Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin AI ne zai kawo ƙarshen ɗan'adam?
Wata maƙalar bincike da aka fitar, wadda ke hasashen yadda ƙirƙirarriyar basira za ta juya akalar duniya, sannan take hasashen yiwuwar ƙarar da al'ummar duniya cikin shekara 10 na cigaba da jan hankali a duniyar kimiyya da fasaha.
Binciken wanda ake kira da AI2027, wasu ƙwararrun masana ƙirƙirarriyar basira ne suka fitar, kuma tuni aka fara tafka muhawara a kansa.
BBC ta kwatanta wasu daga abubuwan da binciken ya ƙunsa da wasu ayyuka da ƙirƙirarriyar basira da aka saba da su suke yi, sannan ta zanta da wasu masana kan irin sauyin da binciken zai iya haifarwa.
Me yake faruwa?
Binciken ya yi hasashen cewa zuwa shekarar 2027, wani babban kamfanin kimiyya na Amurka mai suna OpenBrain zai assasa wata ƙirƙirarriyar basira da za ta kai matakin AGI wato Artificial General Intelligence - matakin da ake ta hanƙoron zuwa inda ake tunanin ƙirƙirarriyar basira za ta iya duk wani aikin da ake buƙata kamar yadda mutane za su yi, ko kuma ta fi mutane bayar da sakamako mai kyau ma.
Amma binciken ya yi hasashen cewa sashen kariya na kamfanin da ake hasashen zai hango yiwuwar mutane su fara ja baya daga fasahar saboda rashin bin ƙa'idoji, amma kuma sai binciken ya yi hasashen cewa kamfanin zai yi watsi ne da gargaɗin.
A hasashen kuma, sun ce kamfanin kimiyya da fasaha na China, Deepcent wanda ya yi fice a fagen ƙirƙirarriyar basira zai biyo bayan OpenBrain bayan watanni.
Binciken ya yi hasashen cewa zuwa shekarar 2027, fasahar ƙirƙirarriyar basira za ta kai matakin da ake kira superintelligent - wadda za ta zama tana da ilimi da ƙwarewa da sauri sama da waɗanda masanan da ƙirƙire su. Za ta zama tana sabunta kanta da kanta ta hanyar ƙirƙirar sababbin abubuwa da inganta wasu abubuwansu na baya.
Hamayyar da ke tsanain China da Amurka kan yunƙurin kaka-gida a fasahar ƙirƙirarriyar basira ce ta sa gwamnatin Amurka ta yi kunnen-uwar-shegu da gargaɗin da ke tattare da abubuwan da bincike ya ƙunsa - kamar ake nema tare da nunawa idan akwai wasu abubuwa da ake ganin sabuwar kimiyya da fasaha za ta saɓa wa rayuwa da tsarin rayuwar ɗana'am.
Binciken ya kuma yi hasashen cewa a shekarar 2029, hamayyar da ke tsakanin China da Amurka zai kai matakin da yaƙi zai iya ɓarkewa a tsakaninsu, ta hanyar ƙirƙirar muggan mukamai na ƙirƙirarriyar basirar.
Amma masu binciken sun yi hasashen ƙasashen biyu za su sasanta, wanda kuma ƙirƙirarrun basirar ƙasashen biyun ne za su sulhunta, su amince su yi aiki tare domin cigaban al'umma.
Abubuwa sun fara nuna alamar nasara domin an fara ganin amfanin ƙirƙararrun basira na superintelligent, inda ake amfani da su wajen magance cututtuka da magance matsalolin sauyin yanayi da yaƙi da talauci.
Amma zuwa tsakankanin 2030, mutane za su fara kawo tsaiko a yanayin ayukan ƙirƙirarriyar basira. Masanan suna tunanin ƙirƙirarrun basira za su fara kashe mutane ta hanyar amfani da wasu na'ukan makaman ƙare dangi.
Me mutane suke cewa game da ƙirƙirarriyar basirar AI2027?
Duk da cewa wasu na ganin batun na AI2027 a matsayin shafa-labari ne na masana kimiyya, masu binciken masana ne ƙwararru da suka yi fice a ɓangaren kimiyyar ƙirƙirarriyar basira.
Daniel Kokotajlo, wanda ya jagoranci binciken na AI2027, ya yi fice wajen hasashen abubuwa da dama a ɓangren ƙirƙirarriyar basira.
Ɗaya daga cikin masu sukar hasashen binciken na AI2027, ita ce wata masaniyar kimiyya ta Amurka mai suna Gary Marcus, wadda ta ce zai iya yiwuwa abubuwan da ake hasashen su faru, amma ta ce ba nan kusa ba.
Ita da wasu masu sukar binciken suna cewa ba a fayyace a ciki ba yadda ƙirƙirarriyar basirar za ta yi tasiri a basira da ƙwarewa, inda suka yi misali da motar da ke tafiya ba tare da direba ba, wadda a cewarsu, duk da yadda aka yi ta ruruta maganar, ba ta cimma nasarar da aka yi hasashe ba.
Shin ana maganar AI2027 a China?
A China, binciken bai zama abin tafka muhawara ba, in ji Dr Yundan Gong, wadda masaniyar tattlin arziki da ƙirƙire-ƙirƙire ce a Jami'ar Kings College London, wadda ta ƙware a kimiyyar China.
"Yawancin tattaunawar da ake yi game da AI2027 a China ba a hukumance ba ake yi ba, wasu ɗaiɗaikun mutane ne suka magana, kuma yawanci suna mata kallon wani tsararren shafa labari ne kawai. Gaskiya ba a mayar da hankali wajen tattaunawa game da ita kamar yadda muka ga ana yi a Amurk," in ji ta.
A taron duniya kan ƙirƙirarriyar basira da aka yi a Shanghai a kwanakin baya, masanin kimiyya na China Li Qiang ya gabatar da muradin ƙasashe na su haɗa kai wajen ƙirƙira da amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira. Masanin ya ce yana so China ta shige gaba wajen tabbatar da hakan.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya fitar da tsare-tsarensa na ƙirƙirarriyar basira, wanda an tsara domin Amrka "ta mamaye" harkokin ƙirƙirarriyar basira.
Me ake cewa game da AI2027 a duniyar fasahar zamani?
Da alama manyan masu faɗa a ji da jagorin manyan kamfanonin ƙirƙirarriyar basira na duniya ba su mayar da hankali kan hasashe-hasashen binciken AI2027 ba.
Yawancin tsare-tsaren da waɗannan kamfanonin suke da su sun sha bamban da na AI2027.
Sam Altman, wanda ya assasa ChatGPT ya ce "duniya ta kusa assasa ƙirƙirarriyar basirar superintelligent" da za ta kawo sauyi kuma ba tare da illa ga ƴan'adam ba.
Ko ma dai yaya abubuwa suka tafi daga nan zuwa shekara 10 masu zuwa, alamu dai sun nuna an fara yunƙurin samar da ƙirƙirarrun basira da suka fi mutane fasaha.