'Ba kuɗi, ba abinci, kuma ba na iya tafiya' - Yadda tsofaffin ‘yansanda ke rayuwa a Najeriya

Hoton tsohon ɗan'sanda mai suna Adegbehin sanye da kaki da kuma a yanzu da yake kwance a asibiti

Asalin hoton, ADEGBEHIN ADETARAMI

Bayanan hoto, Hoton tsohon ɗan'sanda mai suna Adegbehin sanye da kaki da kuma a yanzu da yake kwance a asibiti
    • Marubuci, Gift Andrew
  • Lokacin karatu: Minti 5

"Na kashe kusan naira miliyan 25 wajen jinya, amma rundunar ƴansanda ba ta taimaka min da ko sisi ba. Na yi jinya a asibitocin Reddington da asibitin koyarwa na Jami'ar Jihar Legas da Duchess da asibitin ƙashi na ƙasa na Legas sannan na je asibitin St Nichola, yanzu kuma maganin gargajiya nake yi a Ikorodu a Legas."

Wannan labari ne na tsohon ɗansanda mai suna DSP Adegbehin Adetarami da yake kwance yana jinya a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Adetarami ɗaya ne daga cikin tsofaffin ƴansandan Najeriya da suke da ƙorafe-ƙorafe kan rundunar ƴansandan.

Ƴansandan Najeriya sun daɗe suna ƙorafin yanayin aikin, musamman kan walwalarsu bayan ritaya, har suka gudanar da zanga-zanga a watan Yulin 2025 saboda ƙarancin fansho da wasu haƙƙoƙinsu da suka ce suna nema.

Wannan ya sa BBC ta zanta da wasu domin jin haƙiƙanin halin da suke ciki bayan aikin shekara 35, da kuma abin da suke nema.

Adetarami ya ce tun lokacin da yake aiki ne ya samu rauni a sanadiyyar haɗarin da ya yi, shi ne har ya yi ritaya, har ma zuwa yanzu yana kwance yana jinya.

"Na samu rauni a wuya da ƙashin baya ne a haɗarin, wanda hakan ya sa tun lokacin nake ta yawon neman magani har zuwa yanzu," in ji shi.

Ya ce ya yi haɗarin ne a shekarar 2017 lokacin da zai je wani aiki a Abuja, amma a cewar sa duk da cewa aiki ne ya kai shi Abuja, babu ko sisi da ya samu na taimako daga wajen ƴansanda.

A haka ya ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2021 da ya yi ritaya daga aiki, inda ya ce lamarin ya ƙara ƙamari har ya tare a asibiti.

"Ba na iya miƙewa ballanta tafiya. Ba na iya yin komai domin a kwance kawai nake. Ina da yara huɗu, dole ta sa biyu suka daina zuwa makaranta, gidan da na gada ma na sayar saboda kuɗin jinya."

A cewarsa, bayan ritaya ma sai da aka yi shekara biyu kafin aka ba shi kuɗin giratuti, wanda ya ce miliyan biyu ne da ƴan-kai, sannan ana ba shi fanshon naira 47,000 duk wata.

'Bayan aikin shekara 35, har yanzu bashi nake ci domin cin abinci' - DSP Iliyasu Aliyu

Wasu tsofaffin ƴan'sanda

Asalin hoton, ILIYASU ALIYU

Bayanan hoto, Wasu tsofaffin ƴan'sanda

Tsohon ɗansanda mai muƙamin DSP, Iliyasu Aliyu wanda ya yi ritaya a shekarar 2019 bayan ya yi shekara 35 yana aiki ya ce, "lokacin da na yi ritaya, sai da na yi wata takwas ba tare da fansho ba. Da bashi na riƙa gudanar da rayuwa."

Ya ce har yanzu a gidan aro yake zama saboda ya kasa biyan kuɗin haya ballantana sayen gida.

A cewarsa, bayan wata takwas ɗin ne kuma sai aka fara biysan fanshon naira 35,000 a wata.

"Sun kira ni ne suka ce min kuɗin da na tara naira miliyan 5 ne, sai suka ce za a ba ni kuɗin giratuti naira miliyan biyu, sai a riƙa biyana fanshon wata-wata da sauran kuɗin."

Ya zargi hukumar fanshon ƴansanda da amfani da kuɗinsu wajen kasuwanci, kuma suna cinye ribar.

