Liverpool na shawara kan Greennwood, Man City za ta rabu da Stones

Mason Greenwood

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool na tunanin dauko tsohon dan gaban Manchester United Mason Greenwood. Dan wasan na Ingila mai shekara 24, ya yi bajinta a Marseille a kakar nan. (Fichajes )

Bournemouth na son karbo aron dan wasan gaba na Arsenal Ethan Nwaneri, mai shekara 18, amma kuma dan wasan na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 ya fi son ya ci gaba da zama a Emirate har zuwa karshen kaka duk da cewa ba a sa shi sosai a wasa. (Independent)

Kociyan Crystal Palace Oliver Glasner ya ce zai tattauna sosai da shugabannin kungiyar a kan sabon kwantiragi a makonnin da ke tafe kafin ya yanke shawara ta karshe. (Mirror)

Dan bayan Palace Marc Guehi na daukar hankali a wannan watan inda ake ganin Liverpool za ta iya ware har fam miliyan 20 domin sayen dan wasan na Ingila mai shekara 25. (Mirror)

Dan bayan Liverpool Joe Gomez, dan Ingila mai shekara 28, da kuma dan bayan Nottingham Forest Murillo, na Brazil mai shekara 23, su ne zabin da ke gaban AC Milan a kokarin da take yi na karfafa bayanta. (Calciomercato)

Dan bayan Manchester City John Stones na cikin shekarar karshe ta kwantiraginsa da kungiyar kuma Pep Guardiola na nuna shakku kan ci gaba da zaman dan bayan na Ingila mai shekara 31 a kungiyar. (The Times)

Tsohon dan gaban Manchester City da Liverpool, Mario Balotelli mai shekara 35, na shirin shiga kungiyarsa ta 14, inda zai tafi kungiyar Al Ittifaq wadda ke rukuni na biyu a Hadaddiyar Daular Larabawa. (Goal)

Ana danganta mai tsaron ragar Faransa Mike Maignan, mai shekara 30, da tafiya Chelsea amma kuma yana dab da kulla yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa a AC Milan. (Sky Sports Italia daga Football Italia)

Dan bayan Bayern Munich da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 27, ya amince da sabon kwantiragi, da baka amma kuma sauran batutuwan da ba a warware ba sun hada da batun damar sayar da shi ga wata kungiyar a cikin kwantiragin, idan ana sonshi a wani wajen (Fabrizio Romano)

Liverpool na tunanin dauko tsohon dan gaban Manchester United Mason Greenwood. Dan wasan na Ingila mai shekara 24, ya yi bajinta a Marseille a kakar nan. (Fichajes )

Tottenham na tattaunawa domin sayen matashin dan bayan Santos, Souza na Brazil mai shekara 19, bayan da farko kungiyarsa ta yi watsi da tayin fam miliyan 8 da Spurs din suka yi. (Standard)