Manyan hanyoyi biyar da aka fi samun hatsarin mota a Najeriya

    • Marubuci, Ahmad Bawage
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
    • Marubuci, Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 7

Najeriya ƙasa ce mai girman gaske da kuma yawan al'umma, lamarin da ya sanya take buƙatar hanyoyin da za su riƙa sada al'ummunta daga wani ɓangare zuwa wani.

Duk da cewa akwai hanyoyin sufuri da dama, kamar jirgin sama, da jirgin ƙasa da kuma jiragen ruwa, amma yawancin al'umma a Najeriyar sun fi amfani ne da motoci domin zirga-zirga daga wuri zuwa wani.

Sai da tafiya ta mota na da nasa matsalolin a ƙasar, musamman ta ɓangareen ingancin hanyoyi da kuma tsaro.

Hatsarin mota ya zama tamkar ruwan dare a ƙasar, lamarin da ke haifar da asarar rayuwa da dukiya.

Mutane da dama dai na zaton ana samun hatsari ne idan hanya ba ta da kyau, sai dai a Najeriya hanyoyi masu kyau ɗin ma ana yawan samun haɗuran mota a kansu, a cewar shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa, Shehu Mohammed.

Shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa gudu fiye da ƙima shi ne yake kawo kashi 80 cikin 100 na irin haɗuran da ake samu a faɗin Najeriya.

Ga wasu hanyoyi biyar da aka fi samun haɗura a Najeriya, a cewar shugaban hukumar...

Legas zuwa Ibadan

Legas zuwa Ibadan, hanya ce mai tsawon kimanin kilomita 127, wadda ke cikin hanyoyi mafiya zirga-zirgar ababen hawa a Najeriya.

Hanya ce da ta haɗa Legas, babban birnin kasuwanci na Najeriya da Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kuma ita ce hanyar da ta haɗa Legas ɗin da arewacin Najeriya.

Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa ya ce wannan hanya tana a gaba-gaba cikin hanyoyi da ake yawan samun hatsari a Najeriya.

"Hanyar ke da kusan kashi 30 na yawancin haɗurra da ke afkuwa a Najeriya," in ji Shehu.

Ya ce direbobi masu bin hanyar ba su bin dokokin hanya, inda suke tuƙin ganganci, lamarin da kuma da ke haifar da haɗurra bila adadin.

A shekarar 2013, tsohon shugaban ƙasar, Goodluck Jonathan ya bayar da aikin gyaran hanyar.

Abuja zuwa Lokoja

Ɗaya daga cikin hanyoyi masu matuƙar muhimmanci a Najeriya, Abuja zuwa Lokoja ta zama ta biyu a jerin hanyoyin da aka fi samun hadurra a Najeriya, in ji Shehu Mohammed.

Hanyar mai tsawon kimanin kilomita 200 tamkar mashiga ce da ta haɗa ta masu zirga-zirga daga manyan shiyyoyi biyu na ƙasar, wato kudu da arewa.

Mohammed ya ce ana samun haɗura kan hanyar ce sakamakon rashin kyawunta.

Ya ƙara da cewa hanyar tana kuma da dazuka da tsayi abin da yake bai wa direbobi wahala wajen tuki.

Tana daga cikin hanyoyin da suka yi ƙaurin suna wajen fashi da makamai a shekarun da suka gabata.

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ne ya sake bayar da aikin sake gina hanyar a shekarar 2006.

Sai dai kamar da dama daga cikin ayyukan manyan hanyoyin ƙasar, aikin ya ci ta tafiyar hawainiya, lamarin da ya sa hanyar ta zama mai wahalar bi ga masu safara.

Kaduna zuwa Abuja

Abuja zuwa Kaduna hanya ce mai nisanin kimanin kilomita 200.

Hanya ce da ke jan hankulan al'ummar Najeriya kasancewar ita ce ta haɗa babban birnin ƙasar da arewa maso yammacin ƙasar, yanki mafi yawan al'umma a Najeriya.

Hanyar ta yi ƙaurin suna a shekarun baya kan rashin tsaro, sanadiyyar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Kuma duk da haka tana a sahun gaba cikin hanyoyin da aka fi samun haɗurran mota a ƙasar.

Shugaban hukumar kiyaye haɗuran ya ce hanyar Kaduna zuwa Abuja, "tana cikin hanyoyi da ke salwantar da rayukan mutane."

Ya ce abin da ke janyo haɗura shi ne saboda rashin kammala aikin hanyar.

"Ana kan aikin hanyar ba a gama ba. A wasu wurare an haƙa ba a karasa ba, idan mai mota ya taho da daddare bai sani ba zai iya afkawa," in ji Mohammed.

Abuja zuwa Kaduna wani ɓangare ne na aikin gyara da inganta hanyar Abuja zuwa Kano da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari ta amince da bayarwa a watan Disamban 2017.

Kimanin shekara bakwai bayan haka har yanzu an gaza kammala aikin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna.

