Jaririyar da aka ceto daga ɓaraguzai ta koma hannun ƴan uwan mahaifinta

Baby Afraa had been saved by rescuers earlier in February from beneath the rubble of a building in north-west Syria

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mahaifiyar jaririya Afraa ta mutu ne jim kaɗan bayan ta haifeta

Wata jaririya da aka ceto daga cikin ɓaraguzan wani gini a Syria, wadda ita ce kaɗai a cikin iyalanta ta tsira daga mummunar girgizar ƙasar da ta afka wa yankin, ta koma hannun ƴan uwan mahaifinta.

Dubban mutane sun bayyana sha'awarsu ta karbar jaririyar domin su raine ta, saboda an gano ko cibiyarta ma ba a yanke daga jikin mahaifiyarta ba a lokacin da masu ceto suka isa wajen da baraguzan ginin suka danne ta da sauran iyalan gidan.

An sallame ta daga asibiti bayan da wani gwajin kwayar halita na DNA ya tabbatar cewa wata ƴar uwar mahaifinta na da dangantaka ta jini da ita.

Likitoci sun kuma ce tana cikin ƙoshin lafiya.

"Ta shiga cikin ƴaƴana yanzu," inji kawunta - wato mijin ƴar uwar mahaifinta Khalil al-Sawadi - yayin wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaru na Associated Press.

"Ba zan nuna bambanci tsakaninta da ƴaƴana ba."

A halin yanzu an raɗa wa jaririyar suna Afraa - wanda shi ne sunan mahaifiyarta.

Jim kaɗan bayan an ceto ta, jami'ai sun riƙa kiran ta da sunan Aya, wanda ke nufin abin al'ajabi da Larabci.

Bidiyon yadda aka ceto ta ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka ga wani cikin masu aikin ceto yana gudu yayin da yake dauke da ita, ta yi butubutu da ƙura a jikinta.

Rahotannin sun ce ta shafe sa'a 10 a karkashin ɓaraguzan ginin kuma likitoci sun ce an kai ta asibiti ne cikin wani mawuyacin hali, tana da ciwurwuka a kowane bangare na jikinta.

Afraa's (right) aunt and uncle also welcomed a baby girl (left) of their own three days after the quake.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Al-Sawadi dauke da Afraa da jariryar da matarsa ta haifa kwana uku bayan an haifi Afraa

Gidan da iyayenta da ƴan uwanta suke zama na cikin gidaje 50 da girgizar ƙasar mai karfin maki 7.8 na ma'aunin Richter ta ruguza baki ɗaya a garin Jindayris.

Garin na cikin wani yanki da ƴan adawa ke iko da shi a lardin Idlib, kusa da kan iyakar Syria da Turkiyya.

Mahaifiyarta ta fara naƙuda ne jim kaɗan bayan da iftila'in ya faru, kuma ta mutu jim kaɗan bayan ta haifi Afraa, kamar yadda wani ɗan uwanta ya bayyana.

Mahaifinta da ƴan uwanta huɗu da wata ƙanwar mahaifinta duka sun mutu a sanadiyyar girgizar ƙasar.

Bayan an kai ta asibiti, sai jama'a suka rika bayyana sha'awar a ba su ita, amma daga baya an mika ta ga Sawadi da matarsa Hala domin su tafi da ita gidansu - gidan da shi ma girgizar ƙasar ta ruguza shi.

Wannan lamarin ya sa tilas suka koma gidan ƴan uwan Sawadi kafin a gyara muhallin nasu.

Dama matarsa Hala na da tsohon ciki, inda bayan kwana uku da afkuwar girgizar ƙasar ta haifi ƴa mace.

"She is one of my children now," Afraa's uncle Khalil Al-Sawadi said

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Al-Sawadi: "Ta shiga cikin ƴaƴana yanzu"