Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Ɗan uwana ya kashe kansa yayin da nake ƙoƙarin hana wasu kashe kansu’
- Marubuci, Serin Ha
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
"Lokacin da na ga gawar ƙanina, shekaru uku da suka gabata, wata ne na Mayu amma sai da zuciyata ta daskare tamkar lokaci ne na sanyi.”
Wani yaya ke nan yake bayani.
Sai da Jang Jun-ha ya suma musamman da yake ɗan ƙaramin ɗan uwan nasa shekarunsa a duniya 35 ne kawai.
Jang ya kira `yan sanda bayan kwashe kwanaki da kasa samun dan uwansa ta wayarsa ta salula.
Da suka bude kyauren dakin dan uwan nasa da karfi, sai Jang ya tarar da Jun-An a kwance kan gado babu rai.
“A wannan lokaci, ina wani kwas a cibiyar hana kisan kai da kai domin zama mai koyarwa,” in ji Jang.
“Na ziyarci makarantu domin ilimantar da yara a game da alamu da aka fi saurin gane wanda yake tunanin kashe kansa, da abin da ya kamata a yi domin taimaka musu.
Na kokarta wajen ceton rayukan jama`a amma ban taba tunanin dan uwana zai kashe kansa ba.”
Har yanzun abu ne da yake zame wa Jang mai shekara 45 a duniya mai wahala, yin magana a sarari a kan halin da iyalansa suka shiga domin kuwa batu ne mai ban tsoro ga al`ummar Koriya ta Kudu.
Sai dai yana yin nasa matukar kokarin wajen fadakarwa ta hanyar bayar da nasa labarin.
Manyan ƙasashen duniya da mutane suka fi kashe kansu
Koriya ta Kudu ta yi suna game da mutane `yan K-pop, wato makaɗa da maraya, da kuma kamfanoni na duniya irin su Samsung.
Sai dai a wannan al`umma da duniya take mata kallon ƙasar da ta kai ga nasara, a kullum wayewar garin Allah sai mutum 36 sun ɗauki ransu da kansu.
Ƙasar ce ta fi yawan masu kashe kansu a tsakanin ƙasashe 38 da suke cikin ƙungiyar kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, wato Organisation for Economic Co-operation and Development (OECD).
Hukumar ƙididdiga ta Koriya ta Kudu ta ce mutane 13,352 ne suka kashe kansu da kansu a shekarar 2021.
Kashe kai shi ne kan gaba a abubuwan da suke haddasa mutuwa a tsakanin `yan Koriya ta Kudu, `yan shekara 10 zuwa 39.
Fiye da biyu cikin mace-mace biyar a tsakanin matasa, kashi 43.7 cikin 100 mutuwa ce ta kashe kai.
Hakan ya ƙaru zuwa kashi 56.8 a cikin matasa `yan shekara 20, sannan yana a kashi 40.6 cikin dari a mutane masu shekara 30 a duniya.
Ɗan'uwan Jang yana cikin wannan rukuni da yake ƙoƙarin kaiwa ga gaci.
A Seoul an samu kashi 23.6 na mace-macen a mutum 100,000, ya haura ninkin hakan a tsakanin kasashen da ke cikin OECD inda ake da akalla mace-mace 11.1.
A kwanakin nan ne gwamnati ta sanar da wani shiri na shekara biyar da zai yi rigakafin kashe kai da nufin rage adadin zuwa kashi 30 cikin 100.
Burin da ake da shi na rage wannan matsala da kashi 30 cikin dari yana da muhimmanci saboda idan gwamnati ta kai ga nasara, ba za a sake kiranta da sunan kasar da aka fi kashe kai a tsakanin kasashen da suke cikin OECD ba.
Al`ummar da matsi ya yi wa dabaibayi
Yawan kashe kai da ke aukuwa a Koriya ta Kudu cakuɗuwar dalilai ne na tattalin arziki da na zamantakewa da na al`adu.
Ƙasar ta yunƙura ta zama mai ƙarfin tattalin arziki a duniya bayan yakin Koriya ya ɗaiɗaita ta, yaƙin da aka ƙare shi a 1953.
Sai dai wannan haɓɓaka ta tattalin arziki ba ta yi sanadiyyar faɗaɗar ayyukan jin dadin jama`a ba, a maimakon haka, sai ta taimaka wajen ƙaruwar rashin daidato.
Wannan ya haifar da wata al`umma da aka gina ta a kan gasa da son cimma nasara, wanda hakan ya jefa `yan ƙasar da dama cikin matsalolin da suke shafar ƙwaƙwalwa.
Sai bayan da ya rasu ne, Jang ya gane cewa ashe dan'uwansa yana zuwa ana kula da shi duk mako, tsawon shekaru 10 da suka gabata.
“Dan'uwana ya shahara ne a nazarin fina-finai kuma yana shirin zuwa kasashen waje karatu.
Kamar sauran iyalai masu dama na Koriya ta Kudu, yana cikin babban matsi na ganin ya kai ga nasara.
Sai dai matsala ta kudi take masa tarnaki da ta sa rayuwar ta masa wahala,” in ji Jang.
“Dan'uwana yana ta fama da bakin ciki. Abin ya dame ni, kasancewar duk dadewar nan ban taba lura da hakan ba.”
Da dadewa kwararru suna ta yin nuni da hadarin da ke cikin al`ummar da ta fi mayar da hankali ga nasarar da mutum ya samu, musamman a bangaren kudi ko matsayi na zamantakewa.
“Bayan kashe kai da ya zama ruwan dare a Koriya ta Kudu, akwai kuma labari mara dadi, na al`ummar da take da rauni a tsarinta na kula da jin dadin jama`a da tallafa musu, illa na wanda ya fi samun nasara, inda akan duba kudi, nawa mutum ya tara,” in ji Soong-nang Jang, Shugaba a kwalejin horar da jami`an jinya ta Jami`ar Chung-Ang.
“Kuma a lokacin da al`adar zumunci take ci gaba da rauni a tsakanin `yan uwa da makwabta, sai kowa ya karkata ga gwagwarmayarsa ta neman nasara tasa shi kadai.”
‘Bari mu yi magana’
Sannu a hankali al`adar tana sauyawa, sai dai har yanzun da sauran rina a kaba.
“`Yan Koriya ta Kudu sun saba da kokarin kasancewa a gaba a wannan al`umma da kowa yake ta kansa, kuma Koriya ba kasa ce da za ka iya fitowa cikin sauki ka fadi abubuwan da suke damun ka ba,” in ji Yeon-soo Kim, Daraktan LifeLineSeol, kungiyar taimako da take samar da taimako sa`a 24 a kowace rana ga ayyuka na riga kafin aikata kisan kai.
“Mutane suna bukatar wurin da za su bayyana gwagwarmayarsu da walwalar bayyana abubuwan da suke ji ba tare da wata matsala ba.
Muna bukatar mu ci gaba da tunatar da jama`a cewa akwai hanyoyi daban-daban na kai wa ga nasara da kuma matukar sanin hakan.”
A yanzu Jang yana aiki ne a matsayin kwararre a bangaren kwakwalwa a wata cibiya ta kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Seoul, yana taimaka wa iyalai da lamarin na kashe kai ya shafa ko mutanen da suke tunanin kashe kansu.
“Aiki ne mai wahalar gaske. Iyalai ne suke soma ganin gawar. Suna tuna ganin da kwatanta abin da ya auku.”
Jang yana sane da yadda wannan tattaunawa ke shafar tunaninsa.
“Sai dai wannan aiki ne da ya dace mutum ya yi a lokacin da ka ga suna samun sauki.”
Kuma akwai amincewa da kuma fahimta a nasa iyalan shi ma.
Jang ya ambaci cewa dan'uwansa ya bar wata takarda inda yake ba iyayensa da shi hakurin ya tafi ya bar su.
Sai dai da iyalan suka ziyarci kabarinsa a lokacin bazarar da ta gabata, Jang ya shaida wa kanin nasa `Ya yi`.
“Ba sai ka ce a yi hakuri ba. Muna nan lafiya lau muna kula da juna,” in ji Jang.
“Saboda haka ba bukatar bayar da hakuri, za mu dawo.”