Waɗanda suka yi galaba da marasa ƙoƙari a Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ben Miller and Rob Stevens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
Bayan da Ivory Coast ta lashe kofin nahiyar Afirka 2023, ana ganin cewa gasar ta wannan karo itace mafi ƙayatarwa a tarihi.
Akwai abubuwan ban mamaki daki-daki a labarin hanyar da Ivory Coast ta bi kamar wani abu na almara ko shirin fim da ta kai ta ga lashe kofin bana.
BBC Sport Africa ya yi duba na tsanake kan wadanda suka yi galaba da wadanda suka ci karo da koma baya a kwana 30 da aka buga wasannin da ba a mance da shi ba a babbar gasar tamaula ta nahiyar Afirka.
Zakaru - Ivory Coast da Emerse Fae
Sebastien Haller, wanda ya koma taka leda bayan wata 13 da aka yi masa aiki kan ciwon daji, shi ne ya ci kwallon da ya kai Ivory Coast wasan karshe a karawar da suka yi da DR Congo.
Haka kuma ɗan wasan Borussia Dortmund shi ne ya zura kwallo na biyu a ragar Najeriya da ya kai mai masaukin baki ta lashe Afcon na 2023.
Haka kuma nasara ce mai girma ga kociyan riƙon ƙwarya, wanda ya ja ragamar wasa hudu, kuma manya a fannin tarihin horar da tamaularsa.
''Wani abu ne fiye da na almara,'' in ji Emerse Far, bayan farke kwallon da Nigeria ta ci Ivory Coast, sannan ta kara na biyu ta lashe kofin a wasan karshe.
''Idan na tuna dukkan halin da muka tsinci kanmu, mun kasance ƴan sa'a. Mun jire da kuma fuskantar kalubalen da muka fuskanta.
Tawagar Ivory Coast ta kori kociyanta Jean Louis Gaset, bayan da kaɗan ya rage a yi waje da ita daga karawar rukuni - sannan ta fitar da mai rike da kofin Senegal a bugun fenariti a karawar zagaye na biyu.
Sannan kasar ta ci kwallo daf da za a tashi a fafatawar daf da na kusa da na karshe a minti na 122.
Yanzu abin da ake jira shi ne ko kociyan mai shekara 40 zai karbi jan ragamar tawagar Ivory Coast?, batun da bai yadda ya tattauna ba tun kan wasan karshe.
''Maganar gaskiya ita ce na bukaci mahukunta da kada su yi min magana kan makoma ta bayan kammala gasar,'' in ji Fae.
Mai masaukin baki

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Ivory Coast ta kashe sama da dala biliyan daya wajen karbar bakuncin wasannin ciki har da gida sabbin filin wasa hudu da yi wa biyu gyara.
An kuma yi gyara ko sabon gini a filayen sauka da tashin jirgin sama da hanyoyi da otal a manyan birane biyar a Ivory Coast da ya hada da Abidjan da Bouake da Korhogo da San Pedro da kuma Yamoussoukro.
An yi murna da yawa a kasar da ta dauki bakuncin wasannin, inda za kake ganin riguna masu launin ruwan goro a ko'ina a fadin kasar da kuma suke halartar filaye da yake cika maki, wadanda da farko ba a samu ƴan kallo da yawa ba.
An samu ci gaban sufuri da aka samu karin kudin shiga a yawan bude ido, yayin da shugaban kasar Alassane Ouattara ya shiga cikin ƴan wasa don murnar lashe Afcon a kasar kuma karo na uku jimilla.
Daga nan ne dubban magoya baya suka kashe kwarkwatar ido a lokacin da tawagar ta zagaya birnin Abidjan da kofin a budadɗiyyar mota ranar Litinin.
Wadanda suka yi bazata
Gasar Afcon ta bana an yi abin ban mamaki, inda Equatorial Guinea ta vaskara mai masaukin baki, Ivory Coast, kuma ta ja ragamar rukunin farko a rukuni na daya mai dauke da Najeriya.
Haka itama Cape Verde ta yi ta daya a rukunita duk da fitattun kasashen da ta kara da su.
Namibia da Angola suna daga hudu masu rauni daga kasashe 24 da suka je Ivory Coast, amma sun kai zagaye na biyu, yayin da Mauritania ta ci wasan farko a Afcon a tarihi.
Afirka ta Kudu ta dagula lissafi Morocco a hanyarta ta zuwa ƴan hudun karshe.
Ƴan kallo
Gadar Afcon ta 2023 an ci kwallo 119 kenan ana zura 2.29 a raga a kowanne wasa. Gasar da ka zazzaga ƙwallaye a raga ita ce da a ci 2.38 a duk karawa a 2012.
Caf ta ce sama da mutum biliyan biyu suka kalli gasar a talabijin - kenan wasannin gasar da aka fi kallo a tarihi kenan - inda kasashe 173 suka kalli karawar karshe.
An ci kwallaye a daf da za a tashi daga wasa, inda rukuni na biyu aka fi samun hakan musamman a minti na 89, fiye da irin abinda ya faru a 2021.