'Me zan yi da naira 32,000'

Tsohon ɗansanda ASP Jonah
Bayanan hoto, Tsohon ɗansanda Jonah

"Ban samu damar yin yin aure da wuri ba, hakan ya sa har yanzu nake da ƙananan yara da suke zuwa firamare da sakandare, ta yaya zan iya ciyar da su?"

Abin da wani tsohon ɗansanda mai suna DSP Jonah Inyayang ya bayyana ke nan. "35,000 ba za ta sayi rabin buhun shinkafa ba, kafin a fara maganar kuɗin makarantar yara da sauran buƙatu."

Shi ma SP Umar Ibrahim mai ritaya da ke zaune a jihar Nasarawa ya ce burinsu shi ne a ba su kuɗaɗensu da aka ce ana ajiye musu, a bari su juya kayansu.

Ita ma DSP Roselyn Okoronkwo da ke zaune a jihar Bauchi ta ce ta fara aiki ne tana da shekara 19 a 1988, sannan ta yi ritaya a 2023 bayan shekara 35, amma ta ce fanshon da take karɓa ba ya biya mata buƙatunta na gida.

Tsarin fanshon Najeriya

Tsofaffin ƴansandan Najeriya da tambarin hukumar fansho
Bayanan hoto, Tsofaffin ƴansandan Najeriya da tambarin hukumar fansho
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafin shekarar 2004, Najeriya ta kasance tana amfani da tsarin Defined Benefit Scheme wato DBS wajen sallamar ma'aikatanta bayan sun yi ritaya.

A tsarin, gwamnati na biyan masu ritaya kashi 300 na jimillar albashinsu a matsayin giratuti, sai kuma kashi 80 na albashinsu na ƙarshe za a ci gaba da ba su duk wata a matsayin fansho, amma aka dakatar saboda gwamnati ta ce babu kuɗi.

Sai gwamnati ta ƙirƙiro tsarin fansho na karo-karo wato Contributory Pension Scheme, inda ake cire aƙalla kashi 10 na albashin ma'aikaci, sai kuma gwamnati ta saka kashi 8 sai a ba masu kula da kuɗin suna juyawa.

Wannan tsarin ne tsofaffin ƴansandan suke ƙorafi a kai, inda suke kira da a cire su, sannan a ba su kuɗaɗen da suka tara.

Barista Philip Oyanaa lauya ne a Najeriya, ya ce tsohon ma'aikaci zai iya karbar wani kaso na kuɗin, amma fita a tsarin baki ɗaya ba zai yiwu ba.

Ya ce wanda ya yi ritaya zai iya karɓar kashi 25 na kuɗin da aka tara masa, sai a riƙa biyansa wata-wata da sauran a matsayin fansho.

Abin da rundunar ƴansanda ta ce

Tsohon ɗansandan Najeriya da shugaban ƴansandan ƙasar Kayode Egbetokun
Bayanan hoto, Tsohon ɗansandan Najeriya da shugaban ƴansandan ƙasar Kayode Egbetokun

Babban Sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetukon ya ce suna ƙoƙarin ganin tsofaffin ƴansanda suna samun walwala da jin daɗi bayan kammala aiki.

Ya ce lallai wasu tsofaffin ƴansandan ƙasar suna shiga ƙuncin rayuwa bayan ritaya, wanda hakan a cewarsa ke jefa fargaba a zukatan masu aikin a yanzu.

Shugaban ƴansandan ya ce kuɗin da ake ba ƴan fansho ya yi kaɗan idan aka lura da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki a Najeriya, sannan ya ce suna ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin inganta rayuwar tsofaffin ƴansandan ƙasar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarni a samar da yanayin da tsofaffin ma'aikata za su riƙa samun rangwame a asibitocin ƙasar, sannan ya buƙaci a tabbatar da ƙari a fansho da giratuti.

A watan jiya ne wani tsohon ɗansanda mai muƙamin DSP ya yi bidiyo, inda a ciki ya ce bayan aiki na shekara 35, naira miliyan biyu ya samu a matsayin giratuti, sannan sai bayan kusan shekara biyu ya samu kuɗin.

Tuni dai shugaban ƴansandan ya buƙaci a gudanar da bincike kan abin da ya faɗa.

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumar fanshon ƴansanda amma abin ya ci tura, inda daga bisani ta ce a nemi kakakin rundunar ne domin jin bayani.

Tare da gudumawar Chukwunaeme Obiejesi