Man City za ta fafata da Juventus, Chelsea da Flamengo

Asalin hoton, Getty Images
Gwarzuwar da ke riƙe da kofin Fifa Club World Cup, Manchester City za ta fafata a matakin rukuni da Juventus, yayin da Chelsea za ta yi nata wasa da Flamengo ta Brazil.
Pep Guardiola wanda ya yi nasarar doke Fluminense ta Brazil ya ci kofin a 2023 karon farko a tarihi, zai fara wasa ne da Wydad ta Morocco da kuma Al Ain ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a rukunin G.
Chelsea wadda ta lashe gasar a 2021, tana cikin rukuni ɗaya da ƙungiyar Mexico Leon da ƙungiyar Esperance Sportive de Tusisie a rukunin D.
Za a yi fafatawar wasannin Fifa Club World Cup da za a fadada zuwa kungiyoyi 32 a Amurka tsakanin 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli a shekara mai zuwa.
An fitar da jadawalin ne a wani taro da aka yi a wurare biyu a birnin Miami kuma an kwashe sama mintina 90 ana gudanar da shi, yayin da aka nuna sabon gasar da za a ci gaba da amfani da shi.
An haska wani sakon video daga sabon shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, wadda 'yarsa ta gudanar da raba jadawalin a karon farko.
Inter Miami za ta fafata da ƙungiyar Al Ahly ta Masar a filin wasa na Hard Rock a wasan farko.
A gefe ɗaya kuma PSG za ta kasance da Atletico Madrid a rukunin B, yayin da Bayern Munich za ta fafata da Benfica.
Kungiyoyin za su fafata da juna a wasa ɗaya kacal, yayi da biyun farko za su tsallaja rukunin sili ɗaya kwale.
Jadawalin Fifa Club World Cup na 2025
Rukunin A: Palmeiras, FC Porto, Al Ahly, Inter Miami
Rukunin B: Paris St-Germain, Atletico Madrid, Botafogo, Seattle Sounders
Rukunin C: Bayern Munich, Auckland City, Boca Juniors, Benfica
Rukunin D: Flamengo, Esperance Sportive de Tunisie, Chelsea, Club Leon
Rukunin E: River Plate, Urawa Red Diamonds, Monterrey, Inter Milan
Rukunin F: Fluminense, Borussia Dortmund, Ulsan, Mamelodi Sundowns
Rukunin G: Manchester City, Wydad, Al Ain, Juventus
Rukunin H: Real Madrid, Al Hilal, Pachuca, Salzburg











