Shugaban Kenya zai kafa tarihi a ziyararsa zuwa Amurka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Barbara Plett Usher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Africa correspondent, Nairobi
Shugaban Kenyan Wiliam Ruto zai zamo shugaban Afirka na farko da za a karrama da tarbar ban-girma yayin ziyarar aiki da zai kai Amurka, karo na farko cikin shekara 15.
Wannan dama ce ga shugaba Joe Biden ya nuna cewa yana tare da Afirika, yayin da Washington ke ƙoƙarin inganta alaƙarta da nahiyar.
Ƙasar Kenya a ƙarƙashin mulkin Mr Ruto tana tafiya a kan tsarin da Washington za ta ji daɗin ƙulla alaƙa da ita.
Amma alaƙarta da sauran manyan ƙasashen da ke ƙawance da Afirika ta yi tsami, musamman yadda Rasha da China ke samun karɓuwa tsakanin ƙasashe rainon Turai.
An yi lokacin da babu wanda zai yi tunanin cewa Mista Ruto zai zamo shugaban da zai samu tarba irin ta karramawa a fadar White House, irin tarbar da sai shugabannin ƙasashe masu alaƙar ƙut da ƙut ke samu.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta tuhume shi da aikata laifin keta haƙƙin ɗan’adam, a bayan zabɓen 2007 a Kenya. Amma shari'ar ta shiririce, kuma tuni Mista Ruto ya samu karɓuwa a matsayin abokin Amurka.
Jakadar Kenya a Amurka, Meg Whitman ta ce a iya sanin ta matakin da majalisar Amurkan ta ɗauka na hana shi damar bayyana a gabanta domin gabatar da jawabi ba wani abu ne da ke nuna rashin cancantar sa ba, asali ma ta ce ba a samu lokacin tsara ziyarar ba ne.
Ms Whitman, tsohuwar shugabar kamfanin eBay, ta yi fice wajen tallata Kenya da janyo masu zuba jari musamman a fannin fasaha.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce: “Idan har da gaske za a dogara ne, ko kuma bunƙasa alaƙa da Afirika, wane ne za a gayyata don samun irin wannan karramawa?
Ta ƙara da cewa: “Shekara 60 ke nan ƙasar Kenya tana ƙawance da Amurka. Babu wata shakka ita ce ƙasar da ta fi kowacce kafuwa a bisa tsarin dimokuradiyya. Shugaba Ruto ya ƙara tabbatar da shi shugaba ne na ƙwarai.”
Kenya a ƙarƙashin Mr Ruto ta kafu a fannin hulɗar diflomasiyya da kasuwanci, wadda kuma Amurka ke fatan ƙawance da ita.
Duk da cewa a cikin gida yana fama da turjiya a kan salon sa wajen shawo kan matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki, wadda matsala ce da ta shafi duniya baki ɗaya, ƙasashen duniya na yi masa kallon ɗan fafutukar magance matsalolin Afirka masu alaƙa da sauyin yanayi da kuma neman a yafe wa Afirka bashin da ake bin ta.
Kenya tana da muhimmancin gaske a fannin tsaron Gabashin Afirika, kuma sanarwar da ta yi cewa za ta tura ƴansandan ta zuwa ƙasar Haiti ta faranta ran Amurka.
A bara, duk shugabannin yankin saharar Afirika babu wanda shugaba Biden ya yi magana da shi ta waya sai Mista Ruto, inda suka tattauna alƙawarin da Kenya ta yi na jagorantar dakarun ƙasashen waje domin kwantar da tarzoma a ƙasar da ta dade tana fama da rikici.
Masu sharhi na ganin cewa ziyarar wata hanya ce ta ɓoye gazawar Mista Biden wajen cika alƙawarin da ya yi na kai ziyara Afirika.
Ya yi alƙawarin ne yayin wani taron Amurka da shugabannin Afirka, a birnin Washington, shekara biyu da suka gabata, inda ya bai wa baƙin nasa tabbacin cewa yana shirye ya yi aiki tare da nahiyar. Amma tun daga wancan lokacin sai ya mayar da hankali a wasu fannonin na daban kamar yaƙin Gaza da kuma na Ukraine.

