'Na ga yadda dakarun RSF ke take mutane da mota' - Labarin wasu da suka tsere wa yaƙin Sudan

Abdulqadir Abdullah Ali ya ce ya ga yadda mayaƙan RSF ke harbin mutanen da ke guduwa daga el-Fasher

Asalin hoton, Ed Habershon / BBC

Bayanan hoto, Abdulqadir Abdullah Ali ya ce ya ga yadda mayaƙan RSF ke harbin mutanen da ke guduwa daga el-Fasher
    • Marubuci, Barbara Plett Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Afirka
    • Aiko rahoto daga, Al-Dabbah, Sudan
  • Lokacin karatu: Minti 5

Abdulqadir Abdullah Ali na fama da mummunan ciwon suga, wanda ya kai ga cutar ta shafi tsoka da jijiyoyinsa tare da riƙe masa afa saboda gaza samun magani.

Dattijon mai shekara 62 a duniya na tafiya ne da ƙyar, amma a lokacin da mayaƙan RSF suka mamaye birnin el-Fasher a yammacin Darfur, ya tsorata, ya ɗimauce ta yadda bai san lokacin da ya riƙa falla gudu ba.

"A safiyar ranar da RSF suka shigo, harsasai kawai ke tashi, sai kuma abubuwa da ke ta fashewa," in ji shi.

"Mutane suka ɗimauce saboda tsoro, kowa ya tarwatse yana ta kansa, ba iyaye ba- ba yara ba."

Ƙwace garin na el-Fasher bayan ƙawanyar wtaa 18 na ɗaya daga cikin lokuta mafiya muni a yaƙin basasar Sudan.

BBC ta kai ziyara wani sansani a arewacin Sudan da aka kafa a yankin da sojojin gwamnati ke iko da shi domin jin ta bakin mutanen da suka samu damar tserewa. Jami'an tsaro sun yi ta saka mana ido a baki ɗayan lokacin da muke tare da mutanen.

RSF na yaƙar dakarun gwamnatin tun daga watan Afrilun 2023 lokacin da kokawar neman iko tsakaninsu ta rikiɗe zuwa yaƙi.

Ƙwace el-Fasher babbar nasara ce ga ƙungiyar, inda suka fatattaki sojojin gwamnati daga garin, wanda shi ne na ƙarshe da ke hannunsu a yankin Darfur.

Mun ga Ali na karakaina a kusa da sansanin da ke cikin hamada mai nisan kilomita 770 daga arewa maso gabashin el-Fasher wanda ke kusa da garin al-Dabbah.

Wani yaro yana barci a kan tabarma bayan sun gudu daga el-Fasher zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira a al-Dabbah ranar 12 ga watan Nuwamban 2025.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansuel-Fasher zuwa al-Dabbah

Yana ƙoƙarin yi wa iyalansa rajista ne domin samun tanti.

"'Yan RSF na harbin mutane - tsofaffi, da fararen hula, da harsasai masu kisa," kamar yadda ya faɗa mana.

"Wasu daga cikin 'yan RSF ɗin sun je da motocinsu. Idan suka ga wani nimfashi sai su take shi da motar."

Mista Ali ya ce ya tsere a lokacin da ya samu dama, yakan yi rarrafe a ƙasa ko kuma ya ɓuya idan ya ji sun matso kusa. Ta haka har ya kai ƙauyen Gurni maras nisa daga el-Fasher.

Gurni ne gari na farko da masu tserewa daga el-Fasher ke yada zango, cikinsu har da Mohammed Abbaker Adam, wani jami'i a sansanin Zamzam na 'yan gudun hijira.

Adam ya gudu zuwa el-Fasher lokacin da RSF ta tarwatsa sansanin Zamzam a watan Afrilu, kuma ya tsere kwana ɗaya kafin su kame garin.

Ya tara farin gemu domin ya ɓatar da kamarsa a matsayin tsoho, abin da yake fatan zai sa ya samu sauƙi ko kuma taimako.

Mohammed Abbaker Adam kenan sanye da rigar T-shirt a hoton hagu, da hoton dama da ke nuna shi da farin gemu

Asalin hoton, Ed Habershon / BBC / Mohammed Abbaker Adam

Mohammed Abbaker Adam ya samu damar tserewa

Asalin hoton, Mohammed Abbaker Adam

Bayanan hoto, Mohammed Abbaker Adam ya samu damar tserewa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Titin zuwa nan cike yake da mace-mace," in ji shi.

"Sun harbe wasu mutane a gabanmu kuma suka je suka zubar da su a wani wuri daban. Mun ga gawawwaki a kan titi, wasu ma sun yi kwana biyu ko uku a wurin."

A cewarsa, "akwai mutane da yawa da suka fantsama gari, ba mu san inda suke ba".

