Hotunan bikin Kirsimeti a sassan duniya

Al'ummar Kirista a faɗin duniya na ci gaba da shagulgulan bikin Kirsimeti don murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Kiristi.

Kirsimeti ɗaya ne daga cikin lokuta mafi muhimmanci ne ga mabiya addinin na Kirista.

Bikin Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan Kiristoci ne ke shagalin bikin Kirsimeti a wani babban kanti da ke birnin Hong Kong na ƙasar China
Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Al'ummar Kiristoci a yankin Kashmir ma ba a bar su a baya ba, inda nan suka fito domin yin murnar Kirsimeti
Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan ma dai Kiristoci ne ke addu'a lokacin da suke shagalin Kirsimeti a wata majami'a da ke birnin Ramallah a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Neymar Jr

Asalin hoton, Neymar/Instagram

Bayanan hoto, Shahararren ɗan wasan Brazil da Al-Hilal Neymar Jr tare da ƴan uwansa suke murnar bikin Kirsimeti
Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan wasu masu murnar Kirsimeti ne ke wasan ninƙaya a Sifaniya
Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan wasu masu ibada na kunna kyandir a birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya
Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kiristoci sun taru a wani wurin shakatawa don murnar bikin Kirsimeti a Philipphines
Kirsimeti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata masu bauta a ƙasar Pakistan na gudanar da ibada a wata coci
Tudun Biri
Bayanan hoto, Kiristoci da Musulmai a lokacin murnar bikin Kirsimeti a wata majami'a a Tudun Biri a karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna
Kirsimeti a Tudun Biri
Bayanan hoto, Nan mata masu ibada ne a wata majami'a a garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna