Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBC ta bankaɗo irin azabar da ake yi wa mutane don su amsa laifi a Rasha
Tsofaffin fursunoni sun faɗa wa BBC yadda aka dinga yi musu fyaɗe da azabtarwa a gidajen yarin Rasha.
A shekarar da ta gabata ne aka fara yaɗa wani bidiyo na cin zarafin kuma yanzu sun faɗa wa BBC dalilin da ya sa hakan ta faru da kuma yadda suke gwagwarmayar neman 'yancinsu.
Gargaɗi: Wannan maƙalar na ƙunshe da hotunan da ka iya tashin hankalin ku Asibitin gidan yari na Saratov da ke kudu maso yammacin Rasha ya shahara ne a shekarar da ta gabata lokacin da bidiyon cin zarafin fursunoni suka ɓulla.
Alexei Makarov ya san da zaman gidan yarin tun kafin a mayar da shi can a 2018 don ya yi zaman shekara shida kan laifin cin zarafi. Fursunonin da ake kaiwa Saratov daga sauran gidajen yari kan ce ana ƙirƙirar rashin lafiya a kansu saboda kawai a azabtar da su a asirce.
Gidajen yarin Rasha ba su da masu sa ido masu zaman kansu.
Makarov na fama da rashin lafiya da gaske - yana fama da cutar tarin fuka wato TB - kuma ya yi fatan za a ɗaga masa ƙafa. Amma ya ce an yi masa fyaɗe sau biyu a lokacin da yake can.
Waɗanda aka zalunta da kuma ƙwararru na cewa masu kula da gidan yarin ne ke sahhale cin zarafin tare da uzura wa fursunoni ko kuma tilasta musu amsa laifi.
Bidiyon da suka dinga ɓulla sun tilasta wa gwamnati mayar da martani game da zargin azabtarwa. An samu rahotannin azabtarwa a kashi 90 cikin 100 na yankunan Rasha a 2015 da 2019, a cewar wani binciken Proekt. Sai dai ba a ɗaukar mataki da wuri.
BBC ta nazarci dubban takardun kotu tun daga waɗancan shekarun kuma mun gano cewa fursunoni 41 an ɗaure su ne a wuraren da aka fi cin zarafi. Amma da yawansu an yanke musu hukuncin da ba na zaman gidan yari ba.
Makarov ya ce kafron farko da aka fara cin zarafinsa shi ne a Fabarairun 2020.
A cewarsa, ya ƙi yarda da wata maƙarƙashiya kan ɗaya daga cikin shugabannin gidan, saboda haka aka haɗa shi da wani mutum da ya dinga lalata da shi.
"Suna duka na tsawon minti 10, su yayyaga kayana. Sannan kuma su yi min fyaɗe tsawon kusan awa biyu da sandar abin shara.
"Idan na suma sai su kwara min ruwan sanyi kuma su mayar da ni kan teburi."
Wata biyu bayan haka aka sake maimaitawa. An tilasta masa biyan ruble 50,000 ga waɗanda suka zalunce shi kuma aka yi masa fyaɗe da zimmar hana shi magana. Makarov ya faɗa wa BBC cewa an ɗauki zaluncin da aka yi masa a bidiyo.
'Yan bursin ɗin sun san cewa za a iya yaɗa bidiyon ga sauran fursunoni idan ba su aikata abin da ake so su yi ba. Masu aikata fyaɗen su ma fursunoni ne, waɗanda suka yi imanin cewa umarnin wani shugaban gidan suke bi.
Za a ware kiɗa mai ƙarar gaske idan ana azabtar da mutum, a cewar Makarov, don a hana jin ƙarar mutum.
Sergey Savelyev ya fito da bidiyon a asirce na azabar da ake yi wa fursunoni. Ya yi imanin cewa shugabanni ne suka ba da umarnin aiwatar da azabar. Savelyev ya samu damar ganin bidiyon ne saboda an taɓa saka shi ya yi aiki da sashen tsaro na wucin gadi a gidan yarin.
"Ana umarta ta [na raba kyamarori] daga kwamandan masu," a cewarsa. Sannan sai a ba shi umarnin ya adana wasu daga cikin bidiyon cin zarafin mutanen don a nuna wa sashen tsaro, wani lokacin kuma a saka su cikin wata ma'adanar intanet don a nuna wa wasu manya daga ciki.
Bayan ya fuskanci abin da ke faruwa a bayan fage, sai ya fara aajiyewa tare da ɓoye su. "Idan ka gani kuma ka yi shuru hakan na nufin ka amince da abin da ake yi ke nan."
Ɗan gwagwarmaya Vladimir Osechkin, wanda ƙungiyarsa ta Gulagu.net ta wallafa bidiyon cin zarafin, ya lura cewa hanyoyin da azzaluman ke bi an tsara su da kyau.
"Suna bai wa juna alamu, suna aiki cikin tsari kuma su fahimci juna ko da ba su yi magana da baki ba saboda suna bin wani shiryayyen tsari ne."
Bayan bidiyon da Savelyev ya saki, an kama ma'aikatan gidan yari shida amma sun musanta laifin.