Asalin hoton, Getty Images
Taron ya biyo bayan wata sanarwa ce da gwamnatinsa ta yi cewa za ta aiwatar da sabbin tsare-tsare da nufin inganta alaƙar Amurka da ƙasashen Afirika ta yadda kowanne ɓangare zai ci gajiya.
Ana iya cewa Mr Ruto ne kan gaba wajen gwajin yadda wannan alaƙa za ta kasance, amma zuwan shi birnin Washington sai hankali ya karkata ga cikas ɗin da Amurka ta samu a yammacin Afirika.
Idan akwai wata ƙasa da za a iya kallo a fahimci ƙalubalen da Amurka ke fuskanta a Afirka to Jamhuriyar Nijar ce.
Tsawon shekaru dakarun Amurka fiye da dubu ɗaya ne aka jibge a sansani biyu, inda suke ƙaddamar da ayyukan tsaro kan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a yankin.
Amma juyin mulkin da aka yi a ƙasar a bara, ya canza salon alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, inda shugabannin mulkin sojin Nijar ɗin suka fi karkata da alaƙar su ga Rasha da kuma Iran.
A cikin watan Maris kuma Amurka ta nemi shiga sabuwar alaƙar tsaro tsakanin ta da Nijar.
Firaiminisyan Nijar ya shaida wa jaridar Washington Post cewa a yayin zaman tawagar Amurka ta riƙa nuna izza da nuna rashin mutumta jama'a. Ya kuma zargi Amurkar da neman tilasta wa ƙasashen Afirka bin tsarin da ta shirya masu, ba wanda suka tsara wa kansu ba.
A makon nan ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta sanar da cewa za ta kwashe dakarun ta daga Nijar daga nan zuwa watan Satumba, lamarin da ya ƙara bai wa Nijar damar ƙara bunƙasa alaƙa da Rasha.

Asalin hoton, AFP
Tsamin dangantaka tsakanin Amurka da Nijar dai na zuwa ne bayan gwamnatin mulkin sojin ta raba gari da tsohuwar uwargijiyarta, Faransa.
Yanayin ya kuma haifar da fargaba a yayin da Amurka ke lalubo hanyar ci gaba da alaƙar tsaro da kuma neman hanyar rage ƙara shaƙuwa da Rasha ke yi da Nijar.
Moscow ta kuma faɗaɗa ƙawancen nata zuwa ƙasashen Sahel da aka yi juyin mulki, inda ta yi masu alƙawarin bayar da tallafin tsaro.
A maƙwafciyar Nijar, Chadi ma, kwanan nan aka tilasta wa dakarun Amurka barin ƙasar bayan gwamnati ta bayyana shakku a kan amfanin su.
Amurka na kuma fuskantar barazana daga wasu manyan ƙasashen duniya a fannin alaƙa da Afirka. A misali, China ta shafe aƙalla shekara 20 tana zuba maƙudan kuɗi a Afirka.
Wani bincike da aka gudanar a bara ya nuna cewa Amurka tana rage ƙarfin faɗa a ji, a Afirika, yayin da China ke ƙara samun ƙawaye tsakanin ƙasashen nahiyar, ga kuma Rasha na ƙara samun karɓuwa.
Gwamnatin shugaba Biden ta zayyana wasu nasarori da ta samu a ƙoƙarin ta na inganta alaƙa da nahiyar Afirka.
Goyon bayan Amurka ya taimaka wa ƙasashen Afirka da dama, wajen samun damar shiga a dama da su a manyan ƙugiyoyin da kuma hukumomi a duniya baki daya.

Asalin hoton, AFP
An kuma jinjina wa gwamnatin Amurkar a bisa zuba jarin da ta yi wajen gina layukan dogo a Angola, da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da kuma Zambia.
Alex Vines, shugaban tsare-tsaren Afirka a Chattahm House da ke birnin London ya ce akwai gyara a ra'ayin da ke cewa ƙasashen yamma na danne ci gaban Afirka
“Wani shugaban Afirika ya taɓa ce mani mu mun gaji da tura mota tana watsa mana ƙasa kawai.''
Daga cikin ƙalubalen da ake fama da su akwai salon jagorancin wasun mu. Idan aka samu shugabanni masu hangen nesa da zuciyar aiki to za a samu irin nasarorin da ake buƙata.
Ana dai ganin shugaba Ruto ya na cikin waɗanda za su iya kawo sauyi, amma kowa yana da irin nasa zaɓin da kuma manufofi.











