An fara gwajin allurar tsarin iyali ta maza a Indiya

    • Marubuci, அமன் யாதவ்
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, பிபிசி இந்தி

A baya-bayan nan, wani binciken Cibiyar Lafiya a Indiya (ICMR) ya gudanar, ya shiga sahun kanun labarai a ɓangaren likitanci a duniya.

Bayan shekaru bakwai na bincike, an samu nasarar kammala gwaji na allurar hana maza haihuwa.

Wannan yana nufin cewa yanzu an yarda da allurar kuma za a iya amfani da ita.

ICMR ta bayyana cewa allurar ba ta da mummunan sakamako kuma tana da tasiri sosai.

Ta yaya ake gudanar da gwaje-gwajen asibiti?

An wallafa sakamakon gwaje-gwajen na uku na maganin a watan da ya gabata a cikin mujallar Andrology.

Dole ne allurar, wadda ake kira Reversible Inhibition of Sperm Under Guidance (RISUG), ta bi matakai uku na gwaji kafin a amince da ita.

Mutane daga Delhi, Udhampur, Ludhiana, Jaipur da Kharagpur sun kasance cikin waɗanda aka yi gwajin a kansu.

Gwajin ya kunshi maza 303 matansu masu lafiyar yin jima'i waɗanda ke tsakanin shekaru 25 zuwa 40 da matansu.

An haɗa waɗannan ma'auratan a cikin gwajin lokacin da suka tuntuɓi asibitin kayyade iyali da likitocin da suka kware kan lafiyar al'aurar mata.

Waɗannan ma'auratan sun kasance iyalai waɗanda ke buƙatar aiki don tsinka jijiyar da ke samar da maniyyi ko suka yanke shawarar ba za su ƙara haihuwa ba.

A lokacin waɗannan gwaje-gwaje, wanda likitoci suka jagoranta, an bai wa maza magani da ya kai gram 60.

Ta yaya maganin ke taimakawa wajen hana haihuwa?

ICMR a cikin bincikenta da gwaje-gwajenta, ta gano wannan cewa allurar tana da ingancin gaske musamman cikin hanyoyin hana ɗaukar ciki (maza da mata) da aka amince da su har zuwa yau.

An kuma gano cewa ba shi da wata mummunar illa.

Bincike ya nuna cewa allurar tana da kashi 97.3 cikin 100 na nasara wajen cimma burin da ake so.

A lokaci guda, yana da tasiri da kashi 99.02 wajen hana haihuwa. Azoospermia shi ne toshewar fitar maniyyi.

Da zarar an yi wa mutuma allurar, tasirinsa zai kasance har na kusan shekaru 13.

Ana iya kaucewa ɗaukar ciki a wannan lokacin. Kwaroron roba da magungunan hana ɗaukar ciki na (OCP) na iya taimakawa wajen hana mace ɗaukar ciki na wani lokaci.

Hakanan, akwai wata na'ura da ake sakawa wadda ke hana daukar na dogon lokaci.

Aiki don sinka jijiyar da ke samar da maniyyi, hanya ce ta hana haifuwa ta dindindin. Amma an ce shekaru 13 na haifar da ruɗani a tsakanin maza.

Domin yana taimakawa na ɗan lokaci kaɗan, inda ake ganin cewa wannan maganin ba kowa bane yake ganinsa a matsayin na dindindin ko ke da tasiri.

Fara sabon babi

Kwararru sun yi imanin cewa magunguna da aka samar don hana mata ɗaukar ciki, ya ba su ƴanci na yadda za su tsara iyalansu.

Duk da haka, wannan tsarin kiwon lafiya ya ɗora alhakin hana haihuwa a kan mata. Idan aka yi la’akari da kididdigar, a bayyane yake cewa dole ne mata a Indiya su ɗauki nauyi fiye da maza.

Wannan ba yana nufin maza ba su da isassun hanyoyin da za su ɗauki nauyin tsarin iyali ba. Suna samun kwaroron roba.

Kwanan nan ma, an fara yin amfani da kwayoyi. Dangane da Binciken Kiwon Lafiyar Iyali na 2019-21 (NFHS-5), ƙasa da namiji ɗaya cikin 10 ko kashi 0.5, na amfani da kwaroron roba.

A irin wannan yanayi, ana samun mata da ba sa ɗaukar kwayayen haihuwa a cikin al'umma.

Ko da yake masana sun ce tsinke jijiyar da ke samar da maniyyi yana da lafiya kuma yana da sauƙi, sai dai ana ganin wannan hanyar ba ta kai sauran ba wajen hana haihuwa.

A wani bincike kan Wanene ke da alhakin Tsarin Iyali, kashi 50 na maza daga biranen Uttar Pradesh, Telangana da Bihar na ƙasar Indiya, sun ce haihuwa aikin mata ne kuma bai kamata maza su damu da hakan ba.

A cewar likitoci, akwai camfe-camfe da yawa da ke da alaƙa da hana haihuwa a cikin maza. Misali, ana ci gaba da tunanin cewa amfani da kwaroron roba yana rage jin daɗin jima'i.

Game da haihuwa a ɓangaren maza, akwai tatsuniyoyi da fargabar cewa yana rage wa maza karfi da lafiyar yin jima'i.

Dr. S. Shantha Kumari, shugabar ƙungiyar masu kula da mata masu ciki da cutukan mata a Indiya, ta ce akwai tatsuniyoyi da rashin fahimta da yawa game da allurar tsinka jijiyar samar da maniyyi a cikin al'ummar Indiya.

Ta bayyana cewa saboda haka duk wani nauyi yana kan mata.

Bidisha Mondal, wata mai bincike da ke aiki don inganta daidaiton jinsi, ta shaida wa BBC yayin wata hira da ta yi cewa, matan da ke shan magungunan hana haihuwa sun yi yawa a Indiya.

Da take ambato bayanai daga Hukumar Kula da Lafiya ta ƙasar, Bidisha ta ce kashi 93 na mata suna haihuwa idan aka kwatanta da maza.

A lokaci guda, an yi nuni da cewa tarihi shi ma ya taka rawa wajen sanyawa maza tsoron amfani da maganin hana haihuwa.

Masana sun ce batun hana haihuwar dole, wanda aka gabatar a 1975, ya haifar da tsoro a tsakanin maza.

Suna tunanin cewa yi wa maza aiki na tsinka jijiyar da ke samar da maniyyi zai lalata musu mazakuta.

SP Singh, shugaban Cibiyar Nazarin Rayuwar Al'umma a Indiya, ya shaida wa BBC cewa ba shi da masaniya game da sabuwar allurar da ICMR ta yi da gwajin asibiti a kai.

Amma lokaci ne kawai zai nuna yadda wannan allurar za ta yi tasiri wajen sarrafa al'ummar Indiya.