Wasu daga cikinsu da ba su samu damar kaiwa al-Dabbah ba sun kai kansu Tawila mai nisan kilomita 70 daga el-Fasher.

Wasu sun tsallaka cikin Chadi. Amma Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƙasa da rabin mutum 260,000 da aka yi ƙiyasin suna zaune a garin kafin a ƙwace shi ba a san inda suke ba.

Adam ya ce mayaƙan sun kuma yi wa mata fyaɗe.

"Sukan kai mace bayan bishiya, ko su yi nisa da ita daga wajenmu saboda kada mu gani," kamar yadda ya bayyana.

"Amma kana iya jin kukanta tana neman ɗauki. Daga baya idan ta dawo za ta ce 'Sun yi min fyaɗe.'"

Wata mai shekara 19 ta faɗa mana cewa mayaƙan RSF a wani wurin duba ababen hawa sun ɗauki wata yarinya da suke tare, dole haka suka tafi suka bar ta a wajensu.

"Na firgita," a cewarta. "Lokacin da suka fitar da ita daga motar na ji tsoron ni ma za a iya fitar da ni a wani wuri duba abin hawan na gaba."

Tana tafe ne tare da 'yan'uwanta mace da namiji. Mahaifinta wanda soja ne, an kash shi a yaƙin. Mahaifiyarta ba ta el-Fasher lokacin da RSf suka ƙwace shi.

Ita da sauran tsere tare da kakarsu a ƙafa. Amma ta rasu kafin su kai Gurni, abin da ya sa suka ƙarasa su kaɗai.

"Ba mu sha ruwa da yawa ba saboda ba mu san nisan tafiyar ba," kamar yadda matashiyar ta bayar da bayani.

"Mun yi ta tafiya har kakata ta faɗi ta suma. Na yi tunanin ƙarancin ruwa ne ko abinci. Na duba nimfashinta amma ba ta farfaɗo ba. Sai na nemo likita a wani ƙauye da ke kusa. Yana zuwa ya ce ta rasu."

Hankalinsu ya fi tashi game da ɗan'uwansu mai shekara 15 saboda RSF na zargin mazan da ke guduwa sun taya sojoji yaƙi.

"RSF sun yi ta bincikar mu tsawon awanni a cikin rana," kamar yadda ya bayar da labari lokacin da suka tare su a mota suna yi wa duka mazan motar tambayoyi.

"Mayaƙan RSF sun tsaya a kanmu zagaye da mu, suna dukanmu suna yi mana barazana da bindigogi. Na sadaƙar, kawai na ce musu, 'Ku yi min duk abin da za ku yi.'"

Daga baya sun ƙyale shi ya tafi - bayan ƙanwarsa mai shekara 13 ta fada musu cewa mahaifinsu ya mutu kuma shi kaɗai ne ɗan'uwanta. Sun sake haɗuwa da mahaifiyarsu a sansanin al-Dabbah.

Haka suka yi wa Abdullah Adam Mohamed a garin Gurni lokacin da suka fitar da shi daga cikin 'ya'yansa mata uku. Mutumin da ke sayar da turare na ci gaba da kulawa da su tun bayan kashe matarsa yayin wani hari wata huɗu da suka wuce.

'Ya'yan nasa na da shekara biyu, huɗu, da kuma babbar mai shekara shida.

Abdullah Adam Mohamed kenan tare da 'yarsa Sabaa mai shekara huɗu

Asalin hoton, Ed Habershon / BBC

Bayanan hoto, Abdullah Adam Mohamed kenan tare da 'yarsa Sabaa mai shekara huɗu

"Na bayar da 'ya'yan nawa ga sauran matan da muke tafe tare da su," kamar yadda ya shaida wa BBC. "Sai RSF suka kawo wasu manyan motoci. Mu mazan ciki mun yi fargabar za su tilasta mana shiga cikinsu. Sai wasu daga cikinmu suka gudu cikin gari.

"Na yi ta tunanin ta yaya zan sake haɗuwa da 'ya'yana? Na rasa mutane da yawa a baya - na ji tsoron su ma zan rasa su."

Ali ya ce ya hango daga nesa yadda RSF suka buɗe wa mazaje wuta.

"Sun kashe mazajen ban da mata. Mun ga gawawwaki da yawa kafin mu gudu," kamar yadda ya shaida wa BBC.

RSF wadda Mohamed Hamdan Dagalo ke jagoranta, abokiyar hulɗar rundunar sojan Sudan ce kafin alaƙar shugabannin ta lalace

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, RSF wadda Mohamed Hamdan Dagalo ke jagoranta, abokiyar hulɗar rundunar sojan Sudan ce kafin alaƙar shugabannin ta lalace