Hotunan yadda aka yi sallar Idi a faɗin duniya

Ana bai wa yara mata kyautuka a garin Lviv na Ukraine yayin da Rasha ke ci gaba da luguden wuta a kan ƙasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana bai wa yara mata da maza kyautuka bayan kammala sallar Idi a garin Lviv na Ukraine, yayin da Rasha ke ci gaba da luguden wuta a kan ƙasar
Lokacin karatu: Minti 3

Musulmai a faɗin duniya na bukukuwan Idin Ƙaramar Sallah ko kuma Eid al-Fitr a Larabce, wato ɗaya daga cikin biki mafiya girma a kalandar Musulunci.

Eid al-Fitr - wanda ke nufin "bikin kammala azumi" - akan yi shi ne bayan kammala azumin watan Ramadana duk shekara, wanda shi kuma rukuni ne cikin rukunnan Musulunci.

Dubun dubatar Musulami sanye da hirami suke yin sujjada a Masallacin Ka'aba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubun dubatar Musulami sanye da hirami suke yin sujjada a Masallacin Ka'aba
A birnin Moscow na Rasha, ana iya ganin Musulmai na shirin yin sallar Idi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A birnin Moscow na Rasha, ana iya ganin Musulmai na shirin yin sallar Idi
Ɗaruruwa ne suka fito yin sallar Idin a filin Idi na Tononoka da ke birnin Mombasa na ƙasar Kenya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ɗaruruwa ne suka fito yin sallar Idin a filin Idi na Tononoka da ke birnin Mombasa na ƙasar Kenya
An kuma gudanar da sallolin a cikin wani filin wasa da ke Port Sudan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kuma gudanar da sallolin a cikin wani filin wasa da ke Port Sudan
Ƙananan yara sun bi sawun manya a Masallacin Essalam da ke Rotterdam na ƙasar Netherlands

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙananan yara sun bi sawun manya a Masallacin Essalam da ke Rotterdam na ƙasar Netherlands
Falasɗinawa a unguwar Jabaliya da ke Zirin Gaza sun gudanar da sallolin nasu ne cikin ɓaraguzan wani masallaci sakamakon hare-haren Isra'ila a yaƙin da take yi da Hamas

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Falasɗinawa a unguwar Jabaliya da ke Zirin Gaza sun gudanar da sallolin nasu ne cikin ɓaraguzan wani masallaci sakamakon hare-haren Isra'ila a yaƙin da take yi da Hamas
Iyalai sun taru a Masallacin Ƙudus, wuri na uku mafi tsarki a Musulunci - bayan Makka da Madina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iyalai sun taru a Masallacin Ƙudus, wuri na uku mafi tsarki a Musulunci - bayan Makka da Madina
Wan yaro yana hamma yayin sallar Idi a wani filin wasa da ke ƙasar Ƙatar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wan yaro yana hamma yayin sallar Idi a wani filin wasa da ke ƙasar Ƙatar
Musulmai na yi wa juna barka da sallah a dandalin Martim Moniz da ke birnin Lisbon na Portugal

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Musulmai na yi wa juna barka da sallah a dandalin Martim Moniz da ke birnin Lisbon na Portugal
Mata ma sun fito sallar a Burgess Park da ke birnin Landan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata ma sun fito sallar a Burgess Park da ke birnin Landan
A dandalin Plebiscito ma da ke birnin Naples na Italiya, masallata sun fito

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A dandalin Plebiscito ma da ke birnin Naples na Italiya, masallata sun fito
Wasu mata na ɗaukar hoto bayan kammala sallar Idi a babban masallacin Hagia Sophia na birnin Istanbul ɗin Turkiyya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mata na ɗaukar hoto bayan kammala sallar Idi a babban masallacin Hagia Sophia na birnin Istanbul ɗin Turkiyya
'Yan gudun hijirar Afghanistan suna yin sallah a wani masallaci da ke wajen birnin Peshawar na Pakistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan gudun hijirar Afghanistan suna yin sallah a wani masallaci da ke wajen birnin Peshawar na Pakistan