke cikin tsaka-mai-wuya ke fadawa cikin wahala.
Hatsarin da ake fama da su a masana’antu a kowacce shekara, yana sanadin kashe daruruwan mutane, da mayar da wasu musakai har abada.
Ma’aikatar gwamnati ta shaida wa majalisar a shekarar 2021, akalla ma’aikata 6,500 ne suka mutu lokacin su na aiki a masana’antu, da wurin hakar ma’adinai, da aikin gona, da tashoshin ruwa, har da kamfamnonin gine-gine cikin shekaru biyar.
Masu rajin kare hakkin ma’aikatan da suka shafe kwanaki su na aiki, sun shaidawa BBC cewa adadin wadanda suka mutu ya zarta na hukumomin, saboda wasu ba a kai rahoto.
Kamar yadda kididdigar da kungiyar ma’aikatan duniya ta fitar, ta ce fannonin da aka fi samun mutuwar ma’aikata ta ce yawanci an fi samun haka a masana’antun sinadarai da na gine-gine,
Sun ce a shekarar 2021, a kalla ma’aikata bakwai ke mutuwa a kowanne a masana’antun kasar ta Indiya, idan akai kiyasi kusan muatne 162 ne suka mutu.
Cikin shekarun da suka gabata, ana yawan samun rahotannin ma’aikatan masana’antun da gwamnati ba ta san da zaman su a hukumance ba sun shiga wata matsala.
Yawancin wadanda lamarin ke rutsawa da su matalauta ne, ko ‘yan ci-rani da iyalansu suka tserewa yake-yaken da ake yi a kasashe ko garuruwansu.
BBC ta aikawa hukumar kwadagon birnin Delhi da ma’aikatar kwadago sakon imel kan wannan batu amma babu wanda ya aiko da amsar sakon.
'A bi min hakkina'
A kowacce Safiya, Rakesh Kumar na farkawa tsakar dare, cikin kururuwa wani lokacin har da safe. ‘Ya’yansa uku mata ne suka mutu a gobarar da ta tashi a masana’anta, inda ake ba su albashin dala 100, wato 8,000 a kowanne wata, aikinsu shi ne sanya wa wayoyin salula intanet na Wi-Fi .
"’Ya’yana sun sha bakar wuya," in ji shi.
Iyaye da ‘yan uwan matan sun jira tsahon kwanaki bayan ibtila’in gobarar, daga bisani ‘yan sanda suka kirasu domin daukar samfurinsu domin gudanar da gwajin kwayoyin halitta, ta yadda za a gane gawar ‘ya’yansu da suka kone.
Bayan wata guda da faruwar lamarin, aka ba su gawar inda suka konesu kamar yadda yawancin Indiyawa ke yi.
"ina son ayi musu adalci," in ji Mr Kumar.
A watan Agusta, ‘yan sandan Delhi sun gurfanar da mutane biyar gaban kotu da ake zargi da tashin gobarar.
Ciki har da zargin aikata kisa ba da gangan ba, da sakacin mutuwar ma’aikata.
Rajesh Kashyap, dan fafutuka ne, ya zargi yawancin masu masana’antu da ke birnin Delhi da garuruwa ba sa bin dokokin da suka shafa kafa masana’antu, sannan idan bala’i ya faru ba a cika maida hankalin daukar mataki.
Shi da sauran masu fafutukar kare hakkin ma’aikata, sun jima suna fafutukar ganin an gurfanar da irin wadannan mutanen gaban shari’a amma ba a daukar lokaci sai a ba da belinsu.
‘Yan sandan Delhi, sun ce an yi rijistar hatsarin da ya faru a masana’antu sau 663 a birnin cikin shekaru biyar, inda mutane 245 suka mutu.
An kuma cafke mutum 84, da ake zargi da hannu a hatsarin.
A wani martani kan zargin da kungiyar kwadago ta yi, ta ce ainihin binciken da ake yi a lamura irin wannan ba a daukar matakin gaggawa kan wadanda aka samu da laifi.
Sai dai sun kara da cewa ana daukar lokaci wajen binciken kwayoyin halitta da sauransu, wanda kwararru a fannin ne suke tafiyar hawainiya wajen tabbatar da an yi komai cikin lokaci.
