Yadda manoman albasa suka tafka mummunar asara a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 3

Babbar ƙungiyar manoman albasa ta Najeriya ta ƙoƙa game da rashin samun albarkar noma a bana.

An dangata hakan da rashin amfani da irin albasan mai inganci a lokacin shuka.

Iri mara kyau dai ya daɗe yana yi wa gonaki ko kuma amfanin gona illa, musamman a ƙasashe irin Najeriya.

"Manoma sun shiga halin kakani-kayi a bana da tashin hankali sakamakon sayen irin albasa mara inganci," in ji Ibrahim Danjuma ɗaya daga cikin manoman albasa.

Ya ce Sokoto da Kebbi ne tushen albasa, inda ake fita da ita daga jihohin zuwa Burkina Faso da Mali da Ivory Coast da kuma Ghana.

"Iri ne mara kyau kuma ba shi da inganci sai ganye babu albasa," in ji Ibrahim.

Ya ƙara idan ka je kasuwanni a Sokoto, za ka samu manoma suna ta ƙoƙawa sakamakon asarar da aka yi.

Ya ce a shekaru uku da suka wuce sun kawo wani iri da suka saya da Faransa da Holland wanda ya kasance mai inganci, inda ya ce bayan karewarsa ne aka kawo wani iri mara inganci.

'Za a iya shiga matsalar albasa nan da wata biyu'

Manomin albasan Ibarahim Danjuma ya yi kira ga gwamnatoci da su tashi haikan wajen magance matsalar albasa da ta tinkaro al'umma.

Ya ce kamata ya yi gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya yi hoɓɓasa wajen magance matsalar.

"Mutane za su sha mamaki kan rikicin albasa da za a shiga nan da wata ɗaya zuwa uku," in ji Danjuma.

Ya ce buhun albasa ya kai naira 200,000 a yanzu, wanda a baya bai fi 15,000 zuwa 20,000 ba.

Ya ce babban tashin hankali shi ne mutane na wasa da harkar noma, inda ya ce babu abin da ya kai yunwa matsala a duniya.

Ya kuma ce a yanzu masu mulki da ma'aikata sun ɗauki noma ba da muhimmanci ba.

"Yanzu an yi asarar albasa da ta kai sama da naira biliyan 150. Kowace rana ana cinikin albasa da ya fi na naira biliyan biyu a Sokoto da Kebbi," in ji shi.

'Rashin sani ne ya janyo mana wannan asara'

Shugaban ƙungiyar manoma da masu sarrafa albasa a Najeriya, Aliyu Maitasamu Isa, ya shaida wa BBC cewa sun haɗu da matsalar rashin samun ingantaccen iri da manoma za su yi amfani da shi.

Lamarin ne ya kai suka buƙaci gwamnati ta kawo musu agaji ta hanyar neman kamfanoni daga waje domin samun irin.

"Ganin haka bai yiwu ba, sai aka samu wasu mutane suka shigo mana da mugun iri daga Aljeriya wanda manoman mu suka yi amfani da shi.

"Da mun san haka wannan iri zai janyo mana asara da ba mu amince da shigo da shi ba," in ji Aliyu.

Ya ce sun tafka asarar albasa na tan 200,000 kwatankwacin naira biliyan 150.

"Wannan noman rani dai mun rasa shi, amma gwamnati za ta iya taimakon mu wajen fara shirin noman damina," in ji manomin.