Man City da Real Madrid na rububin Szoboszlai, Mainoo na son komawa Napoli

Dominik Szoboszlai

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City da Real Madrid duk suna zawarcin ɗan wasan Liverpool da Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekara 25. (AS)

Ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a shirye ya ke ya koma Napoli a watan Janairu amma ƙungiyar ta Old Trafford ba za ta bar shi ya tafi kan yarjejeniyar dindindin ba. (Teamtalk), waje

Ɗan wasan Real Madrid ɗan ƙasar Brazil Vinicius Jr, mai shekara 25, yana son a biya shi albashi daidai da na ɗan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 26, kuma ana ci gaba da takun-saƙa tsakaninsa da kulob ɗin wanda hakan zai iya sa shi barin filin wasan Bernabeu. (Sport)

Chelsea ta tuntubi Como game da yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Argentina Nicolas Paz mai shekaru 21. (Caught Offside).

Liverpool ta biya shirya biyan Inter Milan fam miliyan 88 kan ɗan wasan bayan Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 26. (Mundo Deportivo)

Ɗan wasan bayan Liverpool da Scotland Andy Robertson, mai shekara 31, zai bar Anfield idan kwantiraginsa ya ƙare a bazara mai zuwa kuma tuni ya fara tattaunawa da Celtic. (Fichajes).

Wolfsburg na nazari kan ɗaukar ɗan wasan West Ham Niclas Fullkrug a watan Janairu, yayin da ita ma Augsburg ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan na Jamus mai shekara 32 wanda aka ba shi izinin barin Hammers. (Florian Plettenberg)

Bayern Munich ba ta da sha'awar yanke zaman aron ɗan wasan gaban Senegal Nicolas Jackson mai shekara 24 daga Chelsea amma da wuya ƙungiyar ta Bundesliga ta saye shi a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Bild)

Kocin Newcastle Eddie Howe yana da cikakken goyon bayan mamallakan kulob ɗin da kuma sabon shugaban gudanarwa David Hopkinson duk da rashin fara kakar wasan bana da ƙafar dama. (The I)

Antonio Conte ba zai yi murabus a matsayin kocin Napoli ba amma zai gana da mai ƙungiyar Aurelio de Laurentiis nan da ƴan kwanaki masu zuwa domin nemo mafita kan matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta a kakar wasa ta bana. (Il Mattino)