'Jama'ar Bauchi ne za su zaɓar mini magaji'

Asalin hoton, BSG
Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, Bala Mohammed ya ce ba zai yi gaban kansa ba wajen zaɓar wanda zai gaje shi a zaɓen 2027.
Mafi yawa dai ya zamo kamar wata al'ada ga gwamnonin jihohi da ke wa'adin mulki na biyu, su shige gaba wajen ganin naɗin ƴan takara da kuma shigewa gaba domin ganin dole sai shi ne zai gaje su bayan sun kammala mulkinsu.
Gwamnonin sukan kafa hujjar yin hakan ne da buƙatar ganin an ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka faro ko kuma kwaɗayin ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya a karkashin tutar jam'iyyarsu.
To sai dai a hirar sa da BBC, gwamna Bala Mohammed ya ce baya da ra'ayin irin waccan al'ada ta gwamnonin Najeria.
Gwamnan ya ce jama'ar jihar Bauchi ne, musamman masu ruwa da tsaki a siyasance za su tantance wanda ya dace ya gaje shi a ƙarshen wa'adin mulkin nasa, kamar yadda shi ma aka yi masa a baya.
Ya ce burinsa shi ne ganin ''na fito da mutane wanda masu uwa da tsaki a jihar Bauchi za su zaɓa, ba wanda zan imposing masu ba.
''Gani ga wane ya isa wane tsoron Allah, in ya ci b azan zo in ce masa yi nan, yi nan ba domin a zauna lafiya. Ba zan yi siyasar ubangida ba, amma ina son siyasar ɗa'a,'' in ji gwamna Bala.
Dangane da halin da ake ciki a jam'iyyarsa ta PDP a kan shirye-shiryen takara a zaɓe mai zuwa kuwa, gwamnan jihar Bauchi ya ce suna aiki tuƙuru domin ɗinke ɓarakar su ta cikin gida da kuma tabbatar da sun shiga zaɓen da ƙarfin su.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce har yanzu a jam'iyyar ba ta ɗauki matsaya ba a kan shiyyar da ɗan takarar ta a babban zaɓen 2027 zai fito ba ''Ƙila mu sa ɗan kudu, idan muka ga a hangen mu zamu fi cin zaɓe, ƙila kuma mu sa shi a Arewa na tsakiya ko kuma Arewa inda na fito,''
Gwamnan Bala Mohammed ya ce dukkan gwamnonin PDP sun fahimci buƙatar kowa ya jingine buƙatun karan kai domin haɗa hannu wajen fitar da Najeriya daga halin da ta ke ciki.
A baya bayan nan dai ana ƙara samun rabuwar fahimta a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyar PDP, inda ɓangaren gwamnonin jam'iyyar ke jajircewa kan ci gaba da zaman ta babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, tare da cewa ba za su fice daga cikin ta domin shiga wata haɗakar ƴan adawa ba.
Amma a gefe guda akwai ɓangaren tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar da jama'arsa, masu ganin cewa haɗakar ce mafita. Asali ma ana yi masa Kallon wanda ke jagorantar sabuwar háɗakar ta ƴan adawar Najeriya, wada a makon da ya gabata ta narke a cikin jam'iyyar ADC.











