Halal ko Haram: An jingine shirin tara nonon uwa na sadaka saboda sukar malaman Musulunci

Asalin hoton, Rahim Shah
- Marubuci, Riaz Sohail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Urdu
- Aiko rahoto daga, Karachi
Wani shiri irinsa na farko don tara nonon uwa a rumbu ya fuskanci matsala a Pakistan bayan masu kishin addinin Musulunci sun nuna adawa a birnin Karachi.
Tun da farko malamai sun amince da shirin amma bisa sharaɗi, sai kuma suka janye goyon bayansu 'yan kwanaki kafin ƙaddamar da shi.
Pakistan ce ƙasa ta biyar mafiya yawan al'ummar Musulmi a duniya. Kuma ita ce ke da mafi yawan jariran da ke mutuwa a Kudancin Asiya, a cewar asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef.
Shirin tara nonon uwa kamar wannan zai iya taimakawa sosai wajen kare mutuwar yara, saboda ana kallonsu a matsayin zaɓi mafi kyawu ga yara bakwaini waɗanda uwayensu ba su da ruwan nono.
Yaƙin tsira da rayuwa
Bashira ta rasa ɗanta na farko a lokacin haihuwa a ƙauyensu kafin su koma Karachi.
Lokacin da ita da mijinta Rahim suka samu ɗa 'yarsu ta biyu a shekarar da ta gabata a Karachi, sun shiga fargabar rasa ta ita ma.

Asalin hoton, Getty Images
"Mun haifi 'yarmu a matsayin bakwaini, sai likitoci suka ba mu shawarar mu shayar da ita nono," kamar yadda ta faɗa wa BBC.
"Sai dai kuma ba ni da isassehn ruwan nono."
Saboda haka babu yadda suka iya yi.
"'Yata na cikin kwalabar rainon jarirai a sashen kulawa akai-akai. Wata bakwai aka haife ta. Ga shi babu ruwan nono. Ba mu iya ba ta madara. Na yi bakin ƙoƙarina wajen tseratar da rayuwar 'yata," in ji mijin Bashira Rahim Shah.
Wata uwa da ke cikin makoki ce ta taimaka musu.
"Mun yi ta yawon asibiti, sai daga ƙrshe muka haɗu da wata mata da ɗanta ya rasu bayan naƙuda. Mun nemi ta shayar da jaririyarmu kuma cikin sa'a ta amince," a cewar Bashira.
Rumbun ajiyar nono

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matar dai ta shayar da 'yar Bashira da hannunta. Amma a rumbun ajiye nono, nonon sadakar da aka samu daga uwaye akan sarrafa shi don bai wa yara, sai a gwada shi sannan a adana shi firji. Daga baya kuma sai a bai wa jariran da suke buƙata.
Wasu ƙasashen Musulmi kamar Malaysia, da Iran na da irin wannan shiri.
Sai dai wasu malaman Musulunci na cewa hakan ya saɓa wa dokokin shayarwa na Musulunci.
A Musulunci, duk matar da ta shayar da ɗan da ba nata ba to samu wata alaƙa da shi ta kusa, kuma hakan na nufin 'ya'yanta ko kuma sauran yaran da ta shayar sun zama 'yan'uwa.
Duk abin da Musulunci ya amince da shi shi ake kira "Halal", akasin haka kuma "Haram".
Wasu malaman Pakistan na ganin wannan a matsayin haram.
Sai dai kuma hukumomi sun yi yunƙurin saita shirin ya dace da shari'ar Musulunci.
Ministar Lafiya ta Lardi Dr Azra Pechuho ta faɗa wa BBC cewa ta aika wa Majalisar Malaman Musulunci wasiƙa don faɗa musu cewa tabbas mata kan iya shayar da yaran da ba nasu ba a Musulunci.
"Duk wadda ta ba da sadakar nono ana rubutawa, kuma a bai wa iyayen yaron da aka shayar sannan kuma a bi diddigi," kamar yadda ta tabbatar game da fargabar haɗa aure ba tare da masaniya ba tsakanin yaran da suka sha nono ɗaya - wanda haramun ne a Musulunci.
Tana fatan saita lamarin ta hanyar tabbatar da cewa uwayen maza sun shayar da jarirai maza kawai, uwayen mata kuma su shayar da mata kawai.
Irin wannan tsarin malamai a Turkiyya suka ɗauka a shekarar 2012.

Asalin hoton, Sindh Institute Of Child Health and Neonatology
Fatawoyi
An fara amincewa da kafa rumubun ajiyar nono a Karachi ranar 25 ga watan Disamban 2023.
Daga cikin sharuɗɗan akwai cewa dole ne masu gudanar da shi su faɗa mutane sunayen matan da ke ba da sadakar nonon.
Haka nan, nonon mata Musulmai kaɗai za a karɓa. Ba za a karɓi kuɗi ba. Za a bai wa jariran da aka haifa ƙasa da mako 34 nono kawai idan mahaifiyarsu sun kasa samar da ruwan nono.
Tsarin mulkin Pakistan ya sharɗanta cewa dole ne kowace dokar gwamnati ta dace da Shari'ar Musulunci.
Fatawar da aka sauya ranar 16 ga watan Yunin 2024 ta ce abu ne mawuyaci shirin ya iya kiyaye duka sharuɗɗan da aka saka masa da za su dace da Shari'ar Musulunci.
Asibitin Sindh Institute of Child Health and Neonatology (SICHN) ta ce yanzu ba ta da wani zaɓi illa jingine batun shirin bayan wata majalisar malamai mai suna Darul Uloom ta ba ta fatawa.
"Nan gaba za mu nemi wata fatawar game da wannan lamari daga Darul Uloom Karachi da kuma Majalisar Musulunci," a cewar asibitin.

Asalin hoton, Unicef
Rumbun ajiyar nonon uwa a duniya
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce rumbun ajiyar nonon uwa na aiki a ƙasashe sama da 60. Amma har yanzu malamai na nuna adawa da shi.
Wani shirin ajiyar nono da aka ƙaddamar a Bangladesh a 2019 bai kai labari ba cikin wata ɗaya bayan zanga-zangar da masu kishin addini suka yi.
A cewar wata maƙalar bincike da cibiyar American Academy of Paediatrics ta fitar, "Musulmai mazauna ƙasashen Yamma na fargabar amfani da nonon sadaka saboda ba su san masu bayar da sadakar ba".
Zuwa yanzu babu wani tsari da aka fitar na kafawa da kuma gudanar da rumbun ajiyar nonon uwa. Babu daɗewa WHO ta fara aiki a kan hakan.
Idan muka koma Karachi, 'yar Bashira na cike da ƙoshin lafiya yanzu saboda wannan matar da ta taimaka musu.
Ita ma Bashira na jiran lokacin da za ta taimaka wa wata uwar game da 'ya ko ɗanta.
"Ba zan taɓa mantawa da ita ba [matar da ta shayar da 'yarta] kuma nan gaba idan na samu dama zan taimaka wajen tseratar da rayuwar wani yaron," in ji ta.











