Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland ya zama dodon raga a wannan kaka, ko akwai wanda zai ja da shi?
Erling Haaland ya ci ƙwallo 13 wa Manchester City da kasarsa Norway daga fara kakar bana, har da wadda ya zura a ragar Arsenal ranar Lahadi a Premier League.
Wasa takwas jimilla ya buga kawo yanzu, ko hakan na nufin zai lashe takalmin zinare a fagen cin ƙwallaye a nahiyar Turai da Premier League?
Ƙwazon da Haaland ya fara a kakar nan
Haaland ya fara da zura ƙwallo biyu a raga a wasan da Manchester City ta caskara Wolverhampton 4-0 a gasar Premier League ranar 16 ga watan Agusta.
Ya kuma ci ƙwallayen a minti na 34 da kuma a 61 a karawar da aka yi a Molineux a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Sai dai ɗan wasan tawagar Norway, bai ci ƙwallo ba a mako na biyu a wasan da Tottenham ta doke City 2-0 a Etihad, sai dai daga lokacin ya ci ƙwallaye a dukkan wasannin da ya buga na gaba.
Ranar 31 ga watan Agusta, City ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Brighton a wasan mako na uku a Premier League, Haaland ne ya fara cin ƙwallo tun kafin hutun rabin lokaci.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Brighton ta farke ta kuma kara ta biyu da ta kai ta haɗa maki ukun da take bukata.
Norway ta buga wasan sada zumunta da Finland ranar 4 ga watan Satumba, inda Norway ta yi nasara 1-0, kuma Haaland ne ya ci ƙwallon a bugun fenariti a minti na 17 da take leda.
Daga nan Haaland ya zura biyar a ragar Moldova lokacin da Norway ta sharara 11-1 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya - inda mai tsaron raga, Cristian Avram ya ce Haaland ya je ya bashi hakuri kan yawan ƙwallaye da Norway ta zura musu.
Da ya koma Ingila, bayan buga wasannin neman shiga gasar kofin duniya, Haaland ya zura ƙwallo biyu a ragar Manchester United a wasan hamayya a Premier League mako na huɗu ranar 14 ga watan Satumba.
Daga nan City ta fara buga Champions League wasan farko a cikin rukuni da doke Napoli 2-0 ranar 18 ga watan Satumba, inda Haaland ne ya fara cin ƙwallo da suka koma zagaye na biyu a Etihad.
Ranar Lahadi Haaland ya fara cin Arsenal ƙwallo a Premier League wasan mako na biyar, kuma na biyar da ya ci Gunners a karawa ta bakwai.
Sannan ƙwallo na 20 daga wasa 21 da ya ziyarci duk wata ƙungiyar tamaula da take birnin Landan.
Kenan Haaland ya ci ƙwallo shida a Premier League, sannan bakwai a City har da wadda ya zura a ragar Napoli a Champions League, jimilla ya ci 13 a karawa takwas a ƙungiya da kasarsa.
Tarihin da Haaland ya kafa a cin ƙwallaye
Wannan kakar Haaland bai fara da kokari ba duk da cin ƙwallo shida a wasa biyar a Premier League tun bayan da ya koma Etihad a 2022.
A kakarsa ta farko ya zura ƙwallo tara a raga a wasa biyar da fara kakar gasar babbar tamaula ta Ingila, sai kuma ya ci bakwai a wasa biyar da fara kakar 2023/24.
Amma a bara 10 ya zura a raga da fara wasan Premier League biyar har da uku rigis da ya ci Ipswich Town da kuma West Ham United.
A kakar nan ya zura ƙwallo biyu a raga a wasa shi ne a Wolverhampton a Molineux a Premier League da kuma Manchester United a wasan hamayya a Etihad.
Ƙwallo biyar da Haaland ya sharara a ragar Moldova ya yi kan-kan-kan da tarihin da ya kafa a baya a City a fafatawa da RB Leipzig a 2022/23 Champions League da wasa da Luton a FA Cup a 2023/24.
Karo 26 yana cin ƙwallo uku rigis a raga a tarihi, kuma na biyar a tawagar Norway.
Ya ci ƙwallo uku rigis a City da karo uku yana zura uku rigis a raga a Norway tun daga lokacin da ya koma taka leda a Etihad.
Ranar 10 ga watan Mayun 2022, City ta sanar da sayen Erling Haaland daga Borussia Dortmund.
Ƙyautukan da Haaland ya lashe a City a Premier League
- Ɗan wasan Premier League da ya fi ƙwazo: 2022–23
- Matashin ɗan wasan Premier League da ya fi ƙwazo: 2022–23
- Ɗan wasan da ya fi cin ƙwallo: 2022–23, 2023–24
- Fitatcen ɗan wasan Premier League na watan: Agustan 2022, Afirilun 2023 da A 2024
Kofunan da ya lashe kawo yanzu
Red Bull Salzburg
- Austrian Bundesliga: 2018–19
- Austrian Cup: 2018–19
Borussia Dortmund
- DFB-Pokal: 2020–21
Manchester City
- Premier League: 2022–23, 2023–24
- FA Cup: 2022–23
- FA Community Shield: 2024
- UEFA Champions League: 2022–23
- UEFA Super Cup: 2023
Norway U17
- Syrenka Cup: 2016