BBC ta gano yadda sojojin Amurka suka kashe dangi guda a Iraqi

Safa Younes yanzu shekararta 33 - ita kaɗai ce ta rage a cikin danginta
Bayanan hoto, Safa Younes yanzu shekararta 33 - ita kaɗai ce ta rage a cikin danginta
    • Marubuci, Lara El Gibaly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
  • Lokacin karatu: Minti 7

"A wannan gidan ne aka kashe min duka dangina," in ji Safa Younes.

Daga zuwa gidan, wanda yake garin Haditha a ƙasar Iraqi, za ka ga gurabun harbe-harbe. A cikin uwarɗaka, an rufe gadon da aka kashe dangin nata da wata shimfiɗa mai faɗi.

A ɗakin ne ta yi yunƙurin ɓoye danginta biyar, mahaifiyarta da innarta lokacin da dakarun soji na musamman na Amurka suka kutsa gidansu, suka buɗe wuta, suka kashe kowa, inda ita kaɗai ta tsira da ranta a ranar 19 ga watan Nuwamban shekarar 2005. Haka kuma an harbe mahaifinta lokacin da ya buɗe ƙofar gidan.

Yanzu, kimanin shekara 20 bayan waƙi'ar, sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC ya bankaɗo hujjojin da suka nuna sojojin ruwan na Amurka guda biyu suna da hannu a kisan dangin Safa, amma ba su fuskanci hukunci ba.

Hujjojin, waɗanda suka ƙunshi bayanai da nazarin sakamakon binciken ƙwaƙwaf na daƙin gwaje-gwaje sun sanya alamar tambaya kan binciken da Amurka ta gudanar.

Kashe dangin Safa na cikin kashe-kashen da ake kira kisan kiyashin Haditha, inda sojojin Amurka na musamman suka kashe ƴan Iraqi fararen hula guda 24, ciki har da mata huɗu da ƙananan yara shida.

Sun kutsa gidaje uku, inda suka kashe kusan kowa a gidajen, da wani direba da ɗalibai huɗu a mota a hanyarsu ta tafiya makaranta.

Gidan da aka kashe dangin Safa a Haditha a 2005
Bayanan hoto, Gidan da aka kashe dangin Safa a Haditha a 2005

Sojojin sun ce sun mayar da martani ne bayan wani bam ya kashe musu soja ɗaya, sannan biyu suka jikkata.

Amma Safa, wadda a lokacin take da shekara 13, ta bayyana wa BBC cewa, "ba a taɓa zargin mu da wani laifi ba. Ba mu da makami a gidanmu."

Ta tsira ne bayan ta yi mutuwar ƙarya ta kwanta a cikin gawarwakin ƴan’uwanta, ciki har da mai shekara uku a lokacin. "Ni kaɗai na tsira a danginmu a ranar," in ji ta.

An tuhumi sojojin Amirka guda huɗu da laifin kisa, inda duk da sun bayar da hujjoji mabambanta, amma a ƙarshe masu gabatar da ƙara a Amurka suka jingine ƙarar kan sojoji uku, sai suka bar jagoran sojojin, Sajan Mano Frank Wuterich domin ya fuskanci tuhumar a 2012.

A wannan hoton, wanda aka tsakura daga faifan da ba a fitar ba, Humberto Mendoza a tsugune yana kwatanta abin a ya faru

Asalin hoton, Michael Epstein

Bayanan hoto, A wannan hoton, wanda aka tsakura daga wani faifan bidiyon da ba a fitar ba, Humberto Mendoza a tsugune ya kwatanta abin a ya faru
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wani bidiyo da aka naɗa da ba a taɓa fitarwa ba, ƙaramin soja a cikinsu mai igiya ɗaya, Humberto Mendoza ya amsa tambayoyi, sannan ya kwatanta abin da ya faru a gidan su Safa.

Mendoza - wanda a lokacin ba shi da igiya, ya bayyana cewa shi ne ya kashe mahaifin Safa lokacin da ya buɗe ƙofa.

