Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gambia na yunkurin dawo da dokar yi wa mata kaciya
'Yan majalisar Gambia sun jefa kuri'ar da ke amincewa da soke haramci da aka yi kan kaciyar mata, kudirin da zai cire kariyar da milyoyin yara mata ke da shi bisa tsarin doka.
'Yan majalisar da gagarumin rinjaye sun bukaci a soke haramci, inda suke aike da matsayarsu matakin kwamitoci kafin a yi zaɓen karshe nan da wata uku.
Matar Biyar kacal ake da shi daga cikin 'yan majalisar 58, kuma masu suka na cewa maza ne ke kokarin kakabawa mata wannan tsari.
Idan daftarin ya tsallake karatu na karshe, Gambia za ta zama ƙasa ta Farko a duniya da ke cire kariyar da mata ke da shi kan yi musu kaciya.
Ɗaya daga cikin 'yan majalisar, Almammeh Gibba - wanda shi ye kirkiro wannan daftarin, ya shaidawa BBC cewa wannan tsarin bai taba cutar da jikin wata mace ba, abu ne na al'ada, ya shafi kuma addini kuma wannan abu ne da ake yinsa tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
Ya kuma ce mutane da dama na son ganin an cigaba da wannan al'ada.
"Akwai abubuwa na cutarwa da dama da ake yiwa jikin mata amma ba za ka ji ƙasashen yamma na magana a kai ba".
Ƙungiyoyi kare hakkin bil adama sun ce soke haramcin wannan doka da ake amfani da ita tun 2015, zai shafe fafutikar da aka kwashe shekara da shekaru domin kare 'yanci mata da kawo karshen yi musu kaciya.
Michele Eken mai bincike a kungiyar Amnesty International ta shaidawa BBC cewa sai da aka shafe shekaru kusan 10 kafin a yi hukunci na farko kan aikata wannan abu.
A shekarar 2023 aka hukunta mutum na farko, kuma wannan ne ya bijiro da batun neman soke dokar baki-ɗaya.
Ta ce "Amma maimakon a sake komawa gidan jiya, ya kamata a ce an karfafa dokar da kokarin ganin a cigaba da hukunta masu karyata, saboda wannan na faruwa ne bayan jarirai 8, ciki harda 'yar kasa da shekara guda, an yiwa kaciya, kuma mata uku da aka hukunta an ci su takarar kusan dala dari biyu.
"Maimako a ce an tsaurara hukucin, sai gashi ana maganar soke dokar baki ɗaya wanda tamkar ana faɗawa yara mata cewa basu da 'yanci".
Wani bincike na baya-bayanan na nuna cewa kashi 73 cikin 100 na mata a Gambia anyi musu kaciya, kuma kashi 65 na wannan adadi anyi musu kaciyar ne tun suna kasa da shekara biyar a duniya.