Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu bakwai na ban mamaki da suka faru a karon farko a duniya a 2022
Shekarar 2022 ta zo da wasu al’amura masu ban mamakin – kuma ba a duniyarmu kaɗai al’amuran suka faru ba.
Daga kan ƙaruwar yawan mutanen duniya zuwa wani shawagi a sararin samaniya da wani madubin ganhen nesa ya yi inda ya gano wasu abubuwan da suka faru miliyoyin shekaru baya.
Nasa ta kawar da wani dutse da ya tunkaro duniyar Earth
Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka Nasa, ta yi nasarar kawar da wani ƙatoton dutsen asteroid, irin mai shawagi a sararin samaniyar nan a lokacin da ya tunkaro duniyarmu ta Earth, inda Nasa ta yi amfani da jirgin sama jannati wajen kawar da hsi a ranar 28 ga watan Satumba.
An tsara yin karon dutsen da kumbon Nasa ne don gwada ko ana iya kawar da irin wadannan duwatsu na asteroid daga faɗowa duniyar Earth, waɗanda ke yi mata barazana. An gano za a iya kawar da su.
An gano ɓurɓushin roba a cikin jinin ɗan adam
Wani bincike da aka wallafa a mujallar Environment International a watan Maris ya gano cewa akwai ɓurɓushin roba a cikin jinin ɗan adam a cikin kashi 80 cikin 100 na mutanen da aka yi wa gwajin.
Wadannan ɓurɓushin robobi ƴan ƙanana ne da tsawon su bai wuce 5mm ba – suna samuwa ne a yayin da robobi da ledojin da aka zubarwa suka murmushe suka gurɓata teku ko muhalli.
Ba a gano illar waɗannan ɓurɓushin robobin ba, amma masu bincike sun ce sababbin sakamakon bincike na nuna damuwa cewa za su iya lalata ƙwayoyin halittar ɗan adam.
Wasu abubuwa da aka yi a karon farko a Gasar Cin Kofin Duniya
Gasar Cin Kofin Duniya ta Fifa ta 2022 za ta daɗe a littafin tarihi saboda irin jerin abubuwan ban mamakin da suka faru.
Wannan ne karo na da aka yi gasar a wata ƙsar Larabawa kuma ta Musulmai – wato Qatar.
Sannan kuma a gasar ne aka samu mace rafari ta farko inda Bafaranshiya Stephanie Frappart ta kasance babbar rafari a wasan da aka yi tsakanin Jamus da Costa Rica.
Ita ce ta jagoranci tawagar rafari mata zalla da aka samu mataimakan rafari har biyu da suka haɗa da Neuza Back daga Brazil da kuma Karen Medina daga Mexico.
Wani abun da ya kasance a karon farko a gasar shi ne nasarar da wata ƙsar Larabawa kuma ta Afirka, Moroko ta yi har zuwa wasan kusa da na ƙarshe,
A ƙarshe sai ga Lionel Messi ya ɗaga kofin duniyar da ƙsarsa Ajanti ta lashe, wanda shi ne lokaci na farko da ya ci gasar bayan fafatawa a gasar cin kofin duniyar har sau biya.
Mutum biliyan takwas a duniya... ana kuma ta ƙara yawa
15 ga watan Nuwamban 2022. Wannan ce ranar da yawan al’ummar duniya ya zarta biliyan takwas a karon farko, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
“Wannan ƙaruwar ya faru ne saboda yadda ake ƙara hayayyafa sakamakon ci gaban fannin lafiya da yanayin abinci da tsafata da kimiyyar magunguna da aka samu.
“Sannan kuma an samu ƙaruwar hayayyafa a wasu ƙasashen,” in ji MDD a wata sanarwa.
Kazalika MDD ta ce a yayin da aka shafe shekara 12 kafin yawan al’ummar duniya ya ƙaru daga biliyan bakwai zuwa takwas, za a shafe shekara 15 nan gaba kafin a ƙara wata biliyan ɗaywan, saboda yadda a yanzu kuma yawan hayayyafa ke raguwa.
Riga-kafin zazzabin maleriya da zai kawo sauyi a duniya
Masana kimiyya na Jami’ar Oxford University sun sanar a watan Satumba cewa sun samar da riga-kafin cutar maleriya da ka iya sauya duniya.
Riga-kafin, wanda ake sa ran a shekarar 2023 za a fara fitar da shi, an gano shi ne bayan kashi 80 cikin 100 gwajin da aka yi ya yi tasiri a kan mummunar cutar, wacce ke kashe mutum 400,000 duk shekara a fadin duniya.
Masana kimiyyan sun kuma ce riga-kafin ba zai yi tsada ba.
Cutar maleriya na daga cikin cututtukan da ke jawo mace-macen yara kuma samar da riga-kafinta abu ne mai wahaka.
Aike madubin hangen nesan James Webb sararin samaniya
Madubin hangen nesa na James Webb na daga cikin waɗanda suka mamaye kanun labarai a 2022 – tun bayan da aka ƙaddamar da shi a watan Yuli ya aiko hotuna tar-tar masu ban al’ajabi daga sararain samaniya.
Daga cikinsu har da hoton can tsakiyar yankin samaniyarmu mai dandazon taurari da kuma gaba da nan inda ake hasashen a can aka yi ƙarar nan ta farko ta Big-Bang.
An ƙera sabon madubin ne don leƙo halittun da ke can cikin sarrain samaniya - da kuma yin waiwaye kan yadda yanayin wajen ya kasance a baya kaɗan - fiye da yadda muka iya sani.
Madubin Webb ya gano haske daga taurarin farko a sararin samaniya, shekara biliyan 13.5 da suka gabata.
Firaministan Birtaniya da ba Bature ba na farko
A cikin shekarar 2022 Birtaniya ta yi firaministoci biyu cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Liz Truss ta kasance ita ce firaministar da ta yi kwanaki kaɗan wato 45 a kan gadon mulkin.
Bayan saukar ta sai Rishi, wanda asalinsa Ba’indiye ne ya maye gurbinta ranar 25 ga watan Oktoba.