Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 10 da mata suka fi maza ƙwarewa a kai
- Marubuci, Na Dinah Gahamanyi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili News
- Aiko rahoto daga, Nairobi
- Lokacin karatu: Minti 7
Duk da cewa an daɗe ana kallon mata a matsayin masu rauni idan aka kwatanta su da maza, wasu bincike da aka yi suna nuna akwai abubuwa da matan suka fi maza.
Mata sun fi maza juriya wajen gudanar da aikace-aikace da dama a tare da isar da saƙo sama da maza. Sannan sun fi haƙuri da juriya.
Bayan haka, mata sun fi ƙwarewa wajen tsare-tsare da magance matsaloli da ma kula da na kusa da su.
Wannan ba ya nufin maza ba su da waɗannan siffofin, ko kuma maza ba sa nuna ƙwarewa.
Wannan maƙalar ta yi nazarin wasu abubuwa 10 da mata suka fi maza nuna ƙwarewa:
1. Haɗa ayyuka da dama a lokaci ɗaya
Wannan ba abin mamaki ba ne. Mata suna iya aiwatar da ayyuka da dama a lokaci ɗaya, musamman yadda suke gudanar da aikace-aikacen gida. Misali yadda suke iya haɗa girki a shayar da jariri Da share-share da kula da yara.
Jami'ar Glasgow ta fitar da samakamon wani bincike, wanda ya bayyana cewa mata sun fi maza wannan ƙoƙarin. Sun yi nazarin ne ta hanyar tambayar mutane su nemo wani makulli da ya ɓace a daidai lokacin da suke amsa waya.
Masana sun ce mata a haka tsarin halittarsu take, sannan hakan ya samo asali ne daga asalin halittar ƙwaƙwalwarsu, inda sashen hagu da dama na ƙwaƙwalwar mata suka fi alaƙa da juna. Gefen hagun ne ke da alaƙa da tunani da nazari, sannan na daman ne ke da alaƙa da ƙirƙira da fahimta.
Don haka saboda alaƙar da ke tsakanin gefen biyu ne ya sa mata suke saurin sarrafa bayanai sannan su yi aikace-aikace da dama a tare. Haka kuma ƙwaƙwalwar mata ta fi na maza sauƙin sarrafa bayanai, wanda hakan ya sa suke sauƙin koyo.
Wani bincike da Jami'ar Utah ta fitar, ya nuna cewa mata sun fi maza iya haɗa ayyuka da dama a tare. Sun yi binciken ne ta hanyar buƙatar mutane su gudanar da wasu ayyuka a tare suna yi suna canjawa. Sakamakon binciken sai ya nuna cewa mata sun fi saurin canja tsakanin aikace-aikacen.
Haka kuma akwai wasu binciken da suka nuna irin waɗannan sakamakon.
2: Koyon ilimi
Duk da cewa mata ba za su fi maza kaifin basira ba, bincike ya nuna sun fi mazan saurin koyon sabon abu, kamar yadda binciken Jami'ar Georgia da ta Columbia ya nuna.
Binciken ya nuna mata sun fi maza ƙwarewa wajen mayar da hankali da dagiya da sauƙin shiga sabon yanayin neman ilimi.
Haka kuma bincike ya nuna cewa mata sun fi maza kiyaye abu ya kuma daɗe bayan haɗa ayyuka da dama.
Wannan ya sa suke saurin tuna bayanai da sauran abubuwa su daɗe ba su manta ba. Wannan kuma bai rasa alaƙa da kasancewar mata suna da ɓangaren Gray matter babba sama da na maza, wanda kuma shi ne yake tattara bayanai da ɗaukar mataki. Haka kuma mata sun fi maza yawan estrogen, wanda shi ne yake da alaƙa da ƙarfin hadda.
Haka kuma mata sun fi maza mayar da hankali. Sun fi ƙwarewa wajen mayar da hankali na tsawon lokaci, wanda hakan ya sa suka fi iya kiyaye bayanai cikin sauri.
Idan aka haɗa waɗannan abubuwan ne ya sa mata suka fi maza koyon ilimi.
3: Saurin kammala makaranta
Wannan na yiwuwa ne saboda wasu abubuwa da dama. Mata sun fi iya haɗa ayyuka da dama da isar da saƙo sama da maza, wanda hakan zai taimaka musu wajen samun nasara a makaranta.
Haka kuma mata sun fi haƙuri, wanda shi ma zai taimaka musu wajen juriya da wahalhalun makaranta.
Haka kuma mata sun fi maza yawan sinadarin estrogen, wanda yana ƙara ƙarfin ƙwaƙalwa. Dukkan waɗannan abubuwan suna taimakawa wajen samun nasara a makaranta.
Duk da cewa akwai alfanu da dama ga mata a makarantu, haka kuma suna fama da wasu ƙalubale. Daga cikin akwai wariya a wurin aiki, wanda hakan ya sa suke sha wahalar samun aiki bayan kammala makaranta. Haka albashin mata ya fi na maza ƙaranci.
Wannan ya sa suke fuskantar ƙalubale wajen biyan bashin karatu da ƙara karatun ma. Amma duk da waɗannan matsalolin, mata sun fi maza yiwuwar saurin kammala makaranta.
4: Juriya
Akwai wasu dalilai. Misali, gajiya na cikin rayukan yau da kullum ga mata. Sun saba gudanar da aikace-aikace da dama a tare, wanda hakan suke iya jure wahala da kyau.
Na biyu kuma mata sun fi maza kula sosai, wanda hakan ya sa suke gano matsala cikin sauri tare da shirya magance ta.
Bincike ya nuna cewa ƙwaƙwalwar mata sun sha bamban da ta maza wajen juriya, wanda hakan ya sa matan suka fi juriya.