"Ka ga hannunsa a lokacin?," kamar yadda wani lauya ya tambaye shi, sai Mendoza ya ce, "na gani, sannan ya tabbatar da cewa mahaifin Safa bai fito da makami ba.

"Amma duk da haka sai da ka harbe shi," in ji lauyan, sai Mendoza ya amsa cewa, "ƙwarai yallaɓai."

A jawabinsa, da farko Mendoza ya ce da farko bayan sun shiga gidan, ya buɗe ƙofar uwarɗaka, amma da ya ga ƙananan yara ne, sai ya kulle ya juya.

Amma wata murya da aka naɗa daga zaman sauraron shari'ar Wuterich, Mendoza ya bayar da bayani daban. Ya ce ya yi tafiyar kusan mil 2.4 zuwa uwarɗaka.

Wannan ya taimaka kamar yadda masanin binciken ƙwaƙwaf Michael Maloney ya bayyana. Sashen binciken manyan laifuka na sojan ruwan Amurka sun tura shi Iraq domin bincike a 2006.

Safa a lokacin uwarɗakansu inda aka kashe danginta tana kwatanta yadda ta ɓoye ta yi lamɓon mutuwa
Bayanan hoto, Safa a cikin ɗakin da aka kashe danginta tana kwatanta yadda ta tsira

Ta hanyar amfani da hotuna da dakarun sojin ruwan suka ɗauka a lokacin da suka yi kisa, ya ce sojojin ruwan guda biyu sun shiga ɗakin, sun harbe wata mata da ƙananan yara.

Da muka bayyana masa sautin muryar Mendoza da yake cewa ya shiga ɗakin, sai Maloney ya ce, "wannan abin ban mamaki ne, ban taɓa jin wannan bayanin ba kafin yau."

"Idan ka tambaye ni: 'shin wannan amsa laifi ne ko mene ne?' zan iya cewa: 'Mendoza ya amince da aikata dukkn laifukan, harbi ne kawai bai tabbatar ba."

Safa ta gabatar da bayani a wani faifan bidiyo ga sojojin da suke bincike a 2006, amma ba a haska bidiyon a kotu ba. A cikin bidiyon ne ta bayyana yadda sojojin ruwan suka kutsa uwarɗaka, suka wurga ƙaramin bom, amma bai fashe ba, sai wani mutumi ya shiga ɗakin, ya buɗe wuta.

Mendoza ne kaɗai sojan ruwan da ya tabbatar da cewa ya buɗe wuta.

An naɗi bidiyon Safa tana bayyana abin da ya faru ne a lokacin da take da shekara 14

Asalin hoton, US Marine Corps

Bayanan hoto, An naɗi bidiyon Safa tana bayyana abin da ya faru ne a lokacin da take da shekara 14

Wani sojan musamman mai suna Stephen Tatum bai musanta harbin ba, inda ya ce ya bi jagoransu cikin uwarɗaka, amma ya yi ikirarin cewa bai san akwai ƙananan yara da mata ba saboda ba a ganin cikin ɗakin sosai a lokacin.

Amma a wasu wasiƙu da ya rubuta da BBC ta gani, bayanai daban ya bayyana da abin da ya faɗa a baya.

"Na tarar da ƙananan yara a cikin ɗakin a tsugune, amma na manta adadinsu, amma dai suna da yawa. An horar da ni in yi harbi biyu a ƙirji, biyu a kai, kuma da horon na yi amfani," in ji Tatum a jawabin da ya yi wa sashen binciken manyan laifuka na rundunar sojin Amurka a 2006.

Wata ɗaya bayan gabatar da jawabin, sai ya ce ya, "ya gane mutanen da suke ɗakin, akwai wata mata da ƙananan yara kafin ya harbe su."

Sannan kuma bayan mako ɗaya sa ya ce, "a nan ne na ga ƙaramin yaron da na harbe. Na harbe shi duk da cewa na san ƙaramin yaro ne," in ji shi, inda ya ƙara da cewa a lokacin yaron yana sanye da riga fara, yana tsaye a kan gado sanye da gajeran wando.

