Real Madrid ta kai daf da karshe a Copa del Rey

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta kai zagayen daf da karshe a Copa del Rey, bayan da ta ci Leganes 3-2 a fafatawar da suka yi ranar Laraba a Butarque.

Real ta fara cin ƙwallo ta hannun Luca Modric a minti na 18 da fara wasan, sannan Enderick ya kara na biyu a minti na 25.

Sai dai kafin hutu Leganes ta zare ɗaya ta hannun Juan Cruz, sannan ya farke na biyu, bayan da suka koma zagaye na biyu a bugun fenariti.

Daf da za a tashi daga wasan Real ta kara na uku ta hannun Gonzalo García, hakan ya sa ta kai daf da karshe a Copa del Rey na bana.

Ƙungiyar Santiago Bernabeu ta samu ƙwarin gwiwa, wadda za ta fuskanci Manchester City a zagayen cike gurbi a Champions League.

Real Madrid ta je ta doke Leganes 3-0 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi 24 ga watan Nuwambar 2024.

Ranar 30 ga watan Maris Real Madrid za ta karɓi bakuncin Leganes a wasa na biyu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya daga nan ta je Manchester City.

Ranar Asabar 8 ga watan Fabrairu, Real Madrid za ta buga wasan hamayya da Atletico Madrid a La Liga.

Real ce ta ɗaya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Atletico mai 48, bayan wasan mako na 22 a La Liga.

Daga nan Real Madrid za ta je Manchester City, domin fafatawa a wani wasan hamayya a karawar cike gurbi a Champions League ranar Talata 11 ga Fabrairu.

Ita kuwa Leganes za ta je Valencia a wasan La Liga ranar Lahadi 9 ga watan Fabrairu, sannan ta karɓi bakuncin Alaves a dai La Liga ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu.

Ƴan wasan Real Madrid da suka kara da Leganes:

Masu tsare raga: Lunin, Fran González da kuma Sergio Mestre.

Maasu tsare baya: Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Mendy, Jacobo, Asencio, Lorenzo da kuma Mario Rivas.

Masu buga tsakiya: Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos da kuma Chema.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Rodrygo, Endrick, Brahim da kuma Gonzalo.