Wannan ya sanya ɓangarori da dama na hanyar sun yi mummunan lalacewa, manyan ramuka a sassan hanyar sun sanya tafiya a hanyar ya yi wahala, sannan aron hannu ya zama ruwan dare a hanyar.

Lamarin ya haifar da taƙaddama da zazzafar muhawara a tsakanin al'umma, har da majalisar dokokin ƙasar.

Abuja zuwa Keffi

Wannan na daga cikin manyan hanyoyin da suka haɗa Abuja, babban birnin Najeriya da wasu sassan ƙasar.

Mutane da dama waɗanda ke aiki a cikin birnin Abuja na yin asubanci a lokacin zuwa aiki, da kuma yammaci a kanta lokacin komawa gida.

Hanyar ta haɗa Abuja da wasu unguwanni da ke da yawan ma'aikata - kamar Maraba da Nyanya - kafin zarcewa zuwa wasu yankuna na ƙasar.

Corp Marshall Shehu Mohammed ya ce: "Haɗuran na afkuwa kan titin ne saboda yawan cuskoson mutane da ababen hawa".

Ya ce hanyar ce ta dangana zuwa Jos da Makurdi da kuma sauran jihohi da ke arewa maso gabashin Najeiya.

A watan Nuwamban 2018 ne gwamnatin Najeriya ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari suka ƙaddamar da aikin faɗaɗawa da gyara hanyar.

Aikin farko ya ƙunshi faɗaɗa kilomita 5.4 na farko daga Abuja zuwa falle 10, sai kuma sake ginawa da faɗaɗa hanyar wadda ta miƙe zuwa Keffi da Akwanga da Lafiya, har zuwa Makurdi.

Titin zuwa filin jirgin sama na Abuja

Titin Umaru Musa Ƴar'adua Expressway, wadda tun farko ake kira 'Airport road, hanya ce mai falle 10, ta shiga cikin jerin hanyoyin da aka fi yawan samun haɗurra a Najeriya.

Hanyar mai nisan kilomita 37.5 ta haɗa ƙwaryar birnin Abuja da filin jirgin saman birnin (Nnamdi Azikwe International Airport).

Duk da cewa hanyar ta daɗe, amma an sake ginawa da faɗaɗa ta ne domin magance matsalar cunkoson ababen hawa da ake samu a hanyar.

Shehu Mohammed ya ce haɗurra na afkuwa a kan titin ne sanadiyyar gudu fiye da ƙima da direbobi ke yi saboda kyawun hanyar.

"Wani lokaci masu jiran mota ko masu amfani da hanya za su hango mota daga nesa, sai su yi tsammanin za su iya tsallaka titin kafin ta iso, amma kafin su tsallaka mota ta kawo kan su har ta buge su saboda hanyar na shimfiɗe ne samɓal," in ji Shehu.

Baya ga cewa tana kai wa zuwa filin jirgin sama na Abuja, Ƴar'adua expressway ita ce hanyar ficewa daga birnin Abuja zuwa yankunan Najeriya dake kudancin ƙasar.

Haka nan kuma akwai wasu manyan unguwannin da ke ƙunshe da ma'aikata waɗanda ke shige da fice a cikin birnin na Abuja a kowace rana.

Abubuwan da suka fi janyo hatsarin mota a Najeriya

Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya ya ce akwai abubuwa da dama da ke janyo yawan haɗura a Najeriya, waɗanda suka haɗa da...

  • Gudun wuce sa'a ko tukin ganganci
  • Ɗaukar kayan da ya wuce ƙima
  • Rashin mutunta dokokin hanya
  • Tuki cikin maye
  • Barci
  • Rashin lafiyar idanu
  • Rashin bin ƙa'idar fitilar bayar da hannu (danja)
  • Bin ɓarauniyar hanya
  • Amfani da wayar salula lokacin tuki
  • Rashin gogewa wurin tuki

Hanyoyin kauce wa hatsari

Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasan ya ce suna shirin ɓullo da wasu tsare-tsare da nufin magance ko kuma rage yawan haɗura da ake samu a faɗin Najeriya.

Ya ce abubuwan da ya kamata a yi su ne wayar da kan direbobi da fasinjoji.

"Za mu mayar da hankali kan fasinjoji a yanzu saboda su suka fi mutuwa ko jikkata idan aka samu hatsari," in ji Shehu.

Ya ce suna shirin ɓullo da tarukan wayar da kai daga matakin ƙananan hukumomi zuwa jihohi.

Ya ce ya kamata direbobi su kuma daina amfani da wayar salula lokacin tuki domin hakan yana da barazana.

Ya kuma ce sun kaddamar da wata manhaja da mutane za su iya tuntuɓar hukumar.

"Idan fasinja yana da manhajar za ta nuna masa cewa direba na gudu fiye da ƙima don haka sai ya tsawatar masa. Sannan manhajar za ta kuma sanar da mutum idan akwai haɗari a gaban shi," kamar yadda shugaban hukumar kiyaye haɗuran ya faɗa wa BBC.