Abin da ya sa Gwamnan Bauchi ke zargin APC da tursasa wa 'yan hamayya don komawa cikinta

Asalin hoton, BSG
A Najeriya, kura ta fara tashi game da yayin sauyin sheka da gwamnoni da sauran jiga-jigan 'yan siyasa na jam'iyyun hamayyar kasar ke yi zuwa jam'iyyar APC mai mulkin kasar.
Gwamnan jihar Bauci, Bala Mohammed ya bayyana tirjiniya a kan abin da ya kira matsin lambar da ake yi masa ta hanyoyi daban-daban, don ya watsar da jam'iyyarsa ta PDP ya koma APC.
Sai dai jam'iyyar ta APC ta musanta wannan zargi, kuma ta ce ba ta tursasa wa kowa ya koma cikinta.
Yayin da a bayyane gwamnoni da yan majalisar dokokin Najeriya da mukarrabansu da dama da suka yi sauyin sheka daga jam'iyyun hamayya zuwa APC mai mulkin kasar, suke cewa sun yi hakan ne don radin kansu, shi kuwa gwamnan jihar ta Bauchi ya yi zargin, cewa ana ta yi wa jam'iyyarsu ta PDP bi-ta-da-kulli, don a gurgunta su, a kuma tilasta masu sauya sheka.
Wani makusancin gwamnan, Babangida Maliya, wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Shira a jihar ta Bauchin, ya yi karin haske:
''Kwarai kuwa da gaske akwai wannan. Ai idan ka duba yanayin rikicin jam'iyyar PDP da halin da take kasancewa. Yau jam'iyyar PDP an kasa barin ta ta zauna lafiya, inda suke amfani da wasu karnukan-farautarsu ko kuma makusantan shugaban kasa don lalata al'amuran jam'iyyun hamayya, musamman ma PDP wadda al'umma ke ganin ita ce mafitarsu a wannan kasa.
''Ita ce za ta share musu hawaye, shi ne ya sa ake mata wannan bi-ta-da-kulli don a ga cewa ba ta zauna lafiya ba.''
Maliya ya kara da cewa, ''daga baya-bayan nan kuma aka shiga matsin lamba da tursasawa ga gwamnan jihar Bauchin, a kokarin tilasta masa komawa jam'iyyar APC karfi da yaji.''
Ciki kuwa har da yi masa zarge-zargen yin almundahanar kudade, tare da kama wasu jami'an gwamnatinsa, a cewar Babangida Maliya.
Sai dai kuma daraktan yada labarai na kasa na jam'iyyar APC, Bala Ibrahim, ya musanta wadannan zarge-zarge:
''Ya kamata a san cewa ciki da gaskiya ba ya tsoron wuka. Tsari ne fa ake bi na dumukuradiyya ba na kama-karya na mulkin soja ba.''
''Mene ne nasa na yin wadannan bayanai na barazana? Dole idan ka ga an haska fitila to ai an ga duhu ne a guri.''
''Su wadannan gwamnoni da suka koma jam'iyyarmu su ya kamata a bai wa dama su fada da bakinsu amma ba wasu su rika zargi suna hasashe suna zato ba,'' in ji Bala Ibrahim.
Ana kallon wannan ce-ce-ku-ce ne a matsayin wata sabat-ta-juyat-ta da ke aukuwa, sakamakon karatowar zaben shekara ta 2027, inda jam'iyyar APC ke neman wa'adin mulki na biyu, yayin da jam'iyyun hamayya ke neman yi mata jirga-in-maye.