Lallai mata sun fi maza juriya, domin sun saba, amma hakan ba y nufin ba za su yi rashin lafiya ba.
5: Garkuwar jiki
Har yanzu ba a tantance dalilin da ya sa mata suka fi maza garkuwar jiki ba, amma akwai wasu bayanan da suke ɗan bayyana wau dalilan.
Ɗaya daga ciki shi ne mata sun jinin al'ada da haihuwa, wanda hakan ya sa jikinsu yake sabawa da baƙi. Haka kuma sinadarin estrogen na ƙara ƙarfin garkuwar jiki, shi kuma testosterone na maza yana rage shi.
Mata sun fi maza sinadaran kariya, kuma su ne suke taimakawa wajen yaƙi da cututtuka.
Sannan jikin mata ya fi na maza samar da sinadaran da suke ba jiki kariya.
Wannan ba zai rasa nasaba da kasancewar mata suna da sinadaran ƙwayar halitt ta XX ba, maza kuma suna da XY. Akwai yiwuwar X guda na taimakawa wajen ƙara wa mara garkuwar jiki.
6: Kwarewa wajen isar da saƙo
A taƙaice, mata su fi maza ƙwarewa wajen isar da saƙo. Wannan ba ya nufin maza ba su iya isar da saƙo da kyau ba, amma mata sun fi ƙwarewa. Wataƙila hakan na sa nasaba ne da kasancewar mata sun fi maza fahimtar halin da mutane suke ciki, wanda hakan zai iya taimakawa wajen kula da yanayin da suke ciki.
Mata sun fi maza iya isar da saƙo ta hanyar magana, da ma wajen nune.
Don haka idan kana neman ƙwarewa wajen isar da saƙo, mata sun fi nuna bajinta.
7: Tsawon rayuwa
Mata sun fi maza tsawon rai da aƙalla shekara biyar. Wannan na da alaƙa ne da yanayin hlitta kamar ƙwayoyin halitta da wasu sinadarai, amma kuma yanayin tsarin gudanar da rayuwa ma na taka rawa.
Mata sun fi maza zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu sama da maza. Haka kuma sun fi maza kula da cimakanu sama da maza da ma atisaye. Dukkan waɗannan abubuwan suna taimakawa wajen ƙara wa matan tsawon rai.
Don haka idan kana so rayuwarka ta yi tsawo, ka fara sauya yadda kake gudanar da rayuwa. Ka ci abinci mai kyau, ka riƙa atisaye sannan ka riƙa zuwa ganin likita ana duba lafiyarka.
"A dukkan matakan rayuwa, mata sun fi maza rayuwa mai kyau," kamar yadda Steven Austad, masanin tsufa a Jami'ar Alabama.
Sanan kuma bayan tsawon rai, mata sun fi maza lafiya.
Wani binciken ya nuna mata sun fi maza ƙarfin hali, kamar yadda wani bincike da aka yi a Birtaniya ya nuna, cewa a lokacin fari da cututtuka da annoba da zamanin bauta, mata sun yi maza daɗewa da juriya.
Matan Ingila sun rayuwa a tsakankanin shekata 83.1, maza kuma 79.5. A Scotland kuma mata 82, maza kuma 77.1.
8: Sauraron bayani
Mata sun fi maza iya sauraron bayanai, saboda sun fi haƙuri da juriya sauraron, kuma ba sa katse mutum idan yana magana kamar yadda maza suke yi. Waɗannan abubuwan suna taimaka musu wajen sauraron dukkan abin da ake faɗa, tare da fahimtar saƙon sama da maza.
Wannan na da matuƙar muhimmanci a rayuwa da ma a wajen aiki. Wani bincike da ka yi a Jami'ar Maryland ya nuna mata sun fi maza sauraron bayanai.
Binciken wanda aka wallafa mujallar PLOS ONE, ya nuna cewa mata sun fi tuna abubuwan da suka wakana a tattaunawa. Masu binciken sun ce hakan bai rasa nasaba da yadda mata da mazan suke taskance bayanai.
Mata suna amfanin da gefen dama da na hagu na ƙwaƙwalwarsu, maza kuma suna amfani da gefen hagu ne kawai.
9: Magance matsala
Bincike ya nuna cewa mata sun fi maza ƙwarewa wajen magance matsaloli sama da maza.
Haka kuma mata sun fi tunani da kyau domin fuskantar matsala, su kuma maza sun fi yin tunani da zafi-zafi.
Wani bincike da Jami'ar Michigan ya gano cewa mata sun fi mazan wajen magance matsaloli a wani gwaji da aka yi.
A wajen aiki, wannan na nufin mata sun fi maza ƙwarewa wajen ɗaukar matakai da za su amfani kamfanin. Za su iya sadaukarwa domin samar da hanyoyin da za a magance matsalolin da wajen aiki ke nufi.
10: Jagoranci
A wuraren aiki, mata suna kamanceceniya da maza a ɓangarori da dama. Mata da dama sun fi maza tausayi, wanda hakan ya sa suka ƙwarewa wajen magance matsaloli mau ɗaure kai.
Mata sun fi maza sauƙin kai, wanda yake da matuƙar muhimmanci shugabanci. Sannan kuma sun fi iya isar da saƙo, wanda shi me yake taimakawa wajen bayar da umarni.
Haka kuma kasancewar mata sun yi ƙwarewa wajen magance matsaloli, akwai yiwuwar za su fi iya ɗaukar matakai masu kyau da za su shafi ma'aikatansu.
Waɗannan abubuwan ne suka sa mata suka ƙware wajen shugabanci mai kyau. Wannan ne ya sa kamfanoni da dama yanzu suka fara ba mata manyan muƙamai.
Tacewa: Ambia Hirsi