Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Dambarwar zaɓen Adamawa da neman afuwar Buhari
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon jiya ciki har da musanta kasa biyan bashin China da Najeriya ta yi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi afuwar ‘yan ƙasar game da mulkin da ya yi tsawon wa’adi biyu daga 2015 - 2023.
Shugaban ya nemi duk wanda ya ɓata wa rai, ya yafe masa.
Yayin jawabinsa na bikin idin ƙaramar sallah, wanda daga ita zai miƙa mulki, Buhari ya gode wa ‘yan Najeriya saboda amincewar da suka yi da shi, ya ja ragamar ƙasar tsawon shekara takwas.
Wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ya fitar, ta bayyana irin gudunmawar da Buhari ya bayar ta fuskar shugabanci a sama da shekara 40.
Dambarwar zaɓen gwamnan Adamawa da aka ƙarasa
Ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen da aka ƙarasa a makon jiya cikin jihar Adamawa ne sai kwatsam kwamishinan zaɓe na jihar, Barrista Hudu Ari ya shiga zauren tattara sakamako na Yola cikin rakiyar 'yan sanda a ranar Lahadi, inda ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen.
Bai dai yi bayani filla-filla game da sakamakon da kowacce jam'iyya ta samu, da kuma yadda aka ci zaɓen ba.
Matakin da ya sa INEC ta ce aikin da jami'in nata ya yi, ya saɓa doka kuma haramtacce ne don haka ba za a yi aiki da shi ba.
Daga baya ne kuma, 'yar takarar APC, Aisha Ɗahiru Binani ta shigar da ƙara gaban babbar kotu a Abuja tana neman umarnin wucin-gadi.
Ta dai nemi kotun ta yi fassarar doka game da matakin da hukumar zaɓe ta ɗauka ranar 16 ga watan Afrilu, bayan kwamishinan zaɓen jihar ya ayyana cewa ta yi nasara a zaɓen 18 ga watan Maris da kuma na cike-giɓi a ranar 15 ga watan Afrilu.
'Yar takarar ta kuma nemi kotu ta ba da umarni sannan ta hana INEC da jami'anta ɗaukar ƙarin wasu matakai na bayyana wanda ya yi nasara a zaɓukan da aka yi, har sai ta yanke hukunci a kan buƙatar yin fassarar.
Fintiri ya ci zaɓen gwamnan Adamawa - INEC
Ana tsakiyar dambarwar ne kuma, da yammacin ranar Talatar da ya wuce, sai jami'in tattara sakamako ya ci gaba da karɓa tare da bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka ƙarasa.
Bayan kammala karɓar sauran sakamakon zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen da ƙuri'a, 430, 861.
Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa, Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a, 398, 788.
Nasarar ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa'adi na biyu.
Buhari ya amince da dakatar da Hudu Ari
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin hukumar zaɓen ƙasar na dakatar da kwamishinanta na jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Tuni dai hukumar zaɓe ta damƙa batun Hudu Ari hannun babban sufeton 'yan sanda don ya binciki halayyar kwamishinan a lokacin zaɓen cike giɓi na jihar Adamawa.
Shugaba Buhari ya umarci gudanar da bincike da gurfanar da Hudu Ari gaban shari'a, matuƙar an same shi da hannu.
Najeriya ta musanta gaza biyan bashin China
Ofishin kula da basuka na Najeriya, ya musanta zargin cewa gwamnatin tarayya ta gaza biyan kuɗin ruwa ga China don samun bashi.
Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa an ci tarar Najeriya $90m bayan bashin da China ke bin ta ya ƙaru zuwa dala miliyan 240 a cikin shekaru biyu.
An ce an karɓo bashin ne domin gyara waɗansu layukan dogo a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, DMO ya musanta rahotannin, inda ya ce Najeriya ta jajirce wajen ganin ta mutunta yarjejeniyar bashin da ake bin ta, kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wajen biyan basukan da ta ciyo.