Hisba ta ce ta fara shirye-shiryen auren Maiwushirya da Ƴarguda

Ashiru Idris Maiwushirya tare da Basira Ƴargudaliya

Asalin hoton, FB/Maiwushirya

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar Hisba a jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta fara shirye-shiryen auren sanannun ƴan tiktok da ke jihar, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Maiwushirya da Basira wadda ake yi wa laƙabi da Ƴarguda, bayan umarnin da kotu ta bayar na yin hakan.

A ranar Litinin ne wata kotun majistare a Kano ta bai wa Hisbah umarnin ɗaura aure tsakanin matasan biyu, bayan wasu bidiyoyi da suka riƙa wallafawa a shafukan sada zumunta da ke nuna kusanci a tsakaninsu.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan an gurfanar da matasan biyu a gabanta, bisa zargin su da yaɗa bidiyoyi na 'rashin ɗa'a' a shafin sada zumunta.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Halima Wali ta ce rashin gudanar da auren a cikin lokacin da ta ayyana zai zama "saɓa umarnin da ta bayar".

A saƙon da ya aika wa BBC, mataimakin shugaban Hisba a jihar Kano, Aminudeen Mujahideen ya ce hukumar ta yi maraba da hukuncin kotun, kuma hakan zai taimaka wajen kare al'adun al'umma.

"Shi (Maiwushirya) ya nuna yana son ta, ita (Basira) ma ta nuna tana son ta aure shi, kuma tuni kotu ta amsa wannan buƙatu nasu," in ji Mujahideen.

Ba wannan ne karon farko da hukumomi a Kano, jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya suka ɗauki mataki kan ayyukan matasa masu wallafe-wallafe a shafukan sada zumunta ba, musamman ma tiktok.

A baya, Hisbah - wadda hukuma ce da ke tabbatar da ɗa'a da tabbatar da aiki da hukunce-hukuncen addinin Musulunci - ta kama tare da gurfanar da sanannun masu amfani da shafukan sada zumunta a kotu, bisa zargin ayyukan da suka saɓa da al'ada da kuma koyarwar addinin Musulunci.

Ko a cikin watan Nuwamban 2023, ayyukan hukumar a jihar Kano ya janyo muhawara, bayan hotuna da bidiyon yadda hukumar ta riƙa kai samame a wasu gidaje tare da kamen mata da matasa sun karaɗe shafukan sada zumunta.

Shirin auren Idris Maiwushirya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin bayanin da ya yi wa BBC, Aminudden Mujahideen ya ce za a yi wa Idris da Basira aure ne irin tsari na auren gata, wanda hukumar ta saba aiwatarwa.

A cewarsa mataki na farko shi ne tantance asalin mutanen biyu da za a yi wa auren "su wane ne su, su wane ne iyayensu?"

"Babban kwamanda (Aminu Daurawa) tuni ya tura Zamfara domin a binciko iyayen ta (Basira) ya taho mana da su, kasancewar su ne za su yi mata wakilci a lokacin ɗaurin auren," in ji Mujahideen.

Mataimakin na shugaban Hisbah na Kano ya ce kwamandan Hisbah na jihar Zamfara ne aka bai wa aikin yin hakan.

Haka nan hukumar ta ce ta tura domin a je a yi wa matasan biyu gwajin ƙwaƙwalwa domin tabbatar da lafiyar hankalinsu gabanin auren.

"Kuma za a gwada lafiyarsu ta hanyar gwaje-gwajen HIV (cuta mai karya garkuwar jiki) da Hepatitis B (cutar hanta), da genotype (halittar gado) da ciwon sanyi (STI), da kuma gwajin ciki.

Hukumar ta Hisbah ta kuma ce yanzu haka an samu waɗanda suka bayyana aniyar biyan sadakin auren, yayin da kuma ake sa ran gwamnatin jihar za ta iya taimakawa wajen samar musu da muhalli "kasancerwar a cikin sharaɗin da ta bayar, ta ce sai yana da gidan kansa".

Mujahidideen ya bayyana cewa za a yi auren ne "a ƙasa da wata biyu, kamar yadda umarnin kotu ya nuna."

Ko auren zai yi ƙarko?

Ɗaya daga cikin abubuwan da jama'a ke tambaya a kai shi ne batun dorewar auren idan har hukumomi sun ɗaura shi, sai dai jami'in na hukumar Hisbah ya ce akwai matakan da suka ɗauka na ganin auren ya ɗore.

"Auren Hisbah aure ne na mutu-ka-raba, saboda aure ne wanda kotu za ta tabbatar, wanda za mu sa hannu shi ma ya sa hannu, sannan kuma akwai sharuɗɗa.

"Duk inda aka yi irin wannan aure, ba za ka je nan gaba ka ce ka sake ta ba, aure na ya zama dimun-da'imun da izinin ubangiji," in ji Mujahideen.