Me ya kai Abubakar Malami komar EFCC?

Asalin hoton, Malami/EFCC/BBC COLLAGE
A ranar Laraba ne tsohon ministan shari'ar Najeriya a zamani marigayi Muhammadu Buhari, Abubakar Malami ya ɓara cewa jami'an hukuma da ke yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa, EFCC sun kai wani samame ofishinsa da gidajensa a Abuja da Kebbi.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mohammed Bello ya fitar, Malami ya ce samamen na EFCC sun faru ne jim kaɗan bayan da ofishin nasa ya saki wata sanarwa da ke magana kan sashe na 9 na rahoton Ayo Salami da ake zargin ya samu shugaban hukumar EFCC na yanzu da laifi.
Sanarwar ta kuma ce jami'an hukumar ta EFCC sun yi abin da suka yi ne ba tare da sanar da Malami ba sannan sun kasance suna ta faman neman takardu da suke tsammanin na da alaƙa da rahotan na Ayo Salami.
Wannan dai ba shi karon farko na shiga komar EFCC da tsohon ministan ya yi ba, inda ya kwashe kusan mako guda a tsare a ofishin hukumar bisa tuhumar rashawa da cin hanci.
Da me EFCC ke tuhumar Abubakar Malami?

Asalin hoton, Malami/Facebook
Tsohon ministan na Shari'a, Abubakar Malami ya kwashe mako guda a hannun jami'an hukumar EFCC bisa dalilan abin da hukumar ta kira bincike.
EFCC dai ta ce tana binciken tsohon ministan ne kan laifukan da ake zargin sa da su guda uku da suka haɗa da:
- Amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida.
- Safarar haramtattun kuɗade.
- Laifuka masu alaƙa da kadarorin tsohon shugaban ƙasa, Sani Abacha da aka karɓo daga ƙasashen waje da suka kai dala miliyan 346.2
Sai dai kuma tsohon ministan ya yi watsi da zarge-zargen inda ya alaƙanta abin da yake fuskanta daga hukumar ta EFCC da bi-ta-da-ƙullin siyasa.
Bugu da ƙari, Malami ya zargi shugaban hukumar EFCC, Ola Kayode da ƙoƙarin daƙile gaskiyar rahotan da tsohon ministan ya saki kansa a cikin rahoton Ayo Salami.
Shugaban EFCC ya musanta zargin Abubakar Malami, inda ya ce hukumar na aiki ne ba tare da sani ko sabo ba.
Mene ne a takardun da Malami ya saki?
A sanarwar da mai magana da yawun Abubakar Malami ya saki, tsohon ministan ya ce a lokacin da yake ministan Shari'a gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti ƙarƙashin Ayo Salami domin binciken zarge-zargen rashawa da cin hanci da kuma amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida ba a hukumar EFCC.
Ya kuma ƙara da cewa Olukoyede ya yi aiki a matsayin sakatare na kwamitin amma kuma rahoton musamman sashe na 9 ya same shi da laifi.
Hakan ne ya sa Malami ya kokwanta cewa hukumar EFCC wadda Ayo Olukayode ke jagoranta ba za ta yi masa adalci ba, inda ya nemi wata hukumar ta karɓi binciken.
Wane ne Abubakar Malami?

Asalin hoton, Malami/Facebook
Sunansa Abubakar Chika Malami kuma ya riƙe ministan Shari'a na Najeriya a shekaru takwas na mulki tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.
Lauyan mai muƙamin SAN mai shekaru 58 ya yi karatun lauya a jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto.
Malami ya samu tabbacin lauya a 1992 sannan ya zama babban lauya ko kuma SAN a 2008.
Abubakar Malami ya yi takarar gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin jam'iyyar APC a shekarar 2014 amma bai yi nasara ba, kuma bayan nan ne marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin ministan Shari'a.