Fadi tashin karbar diyya
BBC ta gana da iyalai da dama, da har yanzu ke cikin bakin ciki da jimamin mutuwar masoyansu, yawanci s uke kula da iyalan baki daya.
Sai dai har yanzu ba a bai wa iyalan diyyar ‘yan uwansu da suka mutu ba.
Wani babban lauya, da ya dade ya na aiki ya na neman karbawa iyalan mamatan diyya, ya shaidawa BBC cewa yawanci ana daukar shekaru kafin a biya su diyya.
Lokaci zuwa lokaci, gwamnbati na sanar da biyan makudan kudadeen diyya ga iyalai , tare da kauce biyan kamfanoni.
Da zarar an fara shari’a, iyalan mamatan saboda bacin rai da alhini, wanda daman ‘yan cirani neb a sa iya zama a birnin tun da mai daukar hidimarsu ya mutu, sai su tattara su komawa kauye ko wani birnin domin neman aiki.
Batun diyya ya bi shanun sarki.
"Ma’ikata ba su da kwarin gwiwa kan fannin shari’a, da yadda ake daukar lokaci ana yi.
Don haka suna karbar komai kankantar kudin da aka ba su a matsayin diyya daga gwamnati ko masu masana’antun, shi ke nan an gama shari’a," in ji Chandan Kumar, na kungiyar farar hula da ke taimakon ma’aikata.
BBC ta yi kokarin tuntubar iyalan ma’aikatan masana’antar Delhi su 17, da suka mutu sanadin gobara a shekarar 2018, amma yawanci sun yi kaura daga birnin.
Sangeeta Roy, mai shekara 50, wani inji ne ya datse mata kafa a wurin aiki shekaru 3 da suka gabata. Ta ce har yanzu ko rufi daya masana’antar ba ta biya diyya ba, haka ma gwamnati.
Babu wata kidaddigar gwamnati da ta tabbatar da yawan wadanda injina suka mai da musakai a masana’antun da suke aiki.
Binciken baya-bayan nan da hukumar hididdigar da tsaron ma’aikatan kamfanonin kera mota a Indiya ta fitar, sun ce a arewacin kasar kadai, an samu afkuwar munanan hatsari daban-daban har sau 3,955 tsakanin shekarar 2016 zuwa 2022.
Kashi 70 cikin 100 na mutanen da suka ji rauni, injina ne suka yanke musu ‘yan yatsu, wasu kuma injin ya markade hannayensu, wasu kafada lokacin da suke amfani da injin yanka wani abu.
A kudancin yankin Asiya, Indiya ce sahun gaba a karfin masana’antu, an yi kiyasin akwai ma’aikata sama da miliyan 10 da ke aikin a wadannan wurare.
Yawancin masana’antun na aiki a fannin samar da kayayyakin da ake yawan amfani da su a kasar.
Sandeep Sachdeva, yana da masana’anta, ya shaida wa BBC cewa yawancin jihohin Indiya ba sa kai rahoto ko shigar da kara idan an samu lamari irin wannan.
Damuwa kan abin da zai faru nan gaba
Indiya ta fara sauye-sauye a fannin kwadago da walwalar ma’aikata da dokoki hadi da tsaronsu a wuraren aiki har da fannin lafiyar ma’aikata.
Sai dai masu fafutuka sun damu matuka kan sabbin dokokin da aka sanya, ka iya aiki ko akasin hakan, ko ci da gumin wasu.
Yayin da dokar farko ke cewa, duk kamfanin da yake da ma’aikata sama da 10, ya kafa kwamitin tsaro, sabuwar dokar ta kara yawan ma’aikatan daga 190 zuwa 250.
Sai dai kidayar tattalin arziki da aka yi ta shekarar 2016, ta nuna kashi 1.66 na yawan masana’antun da ba na aikin gona ba, na amfani da tsohon tsari, yayin da masana’antun tufafi ke amfani da kashi 2, sai kuma sauran da ke amfani da kashi 1.25 kan ma’aikata 10.
Babu cikakkiyar kididdigar yawan ma’aikatan Indiya na masana’antu da kamfanoni, wadanda kashi 90 cikin 100 na kananan ma’aikata ke aiki a irin wuraren.