Tuchel ya raba maki da Tottenham karon farko a haduwa ta shida

Chelsea ta raba maki da Tottenham, bayan da suka tashi 2-2 a wasan hamayya a karawar mako na biyu a Premier League a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Sabon dan kwallon da Chelsea ta dauka a bana, Kalidou Koulibaly shi ne ya ci kwallo a minti na 19 da fara tamaula.

Ya zama na farko dan wasan Chelsea da ya ci kwallo a wasan farko a Premier League a kungiyar tun bayan Michael Essien a Maris din 2006.

Bayan da suka koma karawar zagaye ne Tottenham ta farke ta hannun Pierre-Emile Hojbjerg, sai dai minti tara tsakani Chelsea ta kara na biyu ta hannun Reece James.

Sai dai kuma daf da za a tashi Tottenham ta farke ta hannun Harry Kane, kwallo na 184 kenan da ya zura a raga a Premier League.

Dan wasan tawagar Ingila ya yi kan-kan--kan da Sergio Aguero a tarihin yawan zazzaga kwallaye a raga a kungiya daya, kowanne yana da 184.

Kawo yanzu Thierry Henry ne kan gaba a cin kwallo 43 a Premier League a wasan hamayya na kungiyoyin birnin Landan, sai Harry Kane mai 42.

Haka Jermain Defoe ne mai tarihin kwallo 15 da ya zura a daf da za a tashi wasa a Premier League, sai Kane mai 13.

To sai dai kuma an bai wa kociyan Tottenham, Antonio Conte da na Chelsea, Thomas Tuchel jan kati bayan tashi daga karawar.

Karo na shida kenan da kociyan Chelsea Thomas Tuchel ya hadu da Tottenham a wasan da ya fuskanci karawar ta hamayya ta birnin Landan.

Tuchel ya fara jan ragamar Chelsea ranar 26 ga watan Janairun 2021, bayan da Paris St Germain ta sallame shi.

Wasannin da Tuchel ya doke Tottenham

Kakar 2022/23

Premier League ranar Lahadi 14 ga watan Agustan 2022

Kakar 2021/22

Premier League ranar Lahadi 23 ga watan Janairun 2022

Chelsea 2 – 2 Tottenham

League Cup ranar Laraba 12 ga watan Janairun 2022

Tottenham 0 – 1 Chelsea

League Cup ranar Laraba 5 ga watan Janairun 2022

Chelsea 2 – 0 Tottenham

Premier League ranar Lahadi 19 ga watan Satumbar 2021

Tottenham 0 - 3 Chelsea

Kakar 2020/2021

Premier League ranar Alhamis 4 ga watan Fabrairun 2021

Tottenham 0 – 1 Chelsea