Yadda aka yi bikin Kirsimeti ba tare da armashi ba a mahaifar Yesu Almasihu

- Marubuci, Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
- Aiko rahoto daga, Bethlehem
- Lokacin karatu: Minti 3
Garin Bethlehem da ke yankin Yamma da Kogin Jordan na tunƙaho da zama cibiyar gudanar da bukukuwan Kirsimeti ta duniya to amma a bana lamarin ya sauya.
Akwai masu ziyara ƙalilan a daidai lokacin da bukukuwan ke kan ganiyarsu. Babu annashuwa da hada-hada a kan titunan birnin kamar yadda aka saba a lokacin bikin Kirsimeti, misali babu manyan bishiyoyin bikin Kirsimeti da aka saba sanyawa a kofar cocin asali ta Nativity wadda aka yi yakinin cewa a nan ne aka haifi Isa Almasihu.
An soke bukukuwan Kirsimetin a karo na biyu a jere saboda yaƙin Gaza. Kiristoci ƴan Falasɗinu na halartar tarukan addini ne kawai da tarukan iyalai.
"Ya kamata ya zama lokacin farin ciki da biki," kamar yadda Rabaran Dr Munther Isaac, wani fasto a garin ya shaida. "To amma Bethlehem gari ne da ke nuna damuwa ga halin da ƴan uwanmu na Gaza ke ciki."
A wannan cocin, akwai wata ƴartsana mai siffar Isa Masihu da aka ɗora a kan ɓuraguzai. Kafin ranar Kirsimeti an mayar da hankali wajen addu'o'in samun zaman lafiya a Gaza.
"Abu ne mai wuya a yi amanna cewa wani bikin Kirsimeti zai zagayo ba tare da an dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza ba," in ji Isaac a cikin huɗubarsa."Mahukunta sun ƙyale hakan ya ci gaba. A wurinsu Falasɗinawa ba su da muhimmanci."
Isra'ila ta musanta zargin kisan kiyash a Gaza sannan alƙalai a kotun duniya har yanzu ba su kai ga kammala tuhumar Isra'ila da laifukan kisan kiyashi ba wanda ƙasar Afirka ta Kudu ta shigar.
Da dama Kiristocin Bethlehem da na haɗu da su na cikin rashin fata sannan suna nuna gazawar sauran garuruwan Kiristoci a duniya na ƙin yin magana kan Gaza.
"Mahaifiyata ta shaida min cewa abin da muke gani a talbijin ba ya nuna hakiƙanin kaso ɗaya na abin da ke faruwa a Gaza, in ji Dr Yousef Khouri, masanin tauhidi, wanda asalinsa ɗan Gaza ne.
Mahaifansa da ƴaruwarsa na daga cikin ɗaruruwan Kiristoci da suka kwashe watanni 14 suna neman mafaka a coci.
"An wahalar da su da yunwa kamar yadda ɗaukacin Gaza ya fuskanta. Kuma sun sha fama da rashin barci sabod aƙarar bama-bamai da kugin jirage mrasa matuƙa da ke shawagi a sararin samaniyya sannan kuma ba su samu kulawar kirki ba dangane da asibitoci," ya ƙara fadi.
"Mun rasa abokai da ƴanuwa."

Asalin hoton, Reuters
A Gaza, fiye da mutum dubu 45 ne aka kashe a yakin da Isra'ila ke yi tun bayan harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Alƙaluman da ma'aikatar lafiya ta Gaza da ke goyon bayan Hamas ta fitar ne Majalisar Ɗinkin Duniya suka dogara da sauran su.
Isra'ila ta ce harin na 7 ga watan Oktoban 2023, Hamas ta kashe Isra'ilawa da ƴan ƙasar waje mutum 1,200, sannan sun yi garkuwa da mutum 250.
An samu tashin hankali a Yamma da kogin Jordan saɓanin yaƙin. Isra'ila ta fito d asabbin takunkumai a kan tafiye-tafiyen Falasɗinawa sannan ta soke dubban takardun kasancewar Falasiɗinawan na aiki a birnin Qudus da sauran wuraren ƴan kama wuri zauna na Yahudawa.
Tattalin arziƙin na fama da matsala musamman a Bethlehem, wanda ya dogara ga yawon buɗe idanu wanda yake gab da tsayawa. Masu rakiya na tsaye a bakin cocin asali ta Nativity inda suke bai wa tattabaru abinci.

Da dama daga cikin Kiristoci da Musulmin da ke Bethlehem sun yi ƙaura a baya. Sakamakon fuskantar barazana da yunƙurin Isra'ila na ƙara faɗaɗa ƙasarta, Falasɗinawa na neman ƙasarsu mai cin gashin kanta, saboda fargaba da rashin tabbas na abin ka iya zuwa a nan gaba.
To sai dai wata ƙungiya a Bethlehem da ke ƙoƙarin samar da sauyi, tana raba wa mabuƙata abinci. Ba abuƙatar tallafin gwamnati a nan, masu aikin sa-kai na karɓar tallafi daga jama'a ciki har daga mutanen da ke zaune a ƙasashen waje.











