Sojojin Nijar sun saki ɗan Mohamed Bazoum

Mohamed Bazoum

Asalin hoton, OTHERS

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta saki ɗan hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum daga ɗaurin talalar da ta yi masa.

Bayanin sakin Salem Bazoum na ƙunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga kotun soji, CNSP, a Yamai jiya Litinin.

Sanarwar ta ce an danƙa shi ga ministan harkokin waje na Togo Robert Dussey.

Ana ganin tuni ministan ya ma bar ƙasar da shi zuwa babban birnin Togon, Lome.

Takardar bayanin sakin nasa, wadda ke ɗauke da sa hannun Squadron Leader Moumouni Abdoulaye, wanda shi ne babban akawun kotun sojin ta tabbatar da cewa Salem Bazoum, mai shekara 23, wanda aka tuhuma da laifin maƙarƙashiya don cutar da tsaron ƙasa ko hukuma, ya samu saki na wucin-gadi, daga alkalin da ke bincike a kansa na kotun sojin a ranar 8 ga watan Janairun 2024, bisa sharaɗin sake amsa kiran shari’a a duk lokacin da ake buƙatarsa.

Tun bayan da sojoji suka hamɓarar da mahaifinsa Mohamed Bazoum daga mulkin Nijar a ranar 26 ga watan Yuli na shekarar da ta kare 2023, sojin ke tsare da shi tare da mahifin nasa, da kuma mahaifiyarsa Khadijah Bazoum a fadar shugaban ƙasar.

Sai dai kuma kotun sojin ta Nijar ba ta bayar da bayani game da makomar Bazoum, wanda shi ma ta tuhuma ba, da kuma mai dakinsa.

An naɗa Togo ne tare da Saliyo a matsayin masu shiga tsakani na ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO a rikicin siyasar na Nijar, da nufin samar da kafar tattaunawa tsakanin sojojin da ke riƙe da mulki da kuma ƙungiyar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan shiga tsakanin gwamnatocin na Togo da Saliyo, mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da Afirka , Mary Catherine (Molly) Phee wadda ta ziyarci Nijar a watan Disamba, ita ma an ce ta taka muhimmiyar rawa wajen sakin ɗan na Bazoum.

A watan da ya gabata ne shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma suka gindaya sharuɗɗan cire wa Nijar ɗin takunkuman da suka sanya mata, bayan hamɓarar da gwamnatin farar hular ta Nijar.

Shugabannin sun kafe cewa lalle sai sun ga cigaba wajen mayar da ƙasar mulkin farar hula, ciki har da sakin hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ba tare da wani sharaɗi ba, kafin su sassauta takunkuman.

A watan da ya gabata ne kotun ECOWAS ta zartar da cewa tsare iyalan ya saba doka, sannan kuma ta bayar da umarnin mayar da Bazoum kan mulki, abin da gwamnatin sojin ƙarƙashin ikon tsohon kwamandan dakarun da ke gadin fadar shugaban ƙasar, Birgediya Janar Abdourahamane Tchiani tun da farko ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba za ta saɓu ba.

Bayan hukuncin kotun ta ECOWAS, wanda ba a ɗaukakawa zuwa gaba, lauyoyi a shari’ar sun ce kotun ta bai wa gwamnatin sojin wata ɗaya, ta faɗi yadda za ta aiwatar da hukuncin.

Jam’iyyar PNDS ta Mohamed Bazoum da kuma ‘yan uwa sun ce an katse wa iyalan hanyoyin samun ruwan famfo da wutar lantarki.

Juyin mulkin na Nijar ya kasance daya daga cikin guda takwas da sojoji suka yi a yankin Afirka ta yamma da kuma Afirka ta tsakiya.

Sauran ƙasashen da sojoji suka yi juyin mulkin bayan Nijar su ne Burkina Faso, da Mali, da Guinea da kuma Chadi, kodayake ita Chadi ɗan marigayi shugaban ƙasar ne ya karɓe iko bayan kashe mahaifinsa Idriss debby a fagen yaƙi da 'yan tawaye.