Kalaman da Ganduje ya yi kan Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf

Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Alhamis ne tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da sauran jiga-jigan jam'iyyar na Kano suka gudanar da wani taro irinsa a karon farko a tsawon lokaci.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibril da sauran shugabannin jam'iyya na ƙananan hukumomi.

Abdullahi Ganduje ya ce sun shirya taron ne domin ƙara ɗinke jam'iyyar da yin kandagarki dangane da rigingimu ka iya taso mata a nan gaba.

Sai dai kuma majiyoyi na cewa an shirya taron ne da manufar yin kandagarki dangane da raɗe-raɗin da ake yi na komawar tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar ta APC.

To amma Abdullahi Gandije ya ce "mu ma mun ji wannan jita-jita ɗin kuma ba mu ɗauke muhimmiya ba. Mu a fahimtarmu da ƙuir'ar liman da ta ɓarawo a tsarin dimokraɗiyya duk ɗaya ne."

Abin da Ganduje ya ce kan Kwankwaso

Toshon gwamnan na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shaida wa BBC cewa shi ba ya tunanin Rabi'u Musa Kwankwaso zai koma APC saboda wasu kalaman da Kwankwason ya yi a baya.

"Su yanzu abin nasu ya zamo wato ɗaukar ni amma ka da ka taɓa ni. Ya zama kamar an yi amai an lashe. Idan ka kula ya zazzagi Bola Tinubu lokacin da yake neman shugaban ƙasa. Sun ce Bola Tinubu kawai gina jihar Legas yake yi. Akwai lokacin da suka ce ma wai mahaukaci ne kawai zai shiga jam'iyyar APC."

"Su suka ce sai mahaukaci ne zai shigo jam'iyyar APC. To ka ga yanzu tunda sun zama mahaukata suna son su shigo jam'iyyar sai mu hana su? Sai dai mu kira su da ƴan APC masu amai su lashe. Saboda haka muna yi musu marhaban su shigo jam'iyyar APC." In ji Ganduje.

Ko za ku haɗe da Kwankwaso da Shekarau?

Da aka tambayi tsohon shugaban jam'iyyar ta APC, sai ya ce:

"Wannan ra'ayi ne mai kyau babu shakka domin idan za a zo a haɗa kai to ai ka ga gwamnati mai ci na da rawar da za ta taka. Domin idan aka haɗamu ai ka ga abin da ake so shi ne gogewarmu.

"Kuma tunda dukkan mu mun yi mulki na shekara 8 duk da cewa biyu daga cikinmu mun yi mulkin shekara 8 a miƙe. Ɗaya daga cikinmu kuma da ya shekara huɗu sai ya kasa zarcewa.....sai da ya tafi bulaguro sannan ya dawo ya cika wasu shekarun huɗu....duk da cewa tare muka dawo...babu shakka.Muka tafi bulaguro muka dawo bayan mun fadi da farko."

"Saboda haka ka ga muna da ilimin yadda ake gudanar da gwamnati domin mun yi an gani. Babu shakka mu ne muka fi cancanta mu bai wa gwamnati mai ci shawara kan wasu abubuwa. Haka ake yi a wasu jihohin amma mu saboda baƙar aƙida ba haka ba ne.....Amma idan yanzu sun ga dacewar hakan to ni ai a shirye nake." In ji Abdullahi Ganduje.

Kalaman Ganduje kan Abba Kabir Yusuf

"Babu shakka idan gwamnati ta shuɗe akan bincike ta to su sababbin shugabannin ba su fahimci yadda aikin gwamnati ba.

Ni da na karɓi mulki na binciki wanda ya gabace ni? Ko lokacin da ƴan ba ni na'iya suka ce mu bincike su sai na ce to ai tare da ni aka yi gwamnati idan an yi daidai da hannunna kuma idan ba a yi daidai ba nan ma da hannuna. Ita gwamnati ba ta ƙarewa."

"Amma su yanzu kuma tun ba aje ko'ina ba suna ta bincike. To amma mai suka iya bincikowa ya zuwa yanzu? Ka duba irin kuɗin da suke samu. Kuɗin da suka samu a wata shida yanzu gwamnatina ba ta same su a tsawon shekaru 8 na mulkina ba.

