An kama gomman mutane a Indiya bayan rikici a kan wani fim game da ƙungiyar IS

Asalin hoton, Film poster
An kama fiye da mutum 100 a jihar Maharashtra ta yammacin Indiya, bayan kashe mutum ɗaya, wasu takwas kuma suka ji raunuka a wani rikicin ƙabilanci.
Rahotanni sun ce tarzomar wadda ta faru a birnin Akola, ta tashi ne sanadin wani saƙo da aka wallafa a shafin sada zumunta game da fim ɗin 'The Kerala Story' mai haddasa ka-ce-na-ce.
Hukumomi sun katse layukan intanet, sun kuma ƙaƙaba dokar hana fita don shawo kan lamarin.
Wata 'yar sanda mai muƙamin kurtu na cikin waɗanda aka jikkata a tashe-tashen hankulan.
'Yan sanda sun ce a ranar Asabar ne tarzomar ta faro lokacin da 'yan wata ƙabila suka taru a wani ofishin 'yan sanda na birnin Akola, suna zanga-zanga a kan saƙon da aka wallafa a shafin sada zumunta game da fim ɗin.
Rahotanni sun ce wani hoto ne da aka ɗauka da wayar salula na wata hira tsakanin mazauna birnin biyu, kuma ɗaya a cikinsu ya yaɗa a shafin Instagram.
Wani jami'in 'yan sanda ya faɗa wa jaridar The Indian Express cewa wasu saƙonni game da hirar "suna iya ƙona zuciyar wasu mabiya addini", amma bai bayar da ƙarin bayani ba.
Ofishin babban ministan Maharashtra, Eknath Shinde ya yi roƙon samun zaman lafiya, kuma ya ba da umarni ga 'yan sandan jihar su ɗauki tsattsauran mataki a kan waɗanda aka samu da hannu a tashin hankali.
Fim ɗin The Kerala Story, wanda aka saki a sinimu cikin makon jiya, ya haddasa taƙaddama watanni ma kafin a fitar da shi.
Fim ɗin ya siffanta wani ƙirƙirarren labari na wasu matan Indiya uku daga jihar da ke kudancin ƙasar da suka shiga ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta IS.
'Yan adawar siyasa sun soki lamirin fim ɗin, inda suka bayyana shi da cewa farfaganda ne kawai.
Sai dai masu shirya fim ɗin sun ce sun yi aikin ne bayan kwashe shekaru suna bincike da kuma nazarin abubuwan da ke faruwa a rayuwar zahiri.
Fim ɗin ya samu goyon baya daga shugabannin jam'iyyar BJP mai mulki, ciki har da a ƙalla ministocin tarayya biyu, sannan Firaminista Narendra Modi ya yaba wa fim ɗin a wani gangamin yaƙin neman zaɓe cikin wannan wata.
Gwamnatin jihar West Bengal ta haramta fim ɗin, yayin da jihohi guda biyu - Uttar Pradesh da Madhya Pradesh, dukkansu a ƙarƙashin mulkin jam'iyyar BJP - suka ɗauke wa fim ɗin haraji.
A ranar Lahadi ma, faɗa a kan fim ɗin The Kerala Story ya kaure a wata kwalejin nazarin aikin likitanci da ke lardin Jammu na Kashmir a ƙarƙashin ikon Indiya.
An jikkata ɗalibai a ƙalla biyu a tarzomar, wadda ta faro bayan wani ɗalibi ya yaɗa wani saƙo a zauren ɗalibai na WhatsApp.
Wani tsohon babban minista Mehbooba Mufti ya ɗora alhakin tashin-tashinar da ta ɓarke a kan gwamnatin tarayya, inda ya zarge ta da ƙarfafa gwiwar tashin hankali "ta hanyar fina-finan da ke iza wutar rikice-rikicen ƙabilanci".