Kwallo hudu da golan Afirka ta Kudu, Ronwen Williams ya tare ya kara fito da rawar da masu tsaron raga suka taka a babbar gasar tamaula ta Afirka ta 2023.
William Troost-Ekong
Despite finishing on the losing side, the Nigeria captain was named as player of the tournament following his three goals at the finals.
The 30-year-old scored high-pressure penalties against Ivory Coast in the group stage and South Africa in the semi-final before opening the scoring against the Elephants in the final.
He marshalled a Super Eagles defence which kept four clean sheets, and the centre-back became the first defender to score three goals at a single Nations Cup since Libya's Ali Al-Beshari in 1982.
VAR da alkalan tamauala
Abu ne mai wahala kaga koci ya yaba da hukuncin da na'urar fasahar ta zarar musamman da bai yi wwa kungiyarsa dadi ba - amma kociyan Super Eagles, Jose Peseiro ya yi jinjina a lokacin wasan daf da karshe da Afirka ta Kudu.
Super Eagles na ganin ta ci kwallo na biyu a minti na 85 ta hannun Victor Osimhen, amma sai aka soke ƙwallon sannan aka bai wa Afirka ta Kudu fenariti, maimakon bugun laifin kafin Najeriya ta ci kwallo na biyun.
An yi amfani da na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci VAR kamar yadda ya kamata da hukunce-hukunce da suka da ce ta kuma taka rawar gani a gabaki dayan wasannin.
Wadanda suka kasa taka rawa - Ghana

Asalin hoton, Getty Images
An yi waje da mai kofin Afcon hudu tun daga karawar cikin rukuni, bayan da ta bai wa Cape Verde sadakar ƙwallo a minti na
The four-time champions slid out at the group stage in calamitous style, gifting Cape Verde a 92nd-minute winner and allowing Mozambique to score twice in second-half injury time.
Coach Chris Hughton was duly dismissed, having struggled to ease the pressure his squad had faced to record a first triumph for their country since 1982.
A second successive winless campaign was another meek Nations Cup showing by the Black Stars. Their only solace came when fierce West African rivals Nigeria lost the final.
Tawagogin Arewacin Afirka
Tawaga daga Arewacin Afirka ta kai wwasan karshe daga gasa uku baya, saboda abin mamaki ne da ba a samu daya daga ciki ba da ta kai wasan karshe a bana.
Hudu daga cikin wadanda suka halarci wasannin bana suna daga biyar da ke matakin farko a kan gaba a taka leda cikin tawaga 24 da suka je Ivory Coast.
Sai dai tuni aka yi waje da Algeria, bayan da Mauritania ta doke ta da wasan da Tunisia ta yi rashin nasara a hannun Namibia, wadda take da tazarar gurbi 85 tsakaninta da Tunisia.
A wasan zagaye na biyu a gasar, Afirka ta Kudu ta fitar da Morocco daga wasannin, wadda ta kai zagayen daf da karshe a gasar kofin duniya a Qatar, yayain da Masar mai Afcon bakwai ta yi ban kwana da gasar, sakamakon da DR Congo ta yi nasara a bugun fenariti.
Morocco ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka da za ta gudanar a 2025, wadda za ta yi fatan lashe kofin a karon farko tun bayan wanda ta dauka a 1976.
Mohamed Salah
Bayan da Masar ta yi ta biyu a 2017 da kuma a 2021, ƙyaftin din tawagar ya yi hira da ƴan jarida kan yadda yake fatan kawo karshe shekara 14 ba tare da ya lashe kofin ba
Ɗan wasan Liverpool shi ne ya farke kwallon da Mozambique ta ci Masar da suka tashi canjaras, amma an canja shi a zagaye na biyu a wasa da Ghana, bayan raunin da ya ji.
Daga baya aka sanar da cewar ɗan wasan ya kammala buga wa Masar Afcon, sannan ya koma Anfield, domin yin jinya.
Har yanzu Salah bai koma buga wa Liverpool Premier League, wanda ya kai sshekara 33 a lokacin da za a buga Afcon ta gaba.
Masu horar da tamaula
Chris Hughton shi ne na farko da aka fara kora a Afcon a 2023, daga baya shida daga cikin koci 24 suka bar aiki ko dai an kore su ko kuma suka yi ritaya.
Cikin wadanda aka kora sun hada da na Algeria, Djamel Belmadi da na Tunisia, Jalel Kadri da na Masar, Rui Vitoria sakamakon kasa taka rawar gani.
Shi kuwa Tom Saintfiet ajiye aikin ya yi, bayan da aka fitar da Gambia, ya yin da Guinea-Bissau da Burkina Faso suka yanke shawarar ba za su tsaita kwantiragin Baciro Cande da kuma Hubert Velud.
Shi kuwa Adel Amrouche an dakatar da shi ne bayan da kociyan tawagar Tanzania aka dakatar da shi wasa takwas a hukuncin da Caf ta dauka.