"Mu yanzu abin da muke so shi ne su faɗi yawan kuɗin da suka samu sannan su faɗi nawa aka kashe."

"Shi ai rashin sanin yadda ake gudanar da gwamnati ne ya sa ya yi haka....ai shi awon igiya ne. Banbancina da shi a aikin gwamnati kamar banbancin masinja ne da famanet sakatare.

"Gwamnatin da na gada ta bar min bashin kuɗin ƴan fansho wadda har sai da EFCC ta yi bincike a kanta. Amma ka ga ni na sani amma ban yi bincike ba. To abin da shi gwamnan bai sani ba shi ne shi ma ai watarana zai bar ofis kuma dole ne ya bar bashi a wani fannin.

"Zai bar wani fannin babu kuɗi. Zai bar wani fannin ba a biya ƴan kwangila ba. Kuma haka aikin gwamnati ya gada. Ba wani abu ne sabo ba. Ba kuma laifi ba ne. Amma idan kai kamun igiya ne. Idan kai dama bundin-bundin ne ba ka san aikin gwamnati ba." In ji Abdullahi Ganduje.

Ko gwamnatin Abba na samun nasara?

Da aka tambaye shi ko bai gamsu da kamun ludayin gwamnatin Kano ta yanzu, sai Ganduje ya ce "ai ba ma su da ludayin ballantana ma a kama. Gwamnatin ƴan bandan-bandan ce. Gwamnatin masu kame-kame."

"To ita gwamnati tana da nasarori da rashin nasarori. To amma ita wannan gwamnatin ba ta da nasarori ne irin waɗanda ake kira cigaban mai haƙar rijiya saboda irin facaka da suke yi da irin yawan kuɗin da ake kashewa kan ayyukan da suke cewa suna yi.

Babu shakka idan an yi aiki misali kamar an gina gada ai cigaba ne to amma idan ka duba irin kuɗin da suke kashewa to da talakawa za su iya cewa ma ba sa son gadar saboda yawan kuɗin da aka kashe."

Tinubu bai yi min laifi ba - Ganduje

Ba haka ba ne. Ba shakka bayan na sauka na je duba lafiyata tunda na daɗe ban je ba. Amma idan za ka iya tunawa ai ni ne mutum na farko da ya fara taya sabon shugaban jam'iyyar APC murna a shafin jarida.

Shi shugabancin jam'iyya ai shiyya-shiyya ne. Su kuma sun ce ya kamata shugabancin ya koma shiyyarsu. To kuma haka aka yi. Ka ga ai shugaban ƙasa bai yi wa kowa laifi ba. Kuma ni ma ban ji haushi ba tunda na san mulki na Allah ne. Ya kan bayar ga wanda ya so a lokacin da ya so kuma ya karɓe lokacin da ya so.

Dangane kuma da dalilin da ya sa aka sauke shi daga kan shugabancin jam'iyyar, Abdullahi Umar Ganduje ya ce babban dalilin shi ne "kamar yadda na faɗa maka batun karɓa-karɓa shi ne dalili."

Waɗanda suka fice daga APC

Idan ka duba tsiraru ne suka fita daga APC kuma da su aka dama aka sha a lokacin Buhari. Yanzu kuma suka kasa yin hakuri.

Amma abin da za ka tambaya shi ne a lokacina ai akwai gwamnoni cancak da suka shigo APC. Amma akwai gwamnan APC da ta bar jam'iyyar.?

Da aka tambaye shi batun ƙoƙarinsu na mayar da Najeriya tafarkin mai jam'iyya ɗaya, sai tsohon shugaban jam'iyyar ya ce "to kenan ai idan har haka ne bai kamata ace don wasu na ficewa daga jam'iyyar abin ya dame mu ba. Ai wannan abin alfahari ne da farin ciki a wurinmu."

Kawo yanzu dai Rabi'u Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf ba su mayar da martani ba.

Amma da zarar sun mayar da martanin za mu kawo muku.