An rantsar da sabon shugaban mulkin soja na Guinea-Bissau

..

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Nicolas Negoce
    • Marubuci, Paul Njie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa reporters
    • Marubuci, Wedaeli Chibelushi
  • Lokacin karatu: Minti 4

An rantsar da Gen Horta N'tam a matsayin sabon shugaban mulkin sojan Gunea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Gen Horta N'Tam ya zamo shugaban da zai mika mulki ga shugabannin farar hula inda zai kasance a mulki na tsawon shekara guda.

An dai rantsar da shugaban ne a wani taƙaitacce kuma gajeren bikin da aka yi ranar Alhamis.

Wasu ƙungiyoyin farar hula a Guinea-Bissau sun soki shugaban da aka hamɓare, Umaro Sissoco Embalo da kitsa juyin mulki na wasan kwaikwayo a kansa bisa taimakon sojoji, inda suke cewa ya shirya wasan kwaikwayon domin hana sakamakon zaɓen da aka yi ranar Lahadi fitowa idan bai yi nasara ba.

Yadda sojoji suka tsare shugaban Guinea-Bissau bayan juyin mulki

..

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin sun yi magana da ƴan ƙasar ta gidan talbijin.

Wasu sojoji sun sanar da ƙwace iko da Guinea-Bissau a daidai lokacin da rahotanni ke cewa shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embalo yana tsare.

Jim kaɗan bayan harbe-harben bindiga a Bissau babban birnin ƙasar, majiyoyin gwamnati sun shaida wa BBC cewa Embala yana tsare a hannun sojojin da suka yi masa juyin mulkin.

Daga nan ne kuma sai sojojin suka bayyana a gidan talbijin ɗin ƙasar suna faɗin cewa sun rushe duk wani zaɓe da aka gudanar, a daidai lokacin da al'ummar ƙasar ke dakon sakamkon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.

Sun ce sun ƙwace ikon ne domin daƙile wani yunƙurin ƴan siyasar ƙasar waɗanda "ke tallafa wa wani gungu da ke ta'ammali da ƙwaya" na manufar lalata ƙasar, sannan sojojin sun kuma rufe iyakokin ƙasar tare da ƙaƙaba dokar hana zurga-zurga da daddare.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Guinea-Bissau da ke tsakanin ƙasashen Senegal da Guinea ta yi kaurin suna wajen kasancewa wata mahaɗa ta safarar ƙwaya, inda kuma sojoji ke da ƙarfin iko tun bayan samun ƴancin ƙasar daga hannun Portugal a 1974.

A ranar Alhamis ne dai ake sa ran fitar sakamakon zaɓen na ranar Lahadi inda manyan ƴan takarar guda biyu, Emballo da Fernando Dias duka suke iƙirarin samun nasara.

Dias ya samu goyon bayan Firaministan ƙasar, Domingos Pereira wanda aka hana takara bisa rashin cancanta.

Da yammacin ranar Laraba ne, Embalo ya shaida wa gidan talbijin na France24 ta waya cewa "An tumɓuke ni."

Majiyoyin gwamnati sun shaida wa BBC cewa Dias da Pereira da Ministan Harkokin Cikin Gida Botché Candé duk suna tsare.

Haka kuma masu juyin mulkin sun tsare babban hafsan sojin ƙasar Janar Biague Na Ntan da mataimakinsa Janar Mamadou Touré, kamar yadda majiyar ta bayyana.

A wata sanarwar haɗin gwiwa, masu sa ido kan zaɓen na Tarayyar Afirka da Ecowas sun bayyana rashin daɗinsu kan juyin mulkin, inda suka ce an fara shirye-shiryen sanar da sakamakon zaɓen ne wanda suka ce "an gudanar lami lafiya" kafin juyin mulkin.

"Muna takaicin yadda aka sanar da juyin mulki bayan mun zauna da manyan ƴan takarar biyu a zaɓen, kuma sun bayyana mana shirinsu na amincewa da sakamakon zabe duk yadda ya fito."

Bayanan bidiyo, An ji ƙarar harbe-harben bindiga a kusa da fadar shugaban ƙasar a babban birnin Bissau na ƙasar

Shaidu sun bayyana cewa sun fara jin harbe-harbe ne da misalin ƙarfe 1 na dare, amma ba su da tabbacin ko an yi asarar rayuka.

Kanfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ɗaruruwan mutane ne suka fara gudu domin neman mafaka bayan jin harbe-harben.

Daga baya ne Janar Denis N'Canha shugaban sojojin da suke gadin fadar shugaban ƙasa ya karanta sanarwar juyin mulki.

Ya ce sun kafa "gwamnatin mulkin soja domin dawo da doka da oda a ƙasar," sannan ya umarci ƴan ƙasar su kwantar da hankalinsu.

Tuni aka kafa shingen sojoji a titunan ƙasar kafin su sanar da ayyana dokar taƙita zirga-zirga.

Sai dai Portugal wadda ita ce ta raini ƙasar ta yi kira da a koma tsarin da doka ta tanada, inda ma'aikatar wajenta ta buƙaci "waɗanda suka shirya juyin mulki da su guji aiwatar da abin da zai bar baya da ƙura."

A cikin shekara biyar da suka gabata, an yi juyin mulki ko yunƙurin juyin mulki guda tara ne a ƙasar.

An zaɓi Shugaba Embaló ne a watan Disamban 2019

Asalin hoton, Corbis via Getty Images

Bayanan hoto, An zaɓi Shugaba Embaló ne a watan Disamban 2019

Embaló ya ce ya samu nasarar tsira daga yunƙurin juyin mulki da dama, amma masu adawa da shi na zargin yana ƙirƙirar labaran ne kawai domin raba kan ƴan ƙasa da neman masoya.

Shugaban mai shekara 53 ya kusa kafa tarihin zama shugaban da ya fara tazarce a ƙasar a cikin shekara 30, kafin a yi juyin mulkin.

Guinea-Bissau, wadda take da mutane kusan miliyan biyu na cikin ƙasashen da suka fi talauci a duniya.

Ƙasar na zagaye da tsibirai da dazuka, wanda hakan ya sa ƙasar take da sauƙinzama mahaɗa domin safarar miyagun ƙwayoyi, inda har Majalisar Ɗinkin Duniya ta annaya ta da "ƙasar miyagun ƙayoyi".

..