Ribar da Musk zai iya samu da shugabancin Trump

Elon Musk a yakin neman zaɓen Trump

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Lily Jamali
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, San Francisco Correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 2

Komawar Donald Trump fadar White House na iya zama nasara ga ɗaya daga cikin manyan magoya bayansa: Elon Musk.

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya ya shafe daren zaɓe a Florida tare da Trump a wurin shakatawar sa na Mar-a-Lago yayin da ake samun labarin sakamkon zaɓe.

"Mutanen Amurka sun ba @realDonaldTrump cikakkiyar wa'adin aiwatar canji a daren yau," Mista Musk ya rubuta a dandalin sada zumunta na X yayin da nasarar Trump ta fara bayyana.

Kuma a jawabinsa na nasara a zauren Taro ta Palm Beach, Trump ya kwashe mintuna da dama yana yabon Mista Musk tare da ba da labarin yadda aka yi nasarar saukar wani kumbo da ɗaya daga cikin kamfanonin Mista Musk SpaceX ya ƙera.

Mista Musk y afara marawa ɗan takaran na ajm’iyyar republican ɗin baya ne jim kaɗan bayan yunƙurin kashe Trump da aka yi a garin Butler da ke jihar Pennsylvania a watan Yuli.

A matsayinsa na ɗaya daga cikin masu goyon bayan zaɓaɓɓen shugaban, hamshakin attajirin ya ba da gudummawar sama da dala miliyan 119 (£92m) don tallafawa ofishin yaƙin neman zaɓe da nufin sake zaɓen Trump a matsayin oshigaban ƙasa.

Ya kuma shafe makonnin da suka gabata gabanin ranar zaɓe yana gudanar da yakin neman zabe a jihohin da bas u da tabbas, inda ya ƙaddamar da wani shiri na bayar da kyautar $1m ga masu kaɗa ƙuri’a a jihohin.Wannan Shirin na shi ya janyo matuƙar cece ku ce a fagen siyasa amma daga baya dai wani alkali ya yanke hukuncin cewa za su iya ci gaba da shrin.

Bayan amfani da sunansa da kudinsa wurin goyon bayan Trump, Mista Musk yana da wadatar riba da zai samu daga sake zaɓen Trump.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zababben shugaban kasar ya ce a wa'adinsa na biyu, zai gayyaci Mista Musk a ya shigo cikin gwamnatinsa domin magance barnar da ake yi a gwamnati.

Mista Musk ya yi magana game da yiwuwar kafa sabuwar ma’aikatar gwamnati da za a kira "Sashen Ingantaccen Gwamnati," ko DOGE.

Haka kuma ɗan kasuwan zai iya cin gajiyar shugabancin Trump sakamakon mallakar da ya yi kamfanin SpaceX, wanda tuni ya mamaye harkokin aikawa da taurarin ɗan adam na gwamnati zuwa sararin samaniya.

Misata Musk zai nemi ya yi amafani da kusancinsa da fadar White House wurin ci gaba da cin gajiyar wannan alaƙar da yak e da ita da gwamnati.

Mista Musk ya soki abokan hamayyar su ciki har da Boeing kan tsarin kwangilolin gwamnatinsu, wanda ya ce yana kawo cikas ga kammala ayyukan kan kasafin kudin da aka zayyana, kuma a kan lokaci.

Kamfani SpaceX ya kuma shiga cikin gina tauraron ɗan adam na leken asiri a daidai lokacin da maaikatar tsaron Maurka da sauran hukumomin leken asirin ƙasar ke shirin saka biliyoyin daloli a cikin wannan harkar.

Kamfanin ƙera motocin Mista Musk Tesla na iya samun riba daga gwamnatin da Trump ya ce za ta kasance mai "mafi karancin matsatsi" a harkar kasuwanci.

A watan da ya gabata, hukumar Amurka da ke kula da sufurin mota ta bayyana cewa tana bincike na'urorin da ke tafiyar da motocin Tesla masu tuƙa kansu.

Mista Musk ya kuma sha suka kan zargin neman hana ma'aikatan Tesla haɗan kungiyar ƙwadago. Ƙungiyar ma'aikata a fannin motoci sun shigar da tuhumar rashin yi wa ma’aikata adalci a kan Trump da Musk bayan da mutanen biyu suka yi magana game da cewa Musk ya kori ma'aikatan da ke yajin aiki yayin wata tattaunawa da suka yi a shafin X.

Trump ya kuma yi alƙawarin rage haraji kan kamfanoni da masu hannu da shuni.

Wannan wani alƙawari ne da ake tunanin Mista Musk yake fatan zai cika.