Wata biyu bayan haka aka kama shugaban gidan yarin Saratov da mataimakinsa - waɗanda su ma suka musanta hannu a lamarin.
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya sauya shugaban da ke kula da gidajen yari sannan ya sanar cewa "ana buƙatar tsare-tsare" kafin a kawo sauyi.
Kazalika, an yi wa dokokin ƙasar kwaskwarima a watan da ya gabata don a tsaurara hukunci ga duk wanda aka kama da yin amfani da azabtarwa wajen tatsar bayanai.
Sai dai masu fafutikar kare haƙƙi na cewa har yanzu ba a mayar da azabtarwa ita kanta a matsayin laifi ba.
An yi wa ma'aikatan gidan yarin Yaroslavl 11 ɗauri maras tsanani a 2020 amma kuma aka wanke shugabbaninsu.
Wata lauya, Yulia Chvanova da ke nema wa wani adalci, ta ce babban abin da ke jawo azabtarwa ita ce yadda mahukunta ke nacewa akan amsa laifi ko da kuwa wane irin laifi ne.
"Ana ɗaukar amsa laifi a matsayin abu lamba ɗaya kuma mafi muhimmanci." Tana ƙoƙrin nema wa wani ɗan shekara 22 diyya mai suna Anton Romashov, wanda aka azabtar a 2017 saboda ya ƙi amincewa ya amsa laifin da bai aikata ba.
An kama Romashov da laifin mallakar tabar wiwi amma 'yan sanda suka dinga matsa masa sai ya amince yana dillancin ƙwaya - laifin da ya fi girma sosai.
Lokacin da ya ƙi amincewa, sai aka kai shi wani sansanin ajiye masu jiran shari'a a Vladimir da ke yammacin Rasha a 2016.
"An kai ni ɗaki mai lamba 26. Na sani sarai irin yadda wurin yake...saboda na jiyo ihu na fitowa daga wurin tsawon kwanaki."
Mutum biyu ne ke jiran sa a wurin. Ya ce aka wurgar da shi a ƙasa, aka ɗaure ƙafa da hannayensa ta baya kafin daga baya a fara jigbar sa.
Da suka fara cire masa wando sai ya amsa cewa zai amince da duk abin da suke buƙata.
An yanke masa hukuncin shekara biyar a gidan yari duk da cewa ya faɗa wa kotu an azabtar da shi kafin ya amsa.
An fara gudanar da bincike kan kurkukun Vladmir bayan wani fursuna ya kashe wani ma'aikacin gidan yarin saboda ya yi masa barazanar azabtar da shi.
Da aka nemi ma'aikatan su ba da bayanan abin da ya faru, sun ce akasarinsu sun san abin da ke faruwa a ɗaki mai lamba 26.
An yanke wa mutumin da ke jagorantar azabatarwar hukunci a wata ƙara da Anton da wasu mutum biyu suka ba da shaida.
Babbar azabtarwar da aka aikata a ƙasar ita ce a garin Irkutsk da ke yankin Siberia yayin wata zanga-zanga a 2020 a gidajen yari 15.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ce an ci zarafinsu a sansanin, Denis Pokusaev wanda aka ɗaure shekara uku kan laifin zamba, ya ce ma'aikatan bursin ɗin ba sa ɓoye dalilin da ya sa ake azabtar da su.
"Sun faɗa min: 'Kana tunanin mun damu ko aikata laifi ko ba ka aikata ba? Saboda zanga-zanga ka zo nan - saboda haka sai ka yi bayani game da haka.'"
Lauya Yulia Chvanova ta bayyana tsarin da aka fi bi wajen azabtarwar.
"Masu bincike na zaɓar wanda za su titsiye, waɗanne shaidu ko kuma binciike za a bincika... Sai kuma su tuntuɓi ma'aikatan bursin ɗin kuma su ba su sharuɗɗa: 'Muna son wane ya amsa laifinsa.'"
"Cin zarafin ya ci gaba har tsawon wata uku a kowace rana, ban da ranakun ƙarshen mako.
"Su yi dariya, su ci kayan marmari...Akan yi wa mutum fyaɗe da abubuwa iri-iri...Kuma sai dai su yi dariya kawai suna jin daɗi."
BBC ta nemi hukumar gidajen yarin Rasha ta mayar da martani kan zarge-zargen azabtarwa da fyaɗe. Sai dai ba ta ce komai ba.
Masu fafutika sun yi ƙiyasin cewa fursunoni 350 aka azabtar bayan zanga-zangar.
Pokusaev na cikin 'yan ƙalilan 30 da suka yi nasara a kotun da ta ce suna da haƙƙin da za a kalle su a matsayin waɗanda aka zalunta.
Yulia da sauran mutanen da ke gabatar da hujja a shari'ar, an nemi su saka hannu kan wata yarjejeniya kan ba za su bayyana abin da ya faru ba.
Sai dai babu tabbas ko waɗannan abubuwan da aka gano za su kai ga ɗaukar mataki.
Pokusaev ya ce har yanzu abin da ya faru na damun sa.