‘'Ya’yan yayana suna maƙale ni amma dole na tafi na bar su a Sudan’

Wata ‘yar Burtaniya da ta tsere wa rikicin Sudan ta bayyana yadda aka ɗauke ta daga ƙasar lokacin da take tsakiyar ‘ya’yan yayyenta waɗanda suke kuka, suna rirriƙe ta domin kada ta tafi, ta bar su.

Waafa Salim ta tattauna da BBC a filin jirgin Larnaca da ke Cyprus, inda jiragen Burtaniya ke sauka bayan sun taso daga Sudan gabanin su ƙarasa ƙasarsu.

Ba a amince mata ta tafi da yaran ba saboda dokokin da Burtaniyan ta shimfiɗa na kwaso mutanen.

“Ala dole, na miƙa su ga mahaifinsu. Wani mummunan lokaci ne da ba zan manta da shi ba,” in ji ta.

‘‘Ƙananan yara ne da ba su da kariya, kamata ya yi a ce an bari ni na taho da su cikin jirgi.

‘‘Sun shaida min cewa ba zan iya ɗauko su ba saboda ƙa’idar da aka sanya, sai mai fasfo ɗin Burtaniya ne kawai za a ɗauka.

Na roƙe su na ce 'ya'yana ne, amma suka ce hakan ba zai yiwu ba.”

Fadar mulki ta Downing Street ta zayyana wasu sharuɗɗa waɗanda ta ce ba za a sauya su ba, amma an bai wa jami'an da ke Sudan, wuƙa da nama game da yanke shawara kan abin da suke gani ya fi zama daidai bisa la'akari da abin da ke faruwa zahiri a Sudan.

Ofishin wajen Burtaniya ya ce jirage takwas da suka tashi sun kwaso mutum 897 daga ƙasar wadda ke gabashin Afrika zuwa Cyprus a ranar Alhamis.

Amma duk da haka wannan wani adadi ne da bai taka kara ya karya ba bisa la'akari da yawan ‘yan Burtaniya da ke Sudan.

Waafa Salim wadda ma'aikaciyar tsare-tsare ce a wani ofis a Buckinghamshire, ta je arewacin Sudan ne, inda ta ce mutane na samun tallafi daga Ƙungiyar ba da agajin ta Red Cross.

Ta je Sudan ne da ɗanta Hasan mai shekara 12, wata ziyara da ta kai wa ‘yan uwanta a lokacin sallah ƙarama.

Ya kamata a ce sun koma Burtaniya a makon jiya, amma yaƙin da aka fara ya haifar musu da tsaiko.

‘Abin firgici ne da tashin hankali’

Ta samu damar tsallake shingen duba ababen hawa da yawa da ɗanta ga kuma ɗan'uwanta, tare da 'ya'yansa da ke tsakanin shekara 3 -10.

Sai dai, bayan ta tattauna da jami'an Burtaniya ne sai aka mayar da ɗan'uwanta da 'ya'yan nasa.

“A dokar da suka bayar sun ce ‘ya’yan cikinmu kawai za mu iya fita da su,” in ji ta.

“Waɗannan yaran da ba su san komai ba, ku bar su tare da ni. Shi ɗan'uwana ya zauna, amma suka ƙi.”

Ta ce yanzu ɗan'uwan nata da iyalansa na ƙoƙarin barin Sudan ta kan iyakar Masar, ta ƙara da cewa da babu yara da tafiyar ta fiye masa sauƙi.

A yanzu haka, duk wani mai fasfo ɗin Birtaniya da iyalansa ko kuma mai shaidar zama a ƙasar zai iya samun damar a ɗauke shi.

Da yake magana tun da farko, sakataren wajen Burtaniya James Cleverly ya ce kada a bar duk ɗan Sudan ɗin da ba shi da takardun zama a Burtaniya ya wuce shingen tantance mutane.

“Lokacin da aka samu ɗan Burtaniya na auren ‘yar Sudan kuma suna da ‘ya'ya, sai mu rasa yadda za mu yi,” in ji shi.

“Ya shawarci ‘yan Burtaniya su gaggauta tattara nasu ya nasu su fice daga Sudan domin ba a san me zai faru ba, idan lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta ya ƙare.

Jami’ai a Burtaniya suna ci gaba da tuntuɓar ɓangarorin biyu da ke gaba da juna, a kan su daure su tsawaita wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakaninsu.

Da yake magana a gaban majalisa, sakataren waje na jam'iyyar adawa, David Lammy ya yi kira ga gwamnati ta bari a kwashe ‘yan Sudan masu shaidar zama a Burtaniya.

A tare da Waafa Salim akwai ɗanta mai shekara 12 Hasan, wanda ya riƙa fama da ƙarancin barci a makon jiya saboda tashin bam da ƙarar harbe-harben bindiga.

Ta ce abin takaici ne ka bar 'yan'uwanka, cikin wannan matsala.

An shaida wa BBC cewa sai da aka kai Waafa Salim asibiti saboda rashin lafiya da ya kama ta a cikin jirgin sama.