Wace dabara ta rage wa Man United bayan shan kashi a hannun Grimsby?

    • Marubuci, Simon Stone
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Manchester United reporter at Blundell Park
  • Lokacin karatu: Minti 4

Rshin ƙwarin gwiwar da ake da ita kan tawagar Manchester United da kocinta Reuben Amorim na ƙara dagulewa bayan rashin nasarar da suka yi a hannun ƙungiyar Grimsby Town.

United ƙungiya ce da ke da kwarjinin da ba a yi tunanin za ta iya yin rashin nasara a hannun wata ƙungiya da ke buga gasa mai daraja ta huɗu ba, amma sai ga shi hakan ya faru.

Babu wanda ya taɓa tunanin ya kamata United ta kammala gasar Premier a mataki na 15, aƙalla ba a wannan zamani ba, amma kuma hakan ta faru a kakar da ta gabat.

To duk da haka ko akwai wani kyakkywan sauyi da aka samu daga kakar da ta gabata zuwa yanzu? Babu alamar hakan.

Babbar tambayar ita ce: me ake yi domin farfaɗo da ƙungiyar?

Ba Amorim ne kaɗai zai zauna ya nemo wannan amsa ba. Ɗaya daga cikin masu hannun jari a ƙungiyar Sir Jim Ratcliffe da shugaban ƙungiyar Omar Berrada da darakta Jason Wilcox su ne ya zama wajibi a kansu su zauna su lalubo abin da zai ceci ƙungiyar.

Su ne wadanda suka yanke shawarar bai wa Erik ten Hag sabon kwantaragi a 2024, sannan kuma suka kore shi daga muƙamin cikin ƙasa da wata uku bayan haka.

Su ne wadanda suka ƙiɗaukar shawara Dan Asworth kan cewa a miƙa horas da ƙungiyar ga Thomas Frank ko Marco Silva ko Graham Potter a matsayin wanda zai maye gurbin ten Hag.

Su ne suka matsa kan a kawo Amorim. Berrada ne ya hau jirgi takanas ya tafi Portugal ya ce wa Amorim dole ya taho United yanzu-yanzu, bayan da Amorim din ya roƙi cewa a bar shi ya kammala kakar a Sporting.

Ya yi nasara a wasa 17 cikin 45, bakwai daga cikin wasannin da ya yi nasara su ne na gasar Europa a kara da ta gabata.

Ƙarara, wannan ba shi ne sakamakon da shugabannin United suka so gani ba, duk da goyon bayan da aka ba shi na kashe maƙudan kuɗaɗe har fam miliyan 200 domin sayen ƴan wasan gaba ba gabanin wannan kaka duk kuwa da rashin kataɓus a Premier.

Kusan irin haka ta faru da Ten Hag a lokacin da ƙungiyar ta yanke shawarar korar shi, bayan an kashe kimanin fam miliyan 200 wajen sayen ƴan wasa irin su Leny Yoro, Matthijs de Ligt, Noussair Mazraoui, Manuel Ugarte da Joshua Zirkzee.

A kakar da ta gabata Amorim ya yi wata magana da ke nuna cewa yana son ya bar ƙungiyar, amma aka shawo kansa ya tsaya.

Akwai alamun cewa za a iya jin labari maras daɗi bayan kalaman da ya yi a ƙarshen wasan da United ta sha kashi ranar Laraba.

"Ina jin cewa ƴan wasana sun nuna abin da suke so ƙarara," kamar yadda ya faɗa.

"A'a," amsar da Amorim ya bayar ke nan lokacin da aka tambaye shi ko ya gano matsalar da ta sa suka sha kashi a filin wasa na Blundell Park.

Ya ƙara da cewa "amma ni ne mai horsawa. Ya kamata a ce na iya gano mece ce matsalar."

Kafin fara wannan kaka, Amorim ya yi bayani kan yadda bai iya ɓoye fargabar da ke cikin zuciyarsa a lokuta daban-daban, inda ya yi alƙawarin rage bayyana dukkanin abin da ke cikin zuciyarsa a lokacin tattaunawa da manema labarai.

Sai dai duk da haka, kalamansa ba su da wani ƙarfafa gwiwa game da farfadowar United, kamar yadda a ywan lokuta ake gani a rashin karsashinsa.

Wannan babbar matsala ce.

Wasu daga cikin rashin nasarorin United ƙarƙashin jagorancin Amorim

  • Yawan nasarar da Amorim ya samu a gasar Premier bai taka kara ya karya ba, kashi 24.7% ne kacal
  • Shi ne wanda ya fi ƙarancin samun nasara a wasanni tsakanin kococin United tun bayan tafiyar Sir Alex Ferguson, David Moyes ke biye masa a mummunan tarihin da kashi 50%
  • United ta samu nasara ne a wasa bakwai kacal na gasar Carabao cikin wasa 29 ƙarƙashin Amorim
  • Maki 42 da ƙungiyar ta samu a a gasar Firimiya a kakar da ta wuce shi ne mafi muni a tarihinta na gasar
  • Bayan ƙarewa a mataki na 15 sun kuma gama ne ƙwallo 44 kacal.