Yadda Tchiroma Bakary ya ɓulla a Gambia bayan ɓatan-dabo

Issa Tchiroma Bakary
Bayanan hoto, Issa Tchiroma Bakary
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Gambia ta tabbatar da cewa Issa Tchiroma Bakary, jagoran ƴan hamayya a ƙasar Kamaru, wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Oktoba ya isa ƙasar domin samun mafaka da tsaro.

A wata sanarwa da ma'aikatar watsa labaran ƙasar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce Bakary ya isa ƙasar ne a ranar 7 ga watan Nuwamba.

Wannan ne ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan ina tsohon jami'in gwamnatin ƙasar ta Kamaru yake.

"Ya iso ƙasarmu inda zai zauna na wani ɗan lokaci saboda tabbatar da tsaronsa a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan samar da matsaya mai kyau cikin diflomasiyya kan abubuwan da suka faru bayan zaɓen Kamaru," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sai dai ƙasar ta ce ba za ta bari a yi amfani da ƙasarsu "domin yin katsalandan ga wata ƙasar ba."

Hukumar zaɓen Kamaru ta sanar da shugaban ƙasar, Paul Biya mai shekara 92 a matsayin wanda ya lashe babban zaɓe, inda ta ce ya samu kashi 54 na ƙuri'un da aka kaɗa, duk da cewa akwai zarge-zargen maguɗi da suka biyo bayan zaɓen.

Sai dai Bakary wanda a baya ya kasance jami'in gwamnatin Biya, ya ce shi fa ba za ta saɓu ba, inda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan da ya gabata ne ɗansiyasar mai shekara 76 ya ce sojojin da suke tare da shi sun ɗauke shi daga garin Garoua da ke arewacin Kamaru zuwa wani wajen domin tabbatar da tsaronsa.

Tun bayan lokaci ne ba a sake jin ɗuriyarsa ba, inda aka fara tambayar ina yake ne duk da cewa wasu sun fara cewa ya wasu ƙasashen da suke maƙwabtaka da Kamarun.

Sai dai duk da haka, babbar jam'iyyar hamayya ta UDP ta soki abin da ta kira ɓoye-ɓoye da gwamnatin ta yi wajen ba Bakary mafaka a ƙasar.

Ta kuma buƙaci hukumomin ƙasar su fayyace yanayin makafar da za a ba Bakary, da yanayin lokacin da zai ɗauka a ƙasar da sauran bayanai.

Amma ta ce tana goyon bayan jagoran hamayyar na Kamaru, inda ta ƙara da cewa tana sane da irin halin da ƴan hamayya suke shiga da fafutikar da suke yi.

Gwamnatin Gambia ta ce tana tattaunawa da sauran ƙasashe maƙwabta, ciki har da Najeriya domin samar da maslaha.

Har yanzu babu tabbas yaya gwamnatin za ta kalli matakin, musamman ganin yadda ministan harkokin cikin gida na ƙasar Paul Atanga Nji ya dage wajen nanata cewa dole Bakary ya fuskanci hukunci, sannan ya ce suna nemansa ruwa a jallo bisa shirya zanga-zanga.

Gwamnatin ta ce zanga-zangar ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 16, amma alƙaluman wasu hukumomin na nuna cewa lamarin ya fi haka ƙamari.

Zaɓin da ya rage wa Bakary

Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa Majalisar Tsarin Mulkin Kamaru ta ɗauki kwana 15 kafin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, shi ne sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen zaɓen - hakan na nufin bayan sanar da sakamakon babu wani abu da mai ƙorafi zai iya yi.

Kan hakan ne BBC ta tuntuɓi masana kimiyyar siyasa guda biyu da suka haɗa da Farfesa Ibrahim Umara, masanin kimiyar siyasa a jami'ar Maiduguri da Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja da ke Najeriya.

"Idan ya ce bai yarda ba ma to ai ba za ka daki mutum ka hana shi kuka ba amma kuma ya san cewa ba shi da ƴansanda kuma ba shi da soja. Duk da cewa Bakary da magoya bayansa sun ci buri a wannan karo to amma dole ne su yi haƙuri su tara a gaba."

"Abin da ya sa ya kamata su yi hakuri shi ne Afirka ba za ta jure wani sabon rikicin a Kamaru ba, wadda kusan da ma ita kaɗai ce a yankin tafkin Tchadi ke da ɗan zaman lafiya. Jamhuriyar tsakiyar Afirka ba sa zaman lafiya. Haka ma Congo da ƙasar Tchadi da ma Najeriya," in ji Farfesa Ibrahim Umara.

Shi ma Farfesa Abubakar Kari ya ce a halin da ake ciki zaɓin da ya rage wa Issa Tchiroma shi ne ya ɗauki ƙaddara.

"Mafi sauƙin abin da zai yi shi ne ya rungumi ƙaddara amma abin kamar da wuya. Ya yarda a kan cewa an kayar da shi ya jira har zuwa wani lokaci to amma abubuwa da dama sun sauya a Kamarun da ba zai bar hakan ta faru ba," in ji Farfesa Kari.

Farfesa Kari ya kuma ƙara da cewa bisa la'akari da irin karɓuwar da Issa Tchiroma Bakary ya yi a wurin ƴan ƙasar ka iya sa dole ko dai gwamnatin Paul Biya ko kuma ƙasashen duniya su zauna da Bakary a ƙulla wata yarjejeniya.