Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama ƙasurgumin mai hada-hadar miyagun ƙwayoyi na duniya
An damke daya daga cikin kasurguman masu hada-hadar miyagun kwayoyi da aka fi nema a duniya, a birnin El Paso na Texas, a Amurka.
Ismael 'El Mayo' Zambada, tare da wani kasurgumin, El Chapo Guzman, wanda aka daure ya kafa kungiyar nan ta masu hada-hadar miyagun kwayoyi ta Mexico, Sinaloa Cartel,
Ismael ‘El Mayo’ Zambada kusan a iya cewa shi ne wani babban mai hada-hadar miyagun kwayoyi a duniya kuma wanda aka fi nema ruwa a jallo, a nahiyar Amurka ta Arewa da ta Kudu.
Mutumin wanda ya kafa kungiyar nan mai karfin gaske ta miyagun kwayoyi ta Mexico, Sinaloa Cartel, kuma wanda ya kasance daya daga cikin masu miyagun laifin da hukumar yaki da masu ta’ammali da miyagun kewayoyi ta Amurka ta fi nema, wanda tun da dadewa gwamnatin Amurka ta sanya ladan dala miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin inda za a same shi.
Kuma duk da haka El Mayo ya shafe gomman shekaru yana yi wa hukumomi kulli-kurciya, saboda haka ne ma rahoton kama shi a birnin El Paso na jihar Texas ya zo da mamaki na gaske a can Mexico.
Wannan ba karamar nasara ba ce ga hukumomin tabbatar da tsaro na Amurka, musamman ma hukumar yaki da masu ta’ammli da miyagun kwayoyi.
Bugu da kari bayanai na nuna cewa an ma kama shi ne tare da dan
Joaquin ‘El Chapo’ Guzman, mutumin da shi ma ya yi kaurin suna a duniya a harkar miyagun kwayoyi, wanda yake daure yanzu.
Babu dai cikakken bayani na inda ake tsare da su a yanzu, amma dai ana ganin suna nan cikin Amurka.
Yayin da ake ci gaba da samun karin bayanai a kan kamen, babu shakka wannan babban labari ne da gwamnatin Shugaba Biden za ta yi tunkaho da shi a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da jami’an hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Amurka suka samu a tsawon shekaru.
Mutanen biyu za su fuskanci tarin tuhume-tuhume da ke da nasaba da safarar miyagun kwayoyi da halatta kudaden haram da kuma tashe-tashen hankali masu alaka da miyagun kwayoyi a Amurka.