Lauyan Tatum ya ce an tursasa wane yake karewa ne wjen bayar da jawabi. A watan Maris na 2008 an jingine ƙarar da ake yi wa Tatum.

Amma masanin binciken ƙwaƙwaf Michael Maloney ya ce bayanan Mendoza da Tatum sun bayyana cewa su ne sojoji biyu da suka harbe dangin Safa. Ya yi amannar cewa Mendoza ne ya shiga uwarɗaka da farko, sai Tatum ya bi shi.

Mun gabatar da zarge-zargen ga Mendoza da Tatum. Mendoza bai ce komai ba, amma a baya ya tabbatar da harbe mahaifin Safa, amma ya ce umarni aka ba shi. Ba a taɓa tuhumarsa da aikata laifi ba.

Lauyan Tatum ya ce wanda yake karewa ba ya so yana magana a game da Haditha, amma bai janye jawabinsa ba na cewa yana cikin wɗanda suka harbe dangin Safa.

Jagoran sojojin Sajan Manjo Frank Wuterich ne kaɗai ne ya fuskanci tuhuma, amma daga bisani ana janye tuhumar

Asalin hoton, Michael Epstein

Bayanan hoto, Jagoran sojojin Sajan Manjo Frank Wuterich ne kaɗai ne ya fuskanci tuhuma, amma daga bisani aka janye tuhumar

Maloney ya shaida wa BBC cewa masu gabatar da ƙara sun so a ce, "Wuterich ne asalin wanda ya yi harbin," amma kafin Meloney ya gabatar da jawbinsa, an janye ƙarar baki ɗaya.

Wuterich ya yi iƙirarin cewa ya manta abin da ya faru a gidan su Safa, amma ya amince da laifi ɗaya na wasa da aiki, tuhumar da ba ta da alaƙa ta kai-tsaye da binciken kashe-kashen.

Lauyan soji na Wuterich, Haytham Faraj, wanda shi ma tsohon sojan ruwa ne ya ce hukuncin ba wani abun a-zo-a-gani ba ne.

Babban lauyan Wuterich, Neal Puckett ya ce an shirya binciken ne domin ɓata sunan wanda yake karewa ne.

Haytham Faraj ya yi amannar cewa an yi kura-kurai a wajen gabatar da binciken.

"Gwamnati ta biya mutane su je su yi ƙarya, kuma biyan shi ne ba su kariya, wanda hakan ya lalata bincike da shari'ar," in ji shi a zantawarsa da BBC.

"Shari'ar Haditha ba a yi ta ba domin jin ta bakin waɗanda aka zalunta ba," in ji shi.

Har yanzu Safa na rayuwa ne a Haditha kuma yanzu tana da yara uku - mace ɗaya da maza biyu
Bayanan hoto, Har yanzu Safa na rayuwa ne a Haditha kuma yanzu tana da yara uku - mace ɗaya da maza biyu

Rundunar sojin ruwa na Amurka ta bayyana mana cewa a shirye take ta ci gaba da tabbatar da adalci, kamar yadda dokokin aikin soji suka tanada.

Sai da ta ce ba za ta sake dawo da binciken ba, sai dai idan har an samu wasu hujjoji manya da a baya ba a nazarce su ba.

Babban mai gabatar da ƙara bai ce komai ba game da tambayayoyin BBC ta miƙa masa.

Safa, wadda yanzu take da shekara 33, kuma take rayuwa a Haditha da yaranta uku - mace ɗaya da maza biyu. Ta ce ta kasa fahimtar yadda za a ce babu wani soja da aka hukunta kan kashe danginta.

Da muka nuna mata bidiyon Mendoza, sai ta ce, "kamata ya yi a ce yana ɗaure a gidan yari tun lokacin da abin ya faru."

"Ji nake kamar a bara abin ya faru, har yanzu abin da ya faru na raina," in ji ta.

"Ina son waɗanda suka kashe dangina su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada. Kusan shekara 20 ke nan, amma babu wanda ya fuskanci hukunci. Wannan ma babban laifin ne."

Ƙarin rahoto daga Namak Khoshnaw da Michael Epstein