Ya za a kwatanta ƙarfin sojin Indiya da Pakistan?

Lokacin karatu: Minti 4

Pakistan ta ce ta kakkaɓo jiragen Indiya marasa matuƙa 25 a faɗin biranen ƙasar bayan Indiya ta ƙaddamar da hare-hare ta sama kan Pakistan da wasu sassan Kashimir da Pakistan ke iko da su.

"Wani mummunan harin soji ne da Indiya ta ƙaddamar,'' a cewar Ahmed Sharif Chaudhry, kakakin sojin.

Indiya ta kuma ce ta wargaza "jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da" ta Pakistan ta girke.

Ga yadda za a iya kwatanta ƙarfin sojin ƙasashen biyu.

Jirage marasa matuƙa

Duka ƙasashen biyu na faɗaɗa yawan jirage marasa matuƙansu, ta hanyar saye wasu daga ƙetare tare da ƙera wasu a cikin gida, sai dai ana ganin Indiya ce kan gaba a yawan jiragen.

Indiya - wadda ke kan gaba a yawan al'umma a duniya za ta mallaki jirage marasa matuƙa kusan 5,000 nan da shekara biyu zuwa huɗu masu zuwa, kamar yadda Rahul Bedi, mai sharhi kan al'amuran tsaro ya shaida wa BBC.

A 2024, Indiya ta ƙulla yarjejeniya da ma'aikatar harkokin wajen Amurka, domin sayen jirage marasa matuƙa 31 masu ɗauke da makamai, samfurin MQ-9B.

Duk da cewa Pakistan ba ta da yawan jirage marasa matuƙa kamar Indiya, amma jiragenta marasa matuƙa na da ƙarfin leƙe asiri domin gano maƙiya da kuma ƙarfin ƙaddamar da hari.

Bababn inda jiragen Pakistan marasa matuƙa suka fi ƙwarewa shi ne iya kai hari. Alal Misali, Buraq - wani jirgi maras matuƙi da aka ƙera a ƙasar, ana amfani da shi a ƙasar wajen kakkaɓe ƴanta'adda tun 2015.

Haka kuma ƙasar na sayo jirage marasa matuƙa daga Turkiyya da China.

Kasafin kudin tsaro da yawan sojoji

Akwai sabon fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda suka yi a 1999.

Yayin da take da yawan sojoji miliyan 1.4, Indiya ta kasance ƙasa ta huɗu mafi ƙarfin soji a duniya, a cewar shafin Global Firepower Index (GFI), mai auna ƙarfin sojin ƙasashen duniya.

A nata ɓangare Pakistan na da yawan sojoji 654,000.

Haka kuma Indiya ta kashe ninki tara na abin da Pakistan ta kashe kan tsaro a 2024, a cewar cibiyar binciken zaman lafiya a duniya ta, Stockholm International Peace Research Institute (SIPRI).

A fannin kayan aikin soji, Indiya na da tankokin yaki fiye da 4,200, da motoci masu sulke kimanin 150,000, yayin da Pakistan ke da tankokin yaƙi 2,600 da matoci masu sulke da ba su gaza 18,000.

Rundunar sojin saman Indiya na da jirage 2,229, ciki har da jiragen yaƙi 513 da masu harba bama-bamai 130, yayin da Pakistan ke da jirage 830 a cewar GFI.

A fannin sojin ruwa kuwa, Idniya na da jiragen ruwa 293, fiye da ninkin adadin da Pakistan ke da shi.

Makamai masu linzami da na nukiliya

Makamai masu linzami na Pakistan sun ƙunshi ƙera makamai masu linzami domin amfanin filin daga, da masu cin matsakaici da gajeren zango, da kuma masu cin dogon zango.

Amma makamai masu linzamin Indiya sun fi girma, ciki har da Prithvi wanda zai iya cin kilomita 250 zuwa 600, da kuma Agni series mai cin kilomita 1,200 zuwa 8,000 da kuma Nirbhaya da Brahmos.

Haka kuma, shirin makamai masu linzami na Indiya na nuna irin aniyar ƙasar na daƙile barazanar China, wata makwabciyar ƙasar da ake taƙaddmar kan iyaka.

Amma hakan ba yana nufin cikin sauƙi za ayi nasara kan Pakistan ba, duka ƙasashen biyu na da makaman nukiliya masu ƙarfi iri guda.

Indiya na da makaman nukiliya 172, yayin da Pakistan ke da 170, a cewar ƙiyasin SIPRI.

To sai dai babu tabbas kan yawan makaman nukiliyar da ke cikin shirin harbawa a duka ƙasashen biyu.

Pakistan ta ƙera makaman nukiliya domin yin gogayya da Indiya, yayin da ita kuma Indiya ta mayar da hankali wajen ƙera masu cin dogon zango saboda barazanar China.

Rikicin ƙasasen biyu ka iya zama barazana ga China, makwabciya ga duka ƙasashen, wadda ita ma ta faɗaɗa yawan makamanta da kashi 22 cikin 100, inda ta ƙara yawan makaman nukiliyarta daga 410 zuwa 500.

Yiyuwar fara yaƙi tsakanin ƙasashen biyu na ƙara yawa, lamarin da ya sa ƙasashen duniya ke kira ga duka ƙasashen biyu su mayar da wuƙa kube.