Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina makomar arewacin Najeriya idan matsalar tsaro ta hana yara karatu?
Matsalar ƴanbindiga a yankin arewacin Najeriya, babbar damuwa ce da ta shafi fannonin ci gaban yankin da dama.
Ƴanbindigar sun kwashe shekaru suna ƙaddamar da hare-hare a wasu yankunan arewacin ƙasar tare da kama mutane domin neman kuɗin fansa.
A wasu lokuta ƴanbindigar kan kai hare-harensu kan makarantu tare da sace ɗalibai.
Matsalar ta sa an rufe makarantu masu yawa na furamare da sakandire a jihohin da matsalar ta fi ƙamari.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ta gano cewa akwai makarantu furamare da na sakandire aƙalla 180 da aka rufe sakamakon matsalolin tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.
Shi ma kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel cikin wani bincike da ya gabatar ya gano cewa daga 2020 zuwa 2025 an rufe makarantu kimanin 210 sakamakon matsalar tsaro a rewacin Najeriya.
A wata hira da BBC shugaban Kamfanin, Kabiru Adamu ya ce a wasu wuraren an sauya wa ɗaliban da lamarin ya shafa makarantu, yayin da a wasu wuraren kuma ɗaliban suka haƙura da karatun.
A wasu jihohin an mayar da wasu makarantun sansanin ƴangudun hijira, yayin da wasu suka koma sansanin jami'an tsaro, wasu kuma suka koma sansanin ƴanbindigar.
Rufe makarantu ya jefa miliyoyin yara cikin halin rashin zuwa makaranta domin samun ilimi, lamarin da ya sa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin ya ƙaru matuƙa.
Shin mece ce makomar waɗannan yara da ma al'ummar yankin baki ɗaya?
Wacce illa matsalar za ta yi wa yaran a yanzu?
Dakta Aliyu Usman Tilde tsohon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya ya ce babbar barazana ce a yanzu a ce yaro baya zuwa makaranta a wannan zamani da ake ciki.
''Matsawar mutum bai yi ilimi ba, to bambancinsa da dabba babu yawa'', in ji shi.
Ya ce duk wanda ya tashi babu ilimin addini ko na zamani to rayuwarsa na cikin gagari.
''Hasali ma zai zame wa al'ummar da yake rayuwa a cikinsu gagarumar matsala'', kamar yadda ya bayyana.
Shi ma Dakta Kabiru Adamu ya ce hakan zai shafi ingancin rayuwar yaran, saboda rashin ilimin, wanda shi ne gishirin rayuwa.
Mece ce makomarsu?
Tsohon kwamishinan ilimin na jihar Bauchi ya ce duk yaron da bai yi ilimi ba, to ba shi da wata makoma mai kyau.
A cewarsa akasari wuraren da ake samun irin wannan matsalar, za ka taras sana'o'in wurin ba su wuce noma da kiwo ba.
''Kuma ko shi noma da kiwon idan babu ilimi ba za su yiwu yadda ake buƙata ba''.
Ya ci gaba da cewa duk sana'ar da mutum zai yi a yanzu tana buƙatar aƙalla ilimin boko na matakin farko.
Galibi irin waɗannan yara za su ƙare cikin halin rashin sanin ciwon kai da shaye-shaye da sace-sace da ma dabar siyasa kamar yadda Dakta Tilde ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa babu wata gwagwarmayar rayuwa da za su iya yi domin su taimaki kansu ko al'umma, saboda ba su da tushe mai kyau.
Babu wani fata da yaran suke da shi zuwa gaba matuƙar ba su samu ilimi ba, saboda babu wani muradi da za su sanya a gaba, a cewarsa.
Mece ce makomar arewa a nan gaba?
Hausawa na cewa yara manyan gobe, kuma idan yaran ba su samu ilimi ba, da akwai yiwuwar gobe za a samu manyan jahilai, kamar yadda masana ke bayani.
Dakta Tilde ya ce rashin ilimin yara babu abin da zai haifar sai cutarwa ga al'ummar gobe.
''Rayuwa ce za a samu ta ci baya, saboda babu masu ilimi a cikin al'ummar'', in ji shi.
Sannan ya ce aikata miyagun laifuka za su yawaita a yankin, matsawar ba a magance wannan matsala ba.
''A yankunan da ake da wadatuwar ilimi ma ya aka ƙare da shaye-shaye da sace-sace, da bangar siyasa, ballantana al'ummar da ba su yi karatu ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
A nasa ɓangare Dakta Kabiru Adamu ya ce abin da hakan ke nufi shi ne nan gaba yankin zai fuskanci koma-baya tsakanin takwarorinsa sauran yankunan ƙasar.
Me ya kamata gwamnati da al'umma su yi?
Dakta Tilde ya ce babban abin da ya kamata al'umma su yi shi ne zaman lafiya.
''Abu na farko shi ne al'umma su yarda su zauna lafiya da juna, babu abin da ya fi zaman lafiya, idan babu zaman lafiya babu abin da za a iya yi ciki har da zuwa makaranta'', in ji shi.
Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum din ya ce yankin arewacin Najeriya yanki ne daya yi fice da tarihin zaman lafiya a baya.
''Amma a yanzu ga shi al'amura na neman sauyawa, ana neman a dagula yankin ta hanyar kawo tashin hankali, don haka zaman lafiya shi ne babban abin da ya kamata a samar tukunna'', in ji shi.
A gefe guda yana da kyau gwamnati ya ti yi bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da smar da tsaron yankin, domin yara su je makaranta.
Haka ma Dakta Kabiru Adamu ya ce yana da kyau masu ruwa da tsaki a yankin da ƴankasuwa su yi iya baƙin ƙoƙarinsu don ganin sun kawo gyara a yanki.
''Matsalar ba ta gwamnati ba ce ita kaɗai kowa da irin rawar da ya kamata ya taka domin magance wannan matsalar'', in ji shi.
Ya yi kiran haɗin kai tsakanin al'umma domin kawar da wannan matsala.