Abubuwan da Trump zai iya yi a ranarsa ta farko a White House

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
- Marubuci, Laura Blasey & Jessica Murphy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
- Lokacin karatu: Minti 9
Donald Trump da Jam'iyyarsa ta Republican suna da manufa mai cike da buri kuma suna da kusan cikakken rinjaye a majalisar dokokin Amurka.
Trump ya ce zai 'bayar da mamaki' yayin da zai fara aiki cikin gaggawa bayan rantsar da shi a ranar 20 ga Janairu.
Tawagar sa ta ce a tsammaci kudurrori da dama da kuma umarni masu yawa - daga Ofishin shugaban Amurka - a cikin makon farko.
Masana siyasa da lauyoyi sun riga sun tsara waɗannan umarni a matsayin wani ɓangare na sauyin gwamnati.
Har yanzu,ƙungiyoyin fafutuka da gwamnonin jihohin da ke ƙarƙashin mulkin jam'iyyar Democrat sun sha alwashin ƙalubalantar aƙalla wasu daga cikin waɗannan tsare-tsaren.
Ga abin da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce game da abubuwan da ya sa a gaba a wa'adi na biyu.
Shige da fice da kuma tsaron Iyaka
Sakatariyar yaɗa labaran Trump Karoline Leavitt ta shaida wa Fox News a ranar Lahadin da ta gabata cewa "mun san ya yi alƙawarin sanya hannu kan dokar kan dokar da za ta tabbatar da tsaro a iyakar kudancin ƙasar".
"Mun san cewa a ranarsa ta farko zai ƙaddamar da korar baƙin haure mafi girma a tarihin Amurka," in ji ta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin mako guda da sake zabensa, Trump ya ba da fifiko wajen cike mukaman shugabancin ɓangarorin da zai sanya ido kan shige da fice, yana mai nuni da cewa yana shirin tunkarar shirinsa na manufofin kan iyaka cikin gaggawa.
Ya naɗa tsohon jami'in shige da fice Tom Homan a matsayin mai kula da harkokin kan iyaka; ya kuma zaɓi gwamnar Jihar South Dakota Kristi Noem don kula da tsaron cikin gida; sannan ya naɗa Steven Miller a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar White House kan manufofi. Mista Miller ya shahara da tsara wasu shirye-shiryen Trump game da shige da fice ba bisa ka'ida ba a wa'adinsa na farko.
Duk wani shirin korar jama'a na iya fuskantar matsaloli a ɓangaren gudanarwa da kuma ɗimbin ƙalubalen shari'a daga masu ruwa da tsaki a harkar shige da fice da kuma masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam.
Trump na iya sake aiwatar da manufarsa ta "Remain in Mexico" wadda ta buƙaci masu neman mafaka su jira a Mexico yayin da ake aiwatar da ake sauraron buƙatunsu.
Shugaba Joe Biden ya kira shirin "rashin mutunci" kuma yayi ƙoƙarin kawo ƙarshensa a ranar farko da ya hau kan karagar mulki, amma ya fuskanci ƙalubalen shari'a. A 2022, Kotun ƙoli ta ba shi damar ci gaba.
A lokacin gwamnatin Trump, kimanin masu neman mafaka 70,000 ne aka mayar da su Mexico domin jiran sauraron buƙatun da suka miƙa.
Wani alƙawarin ranar farko da ya yi shi ne kawo ƙarshen zama ɗan kasa ta nayar haihuwa - dokar da ta shafe shekaru 150 da ta ce duk wanda aka haifa a ƙasar Amurka ɗan Amurka ne.
Ba a dai tabbatar da yadda Trump ke shirin cimma wannan manufa ba. Ya yi alƙawarin ba da umarnin amma kundin tsarin mulkin Amurka ya fayyace duk wasu shika-shikan zama ɗan ƙasa na
Zai buƙaci jihohi su amince da babban taron ƙasa ko kuma kashi biyu bisa uku na kuri'ar amincewa a majalisar dokoki don ba da shawarar kawo sauyi, sannan kuma a sami kashi uku bisa huɗu na majalisun dokokin jihohi - wanda ƴan Republican ke da rinjaye a fiye da rabinsu.
6 ga watan Junairu
Trump bai ambaci afuwa ba a jawabinsa na nasara, amma ya daɗe yana iƙirarin yin afuwa ga waɗanda aka samu da laifin kutsawa fadar majalisar dokokin ƙasar a shekarar 2021.
"Oh, tabbas, zan yi. Idan ba su da laifi, zan yafe musu," in ji Trump yayin wani taron ƙungiyar ƴan jarida baƙaƙen fata ta ƙasa.
Shugabannin Amurka suna da iko mai yawa na gafarta wa mutanen da aka samu da saɓawa dokokin tarayya ko kuma kawo ƙarshen hukuncin ɗaurin da su ke fuskanta a kurkuku. Masu gabatar da ƙara na iya kuma yanke shawarar yin watsi da ƙararrakin da ake gudanarwa amma hakan ya dangata ne kan wanda Trump zai iya zaɓar ya yafewa.
Abin da ba a tabbatar ba shi ne wanda zai iya samun afuwa.
A wani ɓangare kuma, Trump ya shaida wa CNN cewa: "Na yi sha'awar yafewa da yawa daga cikinsu. Ba zan iya magana kan ɗaiɗaikunsu ba, saboda wasu daga cikinsu, watakila sun ɗan wuce gona da iri."
Ms Leavitt ta fada wa jaridar Washington Post cewa zai yanke hukunci "bisa ga shari'a idan ya dawo fadar White House".
Fiye da mutane 1,500 aka kama dangane da tarzomar ta majalisar dokoki. Kamar yadda alƙaluman gwamnatin tarayya suka nuna, an yankewa sama da 750 daga cikinsu hukuncin ɗaurin kan laifukan da suka jiɓanci yin kutse a gini ba tare da izini ba da cin zarafin jami’an ƴansanda da kuma haɗa baki domin aikata laifi.
Jack Smith
Shi ma Trump ya fuskanci na shi ƙalubalen shari'ar kan abubuwan da ya gudanar bayan zaɓen 2020 da kuma wani shari'ar wasu bayanan sirri.
Lauyan na musamman Jack Smith, wani gogaggen mai shigar da ƙara da aka naɗa don sa ido kan binciken da ma'aikatar shari'ar Amurka ke yi kan Trump, ya shigar da ƙara a gaban kotu, wanda zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya musanta aikata ba daidai ba.
Trump ya ce korar Jack Smith zai kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da zai sa a gaba.
"Zan kore shi a cikin daƙiƙa biyu. Zai kasance ɗaya daga cikin abubuwan da za a fara fuskanta," in ji shi a wata hira a watan Oktoba.
Al'amarin ya riga ya fara fuskantar makoma mara tabbas. Kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci a watan Yuli cewa shugabannin ƙasar na da kariya a wani ɓangare daga gurfanar da su a gaban kuliya saboda yadda suke gudanar da ayyukansu yayin da suke kan karagar mulki, lamarin da ya janyo koma baya ga shari’ar Mista Smith.
Nasarar zaɓen da Trump ya samu ya kuma ba shi ikon yafewa kansa duk wani laifi da ake iƙirarin cewa ya aikata, duk da cewa babu shugaban da ya taɓa yin hakan a baya.
An ba da rahoton cewa ma'aikatar shari'a tana tattaunawa da Mista Smith kan janye ƙararrakin. Babu tabbas ko Trump zai ɗauki wasu matakan hukunta Mista Smith.
Trump dai ya sha caccakar lauyan na musamman a cikin hirarraki da kuma shafukan Intanet, inda ya ayyana shi a matsayin mutum "mara mutunci".
Yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris
A yaƙin neman zaɓensa na 2016, Trump ya sanya fifiko kan ficewa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. A cikin watanni shida da hawansa mulki, Amurka ta fara ficewa daga yarjejeniyar da aka cimma.
Shugaba Joe Biden ya sanya an sake shiga yarjejeniyar daya daga cikin manyan abubuwan da ya sa a gaba lokacin da ya yi takara da Trump a shekarar 2020. Biden ya sanya hannu kan wata wasiƙa da ke neman Amurka ta sake komawa cikin yarjejeniyar a ranar farko da ya hau kan karagar mulki.
Yaya Trump zai mayar da martani a wa'adinsa na biyu? Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na nuni da cewa tawagarsa na shirya umarnin sake janyewa idan ya hau karagar mulki a watan Janairu.
Ficewa daga yarjejeniyar na nufin cewa Amurka ba ta da alhakin bayar da na ta gudumawa wurin cimma burion da aka sanya gaba na rage yawar iskar Carbon da ake fitarwa a duniya.
Daga cikin abubuwan da suka sa a gaba wanda suka yi hannun riga da ka'idojin Paris, Trump ya ce yana son ba da fifiko wurin samar da mai da iskar gas. Ya yi alƙawarin hanzarta ba da izinin ƙara ƙaimi wurin haƙar mai - "Za mu ci gaba da hakowa, hakowa, hakowa," in ji shi a wani shiri na Fox Newa a bara.
Trump ya kuma soki shirin gwamnatin Biden na faɗaɗa samar da makamashi ta hanyar iska da kuma ƙara samar da motoci masu amfani da wutar lantarki, wanda hakan na iya zuwa a farkon gwamnatinsa.
Rasha da Ukraine
A lokacin yaƙin neman zaɓensa, trump ya ce zai iya kapwo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine 'cikin kwana guda'. Ya kuma ci gaba nanata sukar da ya ke yi wa gwamnatin ka tallafin da ta ke bai wa Ukraine, inda ya ke cewa yakin na zuƙe kuɗaden Amurka.
Bai bayar da wani bayani kan yadda zai cimma wannan burin kawo ƙarshen yaƙin ba, ya dai ce za samar tabbatar da cewa ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya.
Tun bayan sake zabensa, Trump ya yi magana da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky a wata hira ta wayar tarho da ta ɗauki tsawon "kimanin rabin sa'a", tare da hamshakin attajirin nan Elon Musk. Wata majiya ta shaida wa BBC cewa "da gaske ba hirar tattauna wasu abubuwa masu ma'ana ba ne."
Fadar Kremlin ta musanta cewa Trump ya yi wata tattaunawa da Vladimir Putin, ko da yake rahotannin kafafen yaɗa labarai sun ce Trump ya gargaɗi shugaban na Rasha game da ruruta wutar yaƙin Ukraine.
Cinikayya da tattalin arziki
Tattalin arziki batu ne da Trump ya yi yaƙin neman a kai, inda ya sha alwashin kawo ƙarshen hauhawar farashin kayayyaki da zarar ya hau mulki.
Trump ya ce "Za mu yi mai da hankali kan abubuwan da suka shafi samun kuɗin motocin hawa zuwa samar da muhalli zuwa farashin inshora."
"Zan sanar da majalisar ministocina cewa ina tsammanin sakamako a cikin kwanaki 100 na farko, ko kuma kafin ma a kai ga hakan."
Ya ce zai rattaba hannu kan wani kudurin da zai umurci kowane sakatare na majalisar ministoci da shugabannin hukuma da su yi "amfani da kowane kayan aiki da ikon da suke da shi" don magance hauhawar farashin kayayyaki da kuma rage farashin kayan masarufi.
Shirin na Trump ya haɗa da sanya haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su ƙasar, musamman waɗanda ke shigowa daga China, yana mai cewa waɗannan harajin za su ci gaba da samar da ayyukan yi ga Amurkawa.
Har yanzu dai babu tabbas kan yadda waɗannan kuɗaɗen harajin za su kasance, amma Trump ya yi hasashen akalla kashi 10% na haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, za a kuma ɗaga harajin shigo da kayayyaki daga China kashi zuwa 60 cikin 100.
Ya kuma lashi takobin karkata akalar harajin zuwa kan Mexico.
"Zan sanar da (Shugaban Mexico) a rana ta farko ko ba da jimawa ba cewa idan ba su dakatar da kwararowar masu laifi da kwayoyi da ke shigowa cikin kasarmu ba, nan da nan zan sanya harajin kashi 25% kan duk wani abin da suke shigowa da su Amurka.
Wataƙila waɗannan shirye-shiryen ƙarin harajin ba za su buƙaci amincewar majalisa ba.
Trump ya riga ya ƙara haraji a wa'adinsa na farko, yana mai yin misali da sashe na 232 na dokar faɗada kasuwanci ta 1962, wanda ke bai wa shugaban ƙasa damar ɗora haraji kan kayayyakin da ka iya shafar tsaron ƙasar Amurka.
Wani alƙawarin kuma shi ne "ƙarshen yaƙin Biden da Harris akan makamashin Amurka", in ji Trump, yana mai shan alwashin haɓaka haƙar mai a matsayin wata hanya ta rage farashin kuɗin makamashi kan Amurkawa.
Trump na iya yin hakan ta hanyar zartar da ƙudurin da zai warware wasu kariyar da ake bai wa muhalli, wanda zai ba shi damar dakatar da ayyukan samar da makamashi mai tsafta da kuma kawar da manufofin yanayi da gwamnatin Biden ta tsara.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya kuma sha alwashin korar Gary Gensler, shugaban hukumar hada-hadar hannayen jari a rana ta farko. Gensler, wanda Biden ya naɗa, ya duƙufa wurin tabbatar da samar da bayanan da suka shafi yanayi da kuma tilasta sanya ido kan kasuwar kuɗn kirifto.
Trump ya kasance mai matuƙar goyon bayan kuɗin kirifto, kuma bayan zaɓensa darajar Bitcoin ya hau da 30% a cikin makon da ya gabata saboda tsammanin cewa gwamnatinsa za ta kasance mafi aminci ga masu harkar kuɗin kirifto.
Title X
Donald Trump ya sha alwashin soke sauye-sauyen da Shugaba Biden ya yi a kan Title X, wanda shi ne shirin ƙasa ɗaya tilo da gwamnatin tarayya ke ba da tallafin kuɗi.
A cikin 2019, a lokacin wa'adinsa na farko, gwamnatin Trump ta aiwatar da wata sabuwar doka da ta hana duk wasu masu ruwa da tsaki a ɓangaren kiwon lafiya da ke ƙarƙashin shirin Title X daga ambaton batun zubar da ciki ga marasa lafiya, koda kuwa majiyyaci ya yi tambayoyi game da shi da kansa.
Wannan sauyin ya hana ƙungiyoyi irin su Planned Parenthood wadanda ke bayarwa ko tura marasa lafiya don zubar da ciki samun miliyoyin daloli.
Amma bayan ƴan watanni, lokacin da Biden ya hau kan karagar mulki, ya sauya wannan manufar.
Yanzu, ana tsammanin Trump zai sake mai do da waɗannan dokokin.











