Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
A ba mu makamai don kare kanmu - Jama'ar Sokoto
Al'ummar ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto a Arewa maso yammacin Najeriya ta buƙaci gwamanti ta basu ikon mallakar makamai domin kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga da suka addabe su.
Jama'ar yankin sun ce sun gaji da yadda ƴan bindigar ke ci gaba da kai masu hari, da kashe masu mutane da kuma garkuwa da wasu, lamarin da ya janyo masu mummunar asara.
Sun ce daga cikin garuruwa 17 da ƙaramar hukumar Kebbe ke da su, a yanzu ƴan bindiga sun kori mutane daga garuruwa aƙalla 11, saboda yawaitar hare-hare.
Tukur Muhammad Fakum, daya daga cikin jagororin al'ummar ya shaida wa BBC cewa an riga an kai maƙura, don haka a yanzu fatan su kawai bai wuce neman wa kai mafita ba.
Ya ce ''Mu yanzu muna nan muna gangami, mai ƴar ƙaramar gona ya sayar, mai ɗan ƙaramin gida ya sayar, in muka sayi bindigogi a ba matasa su ma su yi ƙoƙari su kare mu.
''Gwamnati ta ba mu kariya, idan kuma ba ta iyawa to ta bamu makamai a ba matasa, su matasa na iya kare rayukansu da garuruwan su,'' in ji Tukur Muhammad Fakum.
Dangane da halin da irin ɓarnar da ƴan bindigar suka yi masu kuwa, Tukur Muhammad Fakum ya ce ''Babu dai abinci, wanda bai taɓa kwana masallaci ba ya yi, ka tashi ka tafi garin da ba ka taɓa kwana ba, ka kwana dole. Bala'in ya ɓaci.''
Ya kuma ce lamarin rusa kusa duk wata harkar tattalin arziki a yankin.
BBC dai ta yi ƙoƙari jin halin da ake ciki daga ɓangaren gwamnati da jami'an tsaro, amma hakan ba ta samu ba.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da matsalar ƴan bindiga ta addaba sosai a shekarun nan, inda suke aikata ɓarna, musamman a ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni da kuma Kebbe.
Bayan ƴan bindiga masu biyayya ga Bello Turji da suke ayyukan su a jihar, an kuma samu ɓulluwar mayaƙan Lakurawa, wata sabuwar ƙungiyar da masu sharhi a kan harkokin tsaro ke gargaɗin cewa za ta iya zama sabuwar annoba ga jihar da ma yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.
A jihar Kebbi da ke maƙwabtaka da Sokoto ma wasu ƴan bindigar sun kai hari a kan jami'an tsaro, a garin Dirin Daji da ke ƙaramar hukumar Sakaba ta jihar.
Wata mazauniyar garin ta ce ''Sun kai hari a kan sansanin sojoji da na ƴan sanda, wanda ke gadi a sansanin sojojin sun harbe shi, kuma nan take Allah ya mashi cikawa.''
Ta ƙara da cewa ''Daga baya an turo jami'an tsaro, waɗanda suka kawo ɗauki cikin gaggawa, kuma da alama ƙura ta lafa.''