Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tottenham ta je ta ci Ferencvaros a Europa League
Tottenham ta yi nasara a wasa na biyu a Europa League, bayan da ta yi amfani da matasan da suka je suka ci Ferencvaros 2-1 a Hungary ranar Alhamis.
Ange Postecoglou ya fara karawar da matasa huɗu da ya haɗa da mai shekara 17, Mikey Moore da mai 18, Lucas Bergvall da wani mai 18, Archie Gray da mai 19, Will Lankshear.
Moore yana da hannu a ƙwallon da Tottenham ta fara ci a minti na 23 da take leda ta hannun Pape Sarr.
Tun farko mai masaukin baƙi ta ci ƙwallo ta hannun Barnabas Varga , amma aka soke da cewar akwai satar gida.
Haka kuma Ferencvaros ta ci gaba da sa ƙwazo, domin ta farke ƙwallon, inda Kady Borges da kuma Cebrail Makreckis suka zubar da damar maki.
Daga baya ne Tottenham ta kara na biyu ta hannun Brennan Johnson, wanda ya ci na biyar kenan a karawa biyar a kakar nan.
Daf da za a tashi daga wasan ne mai masaukin baƙi ta farke ɗaya ta hannun Verga.
Da wannan sakamakon Tottenham tana da maki shida a wasa biyu, bayan da ta fara da doke Qarabag ta Azerbaijan a gasar ta zakarun Turai ta bana.