Argentina ta yi wasa 35 a jere ba a doke ta ba

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

A tsakar daren Juma'a Argentina ta doke Honduras da ci 3-0 a wasan sada zumunta a Amurka, karo na 35 da ta buga wasa a jere ba a doke ta ba.

Minti 16 da fara wasa Argentina ta fara cin kwallo ta hannun Lautaro Martnex, daga baya Lionel Messi ya ci na biyu a bugun fenariti.

Kyaftin din Argentina mai taka leda a Paris St Germain shi ne ya zura na uku a raga, kuma na biyu da ya ci a wasan na sada zumunta don shirin kofin duniya.

Argentina mai rike da kofin babbar gasar tamaula ta duniya biyu za ta fara wasan farko a Qatar ranar 22 ga watan Nuwamba da Saudi Arabia.

Argentina za ta kara buga wani wasan sada zumunta ranar Laraba da Jamaica a Amurka, daga nan sai shirin zuwa Qatar gasar kofin duniya.