Babban zaɓen Birtaniya: Ta yaya ake cin zaɓen kuma yaya ake kafa gwamnati?

Tutar Birtaniya da akwatin zaɓe

Asalin hoton, Getty Images

Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya sanar da shirinsu na gudanar da babban zaɓen ƙasar ranar 4 ga watan Yuli.

An matso da ranar ne ba kamar yadda aka tsara tun farko ba.

Mun duba wasu daga cikin tambayoyin da za ku so ku san amsarsu.

Yaushe ne babban zaɓen Birtaniya?

Za a gudanar da babban zaɓen ranar 4 ga watan Yulin 2024. Zangon mulkin siyasa a Birtaniya shekara biyar ne, kuma saboda jam'iyyar Conservative ce ta lashe zaɓe na ƙarshe da aka yi a Disamban 2019, a doka wajibi ne a gudanar da wani zaɓen zuwa Janairun 2025.

An raba Birtaniya zuwa yankuna 650, waɗanda ake kira mazaɓu. Masu jefa ƙuri'a a waɗannan yankunan za su zaɓi ɗanmajalisa ɗaya ne don wakiltarsu a majalisar wakilai da ake kira House of Commons.

Akasarin 'yanmajalisar kan ci zaɓe a ƙarƙashin jam'iyya ne, amma wasu kan tsaya takara a ƙashin kansu.

Me ya sa Rishi Sunak ya nemi a yi zaɓe da wuri?

Rishi Sunak kenan lokacin da yake sanar da ranar zaɓe a cikin ruwan sama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rishi Sunak kenan lokacin da yake sanar da ranar zaɓe a cikin ruwan sama

Jam'iyyar Conservative ta Mista Sunak na rasa goyon baya a ƙuri'un jin ra'ayin jama'a tun daga 2011.

Wasu 'yan jam'iyyar "kan ji cewa ba lallai wani abu ya sauya ba, sannan idan aka ƙi sauraron koke-koken masu zaɓe a yanzu na neman ƙara musu 'yancin saka baki a harkokin mulki zai iya ta'azzara baƙin jinin jam'iyyar," a cewar editan harkokin siyasa na BBC Chris Mason.

"A wani gefen kuma, akan ce a yi shi yanzu ko kuma abu ya sake lalacewa.

"Shi ma firaministan zai iya nuna wasu abubuwa da zai ce sun cimma, ko kuma suke shirin cimmawa.

"Alƙaluman hauhawar farashi za su iya zama wata nasara. Tabbas ba wai ƙoƙarin gwamnati ne gaba ɗaya ya jawo hakan ba. Amma za a zargi gwamnatin idan lamarin ya fi haka lalacewa, saboda haka babu mamaki idan suka ɗauki alhakin wani ɓangare.

"Sannan akwai yiwuwar lamurra su yi kyau nan gaba a tattalin arzikin."

Wace jam'iyya ce ta fi farin jini?

Ƙuri'un jin ra'ayi na baya-bayan nan sun nuna jam'iyyar Conservative ta su Sunak ba ta fara yaƙin neman zaɓe da wuri ba saɓanin abokiyar hamayyarta, Labour Party.

Tabbas ba lallai ƙuri'ar jin ra'ayi ta zama ma'auni ba, kuma Mista Sunak zai yi fatan raguwar hauhawar farashi zai taimaka wa jam'iyyar Conservative dawo da martabarta.

A yanzu dai Labour ta fara neman yaƙin neman zaɓe a saman Conservative.

Jam'iyyar Reform UK - wata jam'iyya mai tsattsauran ra'ayi kan 'yancirani - tana matsayi na uku amma da wuya ta iya samun wata nasarar cin kujeru.

Jam'iyyar Lberal Democrats - wadda a baya take ta uku a ƙasar - ta ci gaba da samun kashi 10 cikin 100 a ƙuri'ar jin ra'ayi, amma suna fatan dagewa a kan wasu kujeru da suka saka a gaba zai ba su damar cin wasu da yawa a babban zaɓe.

Me zai faru da shirin kai 'yancirani Rwanda da Sunak ke yi?

Sunak ya ci alwashi a baya na fara aika masu neman mafaka zuwa Rwanda kafin babban zaɓen. Ya saka shirin a matsayin babbar manufar gwamnatinsa yana mai cewa hakan zai hana masu shiga ƙasar ta ƙananan jiragen ruwa ta Kogin Ingila.

Amma ganin yadda aka nemi yin zaɓen da wuri, yanzu ya ce za a fara aiwatar da shirin bayan kammala zaɓen.

Labour ta yi alƙawarin yin fatali da tsarin idan ta yi nasara, abin da ya sa aka fara tunanin ma ko za a tura wani.

Tsarin wanda tuni ya laƙume fan miliyan 240, zai zama babban bambanci tsakanin jam'iyyun biyu yayin yaƙin neman zaɓen na mako shida.

Su wane ne manyan 'yan takara?

Yanzu haka dai jam'iyyun Conservative da Labour ne manya kuma su ne ake sa ran za su samu mafi yawan kujeru a zaɓen.

Firaminista Rishi Sunak mai shekara 44, shi ne shugaban Conservative. Shekarunsa 42 lokacin da ya zama firaminista a 2022, inda ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa hawa kujerar. Shi ne kuma ɗan Birtaniya mai jinin Indiyawa na farko da ya zama shugaba.

Sir Keir Starmer ne shugaban Labour mai shekara 61. An zaɓe shi ne bayan saukar Jeremy Coben a 2020. A baya shi ne shugaban hukumar gabatar da ƙara.

Me ke faruwa da majalisa da 'yanmajalisar kafin zaɓe?

british flag and the parliament building

Asalin hoton, Getty Images

Firaministan ya nemi sarki ya "rushe" majalisa - wato salon rufe majalisar a hukumance kafin zaɓe.

Za a yi hakan a ranar Alhamis 30 ga watan Mayu.

'Yanmajalisa za su rasa muƙamansu tare da fara yaƙin neman tazarce idan suna muradi.

Sama da 'yanmajalisa 100 ne suka bayyana cewa ba za su sake yin takara ba a zaɓe mai zuwa.

Ita ma gwamnati kan tsayar da ayyuka yayin yaƙin neman zaɓen.

Me ke faruwa bayan kammala zaɓen?

Bayan gama ƙuri'u, sarki zai nemi shugaban jam'iyyar da ta fi yawan ƙuri'u da ya zama firaminista kuma ya kafa sabuwar gwamnati.

Shugaban jam'iyyar da ta zo ta biyu kuma zai zama jagoran adawa.

Idan babu jam'iyyar da ta samu 'yanmajalisa mafiya rinjaye - ma'ana 'yanmajalisarta su kaɗai ba za su iya amincewa da wani ƙudirin doka ba sai da taimakon wasu - sakamakon ya zama cankacakare kenan.

A irin wannan yanayin, jam'iyya mafi grima za ta iya yanke shawarar kafa gwamnatin haɗin gwiwa da wata jam'iyyar ko kuma ta yi mulki a matsayin maras rinjaye, inda za ta dinga dogara da ƙuri'un wasu jam'iyyun kafin amincewa da wasu dokoki.